Illar sakin fursunoni daga gidajen yari kan tsaro a Najeriya

Ko a watan Oktoban 2019 an kai hari gidan yarin Koton-Karfe da ke jihar Kogin, inda fursunoni 153 suka gudu
Bayanan hoto,

Ko a watan Oktoban 2019 an kai hari gidan yarin Koton-Karfe da ke jihar Kogin, inda fursunoni 153 suka gudu

An kama fursunoni 111 da suka tsere daga gidan rin Kabba a jihar Kogi da ke yankin arewa ta tsakiya, nbayan hari da wasu 'yan bindiga suka kai tare da sakon 240 daga cikinsu a ranar Lahadi.

Mai magana da yawun hukumar gidan yarin Francis Enobore ya shaida wa BBC cewa an kama wadanda suka tsere din ne a ranar Talata, bayan akddamar da binciken neman su, yayin da wasu kuma suka koma a karan-kansu.

Kamar yadda rahotanni suka nuna maharan sun isa gidan yarin da misalin karfe 11:45 na daren Lahadi dauke da muggan makamai, kuma ba tare da bata lokaci ba suka fara musayar wuta da jami'an tsaro.

Rahotanni sun tabbatar da kashe jami'an tsaro biyu, inda kuma ake kan neman wasu biyu a halin da ake ciki.

Sai dai gwamnan jihar ta Kogi Yahaya Bello ya ce da dama daga cikin fursunonin da suka gudu daga gidan yarin na Kabba an kama su, yayin da wasu suka dawo da kansu.

Rahotanni sun ce mafi yawan fursunonin gidan yarin Kabba din ana zargin mayakan Boko Haram be, amma hukumomi sun ce har yanzu ba su san wanda ya kai harin na ranar Lahadi ba.

Mene ne hadarin balle gidajen yari a halin da Najeriya ke ciki?

Masu sharhi kan lamarin tsaro a Najeriya sun sha bayyana irin hadarin da ke tattare da yi wa dabi'ar fasa gidajen yari rikon sakainar kashi, musamman a halin rashin tsaro da kasar ke ciki.

Lura da cewa Najeriya na cikin halin rashin tsaro a kusan duka yankunan kasar, masana na ganin idan aka yi sake, balle gidajen yari zai iya samar da karuwar 'yan ta'adda a kasar.

A cewar Abdullahi Yelwa, malami a sashen nazarin muggan dabi'u da dakile yaduwarsu na Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere da ke Tatari-Ali da ke Bauchi, ya zama dole a dauki matakan gaggawa kafin lamarin ya fi karfin hukumomi.

Asalin hoton, BBC Pidgin

Bayanan hoto,

A watan Oktoban 2020 ma bata gari sun kai hari gidan yarin Warri suka sa masa wuta

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A ta bakin masanin ''karancin jami'an tsaro da kuma jinkirin yankewa tare da zartar da hukunci na daga cikin manyan abubuwan da ke rura wutar kai hare-hare a gidajen yari''.

''Abin takaici shi ne sai ka ga akwai wadanda an dade da yanke musu hukuncin kisa amma ba za a aiwatar ba sai a ajiye su a gidajen yari''.

''Kuma kasancewar su mutane masu hadari a cikin al'umma, ba abin mamaki ba ne su hada kai da yan uwansu a waje su balla gidajen yarin don fito da su''.

''Akwai kuma rashin kyakkyawan tsaro, wanda yana faruwa ne saboda karancin jami'an tsaro a gidajen yarin Najeriya,'' in ji Abdullahi Yelwa.

Haka ma masanin ya ce jami'an tsaron ba su da horon da ya dace, ga kuma karancin makamai na zamani da za su iya amfani da su wurin dakile faruwar irin wadannan hare-hare.

A kan haka ya bukaci hukumomi a Najeriya da su dauki matakan zartar da hukunci ba tare da bata lokaci ba, da kuma samar da isassun jami'an tsaro tare da ba su horon da ya dace.

Wasu masu sharhin sun hankaltar da hukumomin Najeriya cewa lura da kusancin jihar Kogin da babban birnin kasar wato Abuja, akwai fargabar wasu daga fursunonin su tsallako birnin cikin sauki.

Balle gidajen yari

A shekarun baya-bayan nan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare gidajen yari a garurwuwa daban-daban inda suka saki fursunoni.

A watan Afrilin 2021 ma fiye da fursunoni 1,800 'yan bindiga suka sake bayan wani kwanton bauna da suka kai hedikwatar 'yan sanda a kudu maso gabashin Najeriya.

Ko a watan Oktoban 2019 an kai hari gidan yarin Koton-Karfe da ke jihar Kogin, inda fursunoni 153 suka gudu.

'Yan sanda sun dora alhakin hakan kan kungiyar Ipob da ke fafutukar ballewa daga kasar.