Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Lingard, Haaland, Lukaku, Icardi, Ndidi, Felix, Ramsey, Pedri, da Januzaj

Wifred Ndidi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wifred Ndidi

Newcastle ta tuntubi Manchester United, kan batun kai karshen cinikin Jesse Lingard a watan Janairu. (Sun)

Manchester United za ta nemi daya daga cikin yan gaba, Erling Haaland na Dortmund, ko Joao Felix na Atletico Madrid ko Timo Werner na Chelsea ko kuma matashin dan wasan Sweden Alexander Isak.

United na shirin sayen sabon dan gaba ne yayin da ake tunanin Edinson Cavani zai koma Barcelona. (Mail)

Dan wasan gaban Chelsea da Belgium Romelo Lukaku zai koma buga wasa a gasar Serie A ta Italiya kafin ya yi ritaya a cewar wakilinsa. (Tuttosport, via Goal)

Real Madrid ta nuna sha'awar sayen dan wasan Leicester da Najeriya Wilfred Ndidi, don maye gurbin Casemiro a tsakiya. (Naija)

Juventus ta shirya sauraren tayi kan yan wasanta Weston McKennie da Aaron Ramsey da kuma Arthur a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Brighton na shirin kwace matashin dan wasan tsakiyar Poland Kacper Kozlowski da ke wasa a Pogon Szczecin. (Mail)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyoyi da yawa na son Erling Haaland

Barcelona za ta nemi Adnan Januzaj da zarar kwantiraginsa da Real Sociedad ya kare a karshen kaka. (Mail)

Haka ma Barcelona ta kyalla ido kan dan wasan gaban Manchester United Anthony Martial, watakila idan ta kasa samun Ferran Torres. (Sport - in Spanish)

Matar Mauro Icardi da wakilinsa na tattaunawa da PSG don duba yiwuwar komawar dan wasan Juventus a Italiya. (Fichajes - in Spanish)

A nan kuma dan wasan tsakiyar Sifaniya Pedri ya ce yana jin dadin zama a Barcelona duk da sha'awar da Manchester City ta nuna ta daukarsa. (Tuttosport - in Italian)