Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Rudiger da Casemiro da Hazard da Dybala da Adeyemi da Vinicius Junior da Philippe Coutinho

junior

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid na da kwarin gwuiwar cewa mai tsaron bayan Chelsea da Jamus Antonio Rudiger zai koma kungiyar a karshen kaka. (The Athletic - subscription required)

Ita kuwa Chelsea tana son ta kawo dan wasan tsakiyar Real Madrid din wato Casemiro. (El Nacional - in Catalan)

Manchester City ta saka wa dan wasan tsakiyarta Phil Foden farashin fam miliyan 128, wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin yan wasa mafiya tsada a duniya. (Mail)

Haka kuma City na shirin bai wa mai tsaron bayanta Joao Cancelo sabon kwantiragi a farko watan Janairun 2022. (Fabrizio Romano)

Real Madrid ta yi watsi da tayin fam miliyan 21 da West Ham ta yi kan Eden Hazard. (El Nacional - in Catalan)

Ita kuwa Liverpool ta fara sa'ido kan Raphinha na Leeds United da kuma dan wasan gaban West Ham Jarrod Bowen tun kafin watan Janairu ya kama. (Liverpool Echo)

Majiyar (Calciomercato - in Italian) ta ma ce Liverpool din na kuma sa'ido kan dan wasan Juventus da Argentina Paulo Dybala.

Barcelona na duba yiwuwar yin wani garambawul da zai sa ta saka yan wasanta kasuwa, da suka hada da Frenkie de Jong, da Sergio Dest da Marc-Andre ter Stegen da Umtiti da kuma Philippe Coutinho.(Gerard Romero, via Sun)

Asalin hoton, Reuters

Borussia Dortmund ce gaba-gaba wurin son sayen dan wasan gaban Red Bull Salsburg Karim Adeyemi, wanda ake rade-radin Bayern Munich da Liverpool na nema. (Goal)

Ita kuwa PSG na duba yiwuwar rage yan wasanta da suka hada da Mauro Icardi da Rafinha da kuma Abdou Diallo. (L'Equipe - in French, subscription required)

A nan kuma dan wasan gaban Real Madrid Vinicius Junior ne ya gargadi kungiyarsa cewa kar ta sa kudi kansa don bai shirya barin kungiyar ba. (Vamos, via Marca)

Manchester United na daga cikin kungiyoyin da ke sha'awar daukar Vinicius Junior daga Madrid. (Mirror)