EFCC ta bankado gwamna a Arewa da ya kwashi tsabar kudi Naira biliyan 60

Ma'aikatan EFCC

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Bawa ya ce ma'aikatan sabon sashensu na leken asiri ne suka gano gwamnan

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta'annati ta Najeriya, EFCC, ta ce ta bankado wani gwamna na wata jihar arewacin kasar da ya kwashi tsabar kudi har naira biliyan 60 daga asusun jiharsa.

Hukumar ta bayyana haka ne a sakon da take aike wa manema labarai wata-wata mai taken EFCC Alert.

EFCC, wadda ta ambato shugabanta Abdulrasheed Bawa yana yin karin bayani game da batun a hirarsa da mujallar da hukumar take wallafawa, ta ce gwamnan da aka gano na wata jiha ce da ke Arewa ta Tsakiya ko da yake bai fadi sunansa ba.

"Zan iya gaya muku a kyauta cewa sabon sashen da muka bude kan leken asiri yana aiki tukuru.

"Ya bankado abubuwa da dama. Daya daga cikinsu shi ne wani gwamna a wata jiha ta Arewa Ta Tsakiya, inda suka gano cewa cikin shekara shida da suka gabata (mutum daya) ya cire tsabar kudin da suka kai N60 bn."

"Muna kallon abubuwan da yake yi, kuma ina tabbatar muku cewa bayan mun kammala bincike, za mu sanar da 'yan Najeriya kan abubuwan da muka yi a bayan fage game da laifukan da ake aikatawa ta amfani da shafukan intanet...," in ji Bawa.