Zabukan kananan hukumomin jihar Kaduna ya bar baya da kura

PDP na zargin gwamnatin APC da kokarin murde sakamakon zaben.
Bayanan hoto,

Malam Nasir el-Rufa'i

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, har yanzu ana ci gaba da ta da jijiyoyin wuya kan zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a farkon watan Satumban 2021.

Lamarin na faruwa ne bayan matakin da hukumar zaɓen jihar ta ɗauka na ayyana cewa zaɓen ƙananan hukumomi guda huɗu a cikin 19 bai kammala ba.

A bangare guda kuma, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke iƙirarin cewa ita ce ta lashe akasarin kujerun ƙananan hukumomin da ta ce ana ƙoƙarin hana ta, jam'iyyar APC mai mulki a nata ɓangare na cewa lamarin ba haka ba ne.

Jam'iyyar PDP ta zargi hukumar zabe da zama 'yar amshin shatar bangaren gwamnati, na yanke shawarar jingine zaben kananan hukumomi biyu da suka hada da Jama'a, da Kaciya, da Jaba da kuma karamar hukumar Siba, saboda rashin kammaluwar zaben da ta ce kotu ce kadai za ta yanke hukunci.

Sakataren jam'iyyar PDP a jihar Kaduna Honarabul Aliyu Solo, ya ce hukumar zabe ta koma bangaren gwamnati.

"Abin da aka yi a karamar hukumar Giwa da Igabi da Zaria shi ne duk inda aka san PDP za ta yi nasara ba a kai akwatin zabe ba, don haka za mu kai kara gaban kotu domin a dawo a sake yin zaben a wadannan kananan hukumomi."

To sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta bakin Muhammad Lawal Shehu Molash, mataimaki na musamman kan harkokin siyasa ga gwamnan jihar Kaduna, ya yi watsi da zargin inda ya ce rashin kunya ce ta sanya PDP ke wannan magana.

"A adalci irin na gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa'i, har sun samu sun ci kujerun ciyamomi, wanda idan a lokacinsu ne ba za a taba samun hakan ba, sun ce za su je kotu mu na jira mu ma sai mu je kotun."

BBC ta yi kokarin jin ta bakin hukumar zaben jihar Kaduna sai dai hakar ba ta cimma ruwa ba.