Mohammed bin Salman

Yadda ya zama yarima mai jiran gadon na Saudiyya

Mohammed Bin Salman over a filtered photo of Riyadh

Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman (MBS) na kawo sauye-sauye da kokarin zamanantar da kasar mai tsattsauran ra'ayin rikau.

Sai dai ya jefa kasar cikin yakin kasar Yemen, baya ga tsare masu fafutukar neman 'yancin mata da malaman addini da masu rubuce-rubuce a intanet. Ana kuma zarginsa da daukar nauyin kisan Jamal Khashoggi mai sukar gwamnatin kasar, a bara.

Wanene mutumin da ake kira MBS?

Mai daukar hira

Jedda mai makwabtaka da Bahar Maliya ta kasance cikin tsananin zafi a Satumban 2013. Mun samu shiga fadar Saudiyya bayan dogarai sun bude mana kofa. Mun shafe kwanaki kafin mu samu izinin ganawa da tsohon yarima mai jiran gado kuma ministan tsaro Salman bin Abdulaziz

Shekaru kafin nan Yarima Salman ya yi gwamnan Riyadh inda a 2004 'yan bindiga suka yi mana kwantar bauna. Sun harbe mai daukar mini hoto Simon Cumbers dan kasar Irelan, ni kuma suka harbe ni sau shida suka bar ni rai kwakwai, mutu kwakwai. An ba ni labarin cewa yariman ya je ya duba ni a asibiti. Amma ba zan iya tunawa ba saboda a lokacin ban san inda nake ba.

Salman, mai fama da rashin lafiya, yanzu shi ne Sarki. Ko a 2013, da muke zaune a dakin tarbar bakin fada, na lura cewa yana dogara sanda.

Yana ta murmushi a tsawon hirarmu da shi, inda yake magana a hankali da harshen Turanci, yana ba ni labarin yadda Landan ke burge shi.

Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya

Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya

Ya ga sauye-sauye na ban-mamaki. A matsayin gwamnan babban birnin kasar na kimanin shekara 50, Salman ya ga irin sauye-suyen da suka sa Riyadh ta bunkasa daga garin sahara mai mutane 200,000 ta zama babban birni mai mazuan miliyan biyar.

A tsawon hirarmu da basaraken, ban iya ganowa kai tsaye ba cewa akwai wani a zaune a baya yana daukar hirar tamu.

A lokacin na yi kuskuren tunanin cewa mutumin shi ne sakataren yariman. Mutumin dogo ne kakkarfa sanye da alkyabba ta alfarma.

Da muka gama hirar, sai na gabatar wa mutumin da kaina, muka gaisa da, muka yi musabaha da shi na tambaye shi sunansa.

Sai ya amsa da cewa “Sunana Yarima Salman,” cikin kankan da kai. Ya kara da cewa “Ni lauya ne. Mahaifina ne kuka yi hira da shi.”

A wannan lokaci ko kadan ba ni da masaniyar cewa wannan matashin dan shekara 28 zai zamo daya daga cikin shugabanni mafiya karfin iko da wuyar sha'ani a yankin gabas ta tsakiya ba.

Khashoggi

Hoton da kyamarar CCTV wanda TRT World ta ce na dan jarida dan asalin Saudiyya, Jamal Khashoggi ne a sadda ya isa karamin ofishin jakadancin Saudiyyar a Istanbul, Turkiyya a ranar 2 ga Oktboba, 2018

Ganin karshe da aka yi wa Jamal Khashoggi, yana shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul

Ganin karshe da aka yi wa Jamal Khashoggi, yana shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul

2 ga watan Oktoba da karfe 1:14 na rana, Jamal Khashoggi ya shiga wani gida mara alama a yankin Levent da ke birnin Istanbul.

Khashoggi wanda fitaccen marubuci ne kuma mai sukar MBS, ya je karamin ofishin jakadancin Saudiyya ne domin karbar takardun shaidar rabuwar aurensa.

Amma da shigarsa ofishin sai jami'an tsaro da masu tattara bayanan sirri daga Riyadh suka rinjaye shi, suka kashe shi kuma suka yi wa gawarsa gunduwa-gunduwa suka zubar. An kasa gano inda suka kai sassan jikin nasa.

Dubban mutane sun mutu a yakin da ya daidaita kasar Yemen, yawancinsu sakamakon harin sama da Saudiyya ke jagoranta. Daruruwan masu sukar tsare-tsaren MBS na tsare a gidajen kaso. Duk da haka kisan gillar da aka yi wa dan jaridar ne ya sa yawancin kasashen duniya suka raba gari da yarima mai jiran gadon.

Duk da musantawar da gwamnatin Saudiyya ta yi, hukumomin tattara bayanan sirri na yammacin duniya sun yi amannar cewa akalla tun da fari MBS ya san cewa za a kawar da Khashoggi. Rahotanni na nuwa cewa, hukumar CIA ta yi amannar cewa shi ne ya ba da umurnin kisan.

A hirar da aka yi da shi wacce gidan talabijin na CBS ya gabatar ranar 29 ga watan Satumba, har ta kai ga yariman "ya dauki alhakin" abin da ya faru. Gabanin hakan, a wata hirar da PBS ta yi da shi, yariman ya ce abin "ya faru ne a karkashin kulawarsa." Amma hakan ba ya nufin daukar alhakin abin da gwamnatinsa ke ci gaba da musawa.

Daya daga cikin masu hannu a kisan gillar shi ne wani hadimin MBS mafi kusanci da shi wato Saud Al-qhatini, wanda kuma tsohon jami'in sojan sama ne, mai shekara 41.

Kafin sallamarsa daga aiki bisa umurnin Sarki Salman bayan kisan Khashoggi, Al-qahtani shi ke yin iso ga bakin yarima mai jiran gado a kotun fadar.

Jamal Khashoggi

Jamal Khashoggi

Ana zargin Al-qahtani da gudanar da wani shirin tsattsauran binciken ta intanet na bibiyar aikace-aikacen 'yan kasar a gida a kasashen waje ta hanyar amfani da wata manhaja mai yin kutse ta daukar sauti da bayanai daga wayoyin jama'a ba tare da saninsu ba.

Masu sukar MBS da tsare-tsarensa sun yi ta samun sakonnin zagi da barazana ga rayuwarsu a shafukansu na sada zumunta. Al-qahtani wanda ke da mabiya fiye da miliyan daya a shafinsa na Twitter, ya yi amfani da damar wurin tattara bayanai da ake amfani da su a ci mutunci da kuma razana mutanen da ake gani a matsayin abokan gaba.

Jamal Khashoggi ya fahimci cewa yana cikin hadari bayan da a 2017 aka yi ta kamawa da tsare masu fafutukar kare hakkin dan Adam da masu wallafe-wallafe a intanet da masu gangamin neman mulkin dimokuradiyya da sauransu.

A watan Yunin bara ne Khashoggi ya gaggauta ficewa daga Saudiyya zuwa gudun hijira a Amurka bayan an nada MBS a matsayin yarima mai jiran gado.

Khashoggi mai shekara 59 na yi wa kansa lakabi da dan kishin Saudiyya. A baya ya taba zama mashawarcin jakadan Saudiyya a Landan. A lokacin nakan ziyarce shi har mu sha shayi tare.

Amma bayan komawarsa Amurka sai ya rika rubuta makala a jaridar Washington Post wacce a ciki ya ke sukar salon kama-karya na MBS. Hakan ya dagula wa yariman lissafi, a cewar wasu bayanai.

Dan jaridar ya yi ta samun kiraye-kirayen waya na neman sa ya koma Saudiyya tare da alkawarin kariya da ba shi mukami a cikin gwamnati.

Sai dai bai yarda da tabbacin da aka ba shi ba. Ya kuma sanar da abokansa cewa Al-qahtani da 'yan tawagarsa sun yi kutse a sakonninsa na email sun karanta sakonni da ganawar da ya yi da wasu 'yan adawa.

Khashoggi da sauransu sun yi shirin kaddamar da wani gangamin neman fadin albarkacin baki a yankin gabas ta Larabawa. Yana da magoya baya miliyan daya da dubu dari shida kuma fitaccen dan jarida ne a yankin gabas ta tsakiya.

MBS da na hannun damansa na ganin Khashoggi a matsayin babbar barazana. Amma yariman ya musanta hakan a hirarsa da CBS.

Daya daga hotunan da ke kan shafin tuwita din Saud al-Qahtani

Daya daga hotunan da ke kan shafin tuwita din Saud al-Qahtani

Jami'in dan sandan Turkiyya tsaye a wajen kofar karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul

Jami'in dan sandan Turkiyya tsaye a wajen kofar karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul

A tsawon tarihi gwamnatin Saudiyya ta sha sace 'yan kasar da take gani sun kauce hanya daga wasu kasashe, tana mayar da su Riyadh domin mayar da su kan hanya. Cikinsu har da 'ya'yan sarakuna, amma ba su kisa a kasashen waje domin yin haka ba ya cikin tsarin aikin.

Mutuwar Khashoggi ta yi saurin zama babbar badakala ta kasa-da-kasa.

Baya ga bayanai da ta yi masu cike da rufa-rufa a game da abin da ya samu Khashoggi a Istanbul, hukumomin Saudiyya sun yi iya bakin kokari wurin nesanta MBS da badakalar.

Sun ce kisan Khashoggi aikin masu zarce iyaka ne ko masu daukar doka a hannunsu. Amma CIA da sauran hukumomin tara bayanan sirri na wasu kasashen yammacin duniya sun saurari sautin kisan gillan wanda takwararsu ta kasar Turkiyya MIT ta nada daga karamin ofishin jakadancin Saudiyyan.


Domin karin bayani, za a iya kallon Shekara daya da mutuwar Jamal Khashoggi a shafin BBC da kuma fassarar rahoton Jane Corbin's report, Yadda aka yi gunduwa-gunduwa da Jamal Khashoggi


Da Amurka ta fitar da jerin sunayen wasu mutum 17 da ta sa wa takunkumi saboda zarginsu da hannu a kisan, sunan Al-qahtani shi ne na farko a jerin.

Zuwa yanzu babu wata tabbataciyar hujja da ke dora laifin kisa a kan MBS.

Sai dai CIA ta yi wani zuzzurfan bincike a kan kisan. Mujallar Wall Street Journal ta samu kwafen rahoton binciken wanda ya nuna wasu rubutattun sakonni 11 da MBS ya aike wa Al-qahtani kafin lokacin da kuma bayan kisan Khashoggi.

A nan dole a fede biri har wutsiya. Ni na zauna a kasashen Larabawa na yankin Gulf kuma na yi aiki na shekaru a yankin. Babu wani jami'in da ya isa ya dauki doka a hannunsa ko ya zarce iyaka. Hakan ba zai yiwu ba. Ba a yin komai sai da sa hannun wani babba.

A watan Agustan 2018 kafin kashe Khashoggi, Saud Al-qahtani ya wallafa wata magana a shafinsa na Twitter inda yake cewa "Shin an dauka gaban kaina nake yi ba mai lura da ni ne? Ni ma'aikaci ne kuma mai aiwatar da umunin sarki da na yarima mai jiran gado."

Ba wani wanda ke zargin cewa Sarki Salman da kansa na da hannu a kisan ba. Amma da alama manyan makusantan dan shi ne suka shirya kisan. "Hankali ma ba zai dauka ba a ce MBS ba shi da masaniya a kai", a cewar wani tsohon jami'in tattara bayanan sirri na kasar Birtaniya.

“Kisan Khashoggi tabo ne ga kasarmu da gwamnatinmu da kuma jama'armu”
Yarima Khalid bin Bandar al-Saud, Jakadan kasar Saudiyya a birnin Landan

Ina Al-qahtani yake kuma me ya sa ba a gurfanar da shi ba?

Tambayar da na yi wa sabon jakadan Saudiyya a Landan ke nan, Yarima Khalid bin Bandar Al-Saud. Jakadan ya tabbatar mini cewa an sallami Al-qahtani daga aikinsa kuma ana bincikar sa. Kuma idan aka sami Al-qhatanin da hannu za a gurfanar da shi. Sai dai wasu rahotanni daga Riyadh na nuna cewa ko da yake Al-qahtani ya daina fitowa bainar jama'a, amma ba tsare shi ake yi ba.

"Ba ya halartar zaman kotu ne saboda yana lura da shirin tsaro na intanet da wasu ayyuka," in ji wani mazaunin yankin Gulf kuma masanin makusantan MBS. "Ba ya fitowa bainar jama'a ne, amma suna ci gaba da amfani da kwarewarsa."

Mai sharhin ya kara da cewa makusantan MBS na ganin Al-qahtani shi ne wanda ya yi aikin a madadin tawagar. "Tabbas an samu akasi a abun da aka yi [a Istanbul], amma shi umurnin da aka ba shi ya zartas."

Gwamnatin Saudiyya ta gurfanar da mutum 11 da zargin kisan Khashoggi. Yanzu wata 9 ke nan da fara shari'ar amma babu wata kwakkwarar magana game da samun laifi, ko horo, ko sadda za a kammala shari'ar.

Bangaren shari'ar Saudiyya ya yi kaurin suna wurin yin rufa-rufa, inda ake ganin a wasu lokuta alkalai na yin radin kansu wurin yanke hukuncin da suka ga dama ba tare da bin wani tsarin doka ba.

Mataimakain shugaban hukumar tara bayanen sirri, Manjo Janar Ahmed Al-assiri na daga cikin mutanen da hukumomin kasar ke zargi. Al-assiri shi ne tsohon kakakin rundunar da Saudiyya ke jagoranta mai kai hare-haren sama a kasar Yemen.

Na sha haduwa da Al-assiri a Riyadh. Ba za ta yiwu Al-assiri ya iya kitsa wani abu ba sai ya samu izinin na gaba da shi.

Duk yadda sakamakon shari'ar ta kasance, akwai abu daya. Kisan da Khashoggi ya yi wa kimar MBS da kasar Saudiyya babban tabo da zai dade a idon duniya.

A watan Satumba jakadan Saudiyya a Landan ya tabbatar mini cewa "Ina magana da babbar murya. Kisan Khashoggi ya yi babban tabo garemu da kasarmu da gwamnatinmu da 'yan kasar. Na so a ce hakan ba ta faru ba."

Kisan Khashoggi ya haifar da zanga-zanga a fadin duniya

Kisan Khashoggi ya haifar da zanga-zanga a fadin duniya

2 ga watan Oktoba 2018 da misalin karfe 1:14 na rana Jamal Khashoggi ya shiga wani gini mara alama a yankin Levent a birnin Istanbul.

Fitaccen dan jaridar kuma mai sukar MBS ya je karamin ofishin jakadancin Saudiyya ne domin tantance takardun shaidar rabuwar aurensa.

Bayan shigarsa sai jami'an tsaro da masu leken asiri 'yan ina-da-kisan daga Riyadh suka danne shi suka kashe kuma suka yi mishi gunduwa-gunduwa suka zubar da namansa a inda ba za a iya gani ba.

Jamal Khashoggi

Jamal Khashoggi

Dubban mutane sun mutu a yakin da ya daidaita kasar Yemen, yawancinsu sakamakon hare-haren saman da Saudiyya ke jagoranta. Daruruwan masu sukar tsare-tsaren MBS kuma na tsare a gidajen kaso. Amma wannan kisan gillar da aka yi wa dan jarida ne ya yi sanadiyyar yawancin kasashen duniya suka juya wa yarima mai jiran gadon baya.

Duk da cewa hukumomin kasar Saudiyya sun musanta zargin, hukumomin tara bayanan sirri na yammacin duniya sun yi ammar cewa akalla tun da farko MBS na da masaniyar cewa za a kawar da Khashoggi. Rahotanni na cewa CIA ta na kyautata zaton shi ne ya bayar da umurnin.

A wata hirar awa daya da aka yi da MBS wanda gidan talabijin na CBS ya gabatar ranar 29 ga watan Satumba, sai da ta kai ga yariman "ya dauki alhakin dukkan" abin da ya faru. Sai dai ba za a iya cewa ya amsa laifin ba abin da shi da gwamnatin kasarsa ke ci gaba da musawa.

Wani muhimmin abun lura a wannan kisan gillar shi ne daya daga cikin hadiman MBS mafiya kusanci Saud Al-qhatini, kuma tsohon jami'in sojan mai shekara 41.

Kafin sallamar Al-qahtani daga aiki bisa umurnin Sarki Salman bayan kisan Khashoggi, Al-qahtanin shi ke yin iso ga bakin yarima mai jiran gado.

Ana zargin Al-qahtani da gudanar da wani shirin tsattsauran binciken ta intanet da ke bibiyar harkokin 'yan Saudiyya a gida da ketare ta amfani da wata manhaja mai yin kutse da daukar sauti da bayanai daga wayoyin jama'a ba tare da saninsu ba.

Masu sukar MBS da tsare-tsarensa sun yi ta samun sakonnin zagi da barazana ga rayuwarsu a shafukansu na sada zumunta. Kasancewar Al-qahtani yana da mabiya fiye miliyan daya a shafinsa na Twitter, hakan ya ba shi damar tattara bayanai da ake amfani da su wurin cin mutunci da yi wa mutanen da ake gani a matsayin abokan gaba barazana ga rayuwarsu.

Shafin tuwita na Saud al-Qahtani's

Shafin tuwita na Saud al-Qahtani's

A 2007 an yi ta kamawa ana kuma tsare masu fafutukar kare hakkin dan Adam da masu wallafe-wallafe a intanet da masu gangamin neman mulkin dimokuradiyya da sauransu. A nan ne Jamal Khashoggi ya fahimci cewa yana cikin hadari.

Bayan nada MBS a matsayin yarima mai jiran gado a cikin watan Yunin shekarar da ta gabata, sai Khashoggi ya yi gaggawar ficewa daga Saudiyya zuwa gudun hijira ta kashin kai a Amurka.

Khashoggi mai shekara 59 mai yi wa kansa lakabi da dan kishin Saudiyya shi ne tsohon mashawarcin jakadan Saudiyya a Landan kan yada labarai. A wannan lokacin nakan ziyarce shi har mu sha shayi tare.

Bayan komawarsa Amurka sai ya rika yin rubuce-rubuce da ke sukar salon kama-karya na MBS a jaridar Washington Post, wanda a ciki ya ke sukar salon kama-karya na MBS.

Dan jaridar ya yi ta samun kiraye-kiraye daga Riyadh na neman sa ya koma Saudiyya tare da Khashoggi bai aminta da tabbacin da aka ba shi ba. Ya kuma sanar da abokansa cewa Al-qahtani da yaransu sun yi kutse a email dinsa sun karanta sakonni da ganawar da ya yi da wasu 'yan adawa.

Khashoggi da sauransu sun yi shirin kaddamar da gangamin neman fadin albarkacin baki a yankin Larabawa. Ya samu magoya baya miliyan daya da dubu dari shida kuma fitaccen dan jarida ne a yankin gabas ta tsakiya.

Shi kuma MBS da na hannun damansa na ganin Khashoggi a matsayin babbar barazana. Sai dai yariman ya musanta hakan a wata hirar da ya yi da CBS.

Tarihi ya nuna cewa gwamnatin Saudiyya ta sha sace 'yan kasar wadanda take gani sun kauce hanya daga wasu kasashe, tana mayar da su Riyadh domin 'mayar da su kan hanya'. Cikinsu har da 'ya'yan sarauta, amma ba a kashe irin wadannan mutane a kasashen waje domin ba ya cikin tsarin aikin.


Kofar karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul

Kofar karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul

Domin karin bayani, za a iya kallon Shekara daya da mutuwar Jamal Khashoggi a shafin BBC da kuma fassarar rahoton Jane Corbin's report, Yadda aka yi gunduwa-gunduwa da Jamal Khashoggi


Mutuwar Khashoggi ta yi saurin zama babbar badakala a duniya.

Baya ga bayanai da ta yi masu cike da rufa-rufa a game da abin da ya samu Khashogi a Istanbul, kasar Saudiyya ta yi iya bakin kokari wurin nesanta MBS da badakalar kisan Khashoggi.

Hukumomin kasar sun ce kisan Khashoggi aikin masu zarce iyaka ne ko masu daukar doka a hannunsu. Amma CIA da sauran hukumomin tara bayanan sirri na kasashen yammacin duniya sun saurari faifan sautin kisan gillar, wanda takwararsu ta Turkiyya MIT ta nada daga karamin ofishin jakadancin Saudiyyan.

Da Amurka ta fitar da sunayen wasu mutum 17 da ta kakaba masu takunkumi saboda zarginsu da hannu a kisan Khashoggi, sunan Al-qahtani shi ne na faro a jerin sunayen.

Zuwa yanzu babu wata tabbataciyar hujja da ke dora laifin kinsa a kan MBS.

Sai dai an ga rubutattun sakonni 11 da MBS ya aike wa Al-qahtani kafin, lokacin da kuma bayan kisan Khashoggi a rahoton binciken da CIA ta yi kan kisan wanda Mujallar Wall Street Journal ta samu kwafensa.

Kisan Khashoggi ya jawo zanga-zanga a fadin duniya

Kisan Khashoggi ya jawo zanga-zanga a fadin duniya

A nan dole a fede biri har wutisya. Na zauna a kasashen Larabawa na yankin Gulf kuma na yi aiki na shekaru a yankin. Babu wani jami'in da ya isa ya dauki doka a hannunsa ko ya zarce ka'ida a yankin. Hakan ba zai yiwu ba. Ba a yin komai a yankin Gulf sai da sa hannun wani babban.

A watan Agustan 2018 kafin kashe Khashoggi, Saud Al-qahtani ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "Shin an dauka gaban kaina nake yi ba mai lura da ni ne? Ni ma'aikaci ne kuma mai aiwatar da umunin sarki da na yarima mai jiran gado."

Ba a cewa Sarki Salman da kansa na da hannu a kisan ba. Amma da alama manyan makusantan dansa ne suka shirya kisan. "Hankali ma ba zai dauka ba a ce MBS ba shi da masaniya a kai", in ji wani tsohon jami'in tara bayanan sirri na kasar Burtaniya.


“Kisan Khashoggi tabo ne ga kasarmu da gwamnatinmu da kuma jama'armu”
Yarima Khalid bin Bandar al-Saud, Jakadan kasar Saudiyya a birnin Landan

Ina Al-qahtani yake kuma me ya sa ba'a gurfanar da shi ba?

Wannan ita ce tambayar da da na yi wa sabon jakadan Saudiyya a birnin Landan, Yarima Khalid bin Bandar Al-saud. Jakadan ya tabbatar mini cewa an sallami Al-qahtani daga aiki kuma ana bincikar sa. Kuma idan aka sami Al-qhatanin da hannu za a gurfanar da shi. Sai dai wasu rahotanni daga Riyadh sun ce duk da cewa Al-qahtani ya daina fitowa bainar jama'a, amma ba tsare shi ake yi ba.

"Ba ya halartan zaman kotu ne saboda yana lura da shirin tsaro na intanet da wasu ayyuka," inji wani mazaunin yankin Gulf kuma masanin makusantan MBS. "Ba ya fitowa bainar jama'a ne kawai, amma suna ci gaba da amfani da kwarewarsa."

Mai sharhin ya kara da cewa mukarraban MBS na ganin Al-qahtani a matsayin wanda ya yi aikin a madadin tawagar. "Tabbas an samu akasi a abun da aka yi [a Istanbul], amma shi umurnin da aka ba shi ya zartas."

Gwamnatin Saudiyya ta gurfanar da wasu mutum 11 bisa zargin kisan Khashoggi. Wata 9 bayan fara shari'ar amma har yanzu babu wata kwakkwarar magana game da samun laifi, ko horo, ko sadda za a kammala shari'ar.

Ana zargin bangaren shari'ar Saudiyya da yawan yin rufa-rufa, inda ake ganin alkalai kan yi gaban kansu wurin yanke hukuncin da suka ga dama ba tare da yin dogaro da wani tsarin doka ba.

Wani babban jami'in gwamnatin kasar da hukumomi ke zargi shi ne Manjo Janar Ahmed Al-assiri. Al-assiri shi ne mataimakain shugaban hukumar tara bayanen sirri kuma tsohon kakakin rundunar da Saudiyya ke jagoranta mai kai hare-haren sama a kasar Yemen.

Manjo Janar Ahmed al-Assiri

Manjo Janar Ahmed al-Assiri

Ni na sha haduwa da Al-assiri a Riyadh.kuma na san ba yadda za a yi Al-assiri ya iya shirya wani abu ba tare da ya samu izini daga sama shi.

Duk yadda sakamakon shari'ar ta kasance, akwai abu daya. Kisan Khashoggi ya yi wa kimar MBS da kasar Saudiyya babban tabo da zai dade a idon duniya.

A watan Satumba jakadan Saudiyya a Landan ya tabbatar mini cewa "Ina magana da babbar murya. Kisan Khashoggi ya yi babban tabo garemu da kasarmu da gwamnatinmu da 'yan kasar. Na so a ce hakan bata faru ba."

Saudiyya mai sassauci?

Wata mata 'yar asalin Saudiyya na tuka mota bayan karfe 12 na dare a Riyadh a karon farko, ranar 24 ga watan Yuni, 2018, bayan dokar ba wa mata izinin tuki ta fara aiki

Tana tuka mota a Riyadh bayan karfe 12 na dare, ranar 24/06/2018, bayan dokar ba wa mata izinin tuki ta fara aiki a kasar Saudiyya

Tana tuka mota a Riyadh bayan karfe 12 na dare, ranar 24/06/2018, bayan dokar ba wa mata izinin tuki ta fara aiki a kasar Saudiyya

A cikin dare ne a watan Disamba dumbin matasa maza da mata sanye tufafin Turawa sun taru a wani dakin taro inda suke daddaga wayoyinsu suna daukar hotuna suna sauraron kade-kade.

A wannan wuri kuma mata sun yi amfani da damar da sabuwar 'yancinsu na tuka motocinsu suka halarci gasar tseren motoci na Formula E a birnin Riyadh. Mawakan Turawa irinsu Black Eyed Peas da Enrique Iglesias sun shirya casu. Ga kuma makadi dan kasar Faransa, Dj David Guetta ya hallara da kayan kidansa.

Wannan ita ce sabuwar Saudiyya da yarima mai jiran gado ya kawo. Ya shigo da harkar shakatawa kuma an yi watsi da al'adu.

Duk wanda ya taba zama ko ziyartar Saudiyya shekara 40 da suka gabata, zai ga hakan a matsayin wani irin sauyi na yankan shakku.

Masu ayarin babura da motoci a Jeddah

Masu ayarin babura da motoci a Jeddah

A 'yan kwanakin baya ba za a yi tunanin yiwuwar samun irin wannan cudanyar maza da mata a kasar ba. Yin hakan ya haramta bisa fatawar manyan malaman kasar masu tsattsauran ra'ayi, wadanda gidan sarautan kasar ke rabewa da su domin samun karbuwa.

A iya sani na, mutanen Saudiyya masu kamun kai ne da bin addini, inda kuma 'yan sandan cikin gida (Mutawwa) suka rurrufe wuraren shan shisha a Riyadh kuma suka hana sanya kade-kade da raye-raye a shaguna, bisa tasu fahimtar addinin Islama.

Amma bayan zaman MBS yarima mai jiran gado sai ga shi yana ta kokarin kawo sauyi, na shakatawa tare da goyon bayan sarkin. A shekarun baya an haramta bude gidajen sinima wuraren casu da tukin mata a kasar. Amma yanzu yariman na neman sassauta wadannan abubuwan a kasar.

A 2018 Saudiya ta janye dokar haramta gidajen sinima a kasar

A 2018 Saudiya ta janye dokar haramta gidajen sinima a kasar

A 2017 MBS ya ce abubuwan da aka gani a shekaru 30 da suka gabata ba kasar Saudiyya ba ce. Bayan juyin juya halin kasar Iran a 1979, mutane sun yi ta kwaikwayansu a kasashe daban-daban, cikinsu har da kasar Saudiyya. Ba mu san yadda za a magance matsalar wacce ta yadu a duniya ba. Yanzu lokaci ya yi da za mu kawar da ita."

Ana iya cewa Saudiyya ba ta taba more rayuwar shakatawa ba kamar wasu manyan biranen kasashen Larabawa irinsu Al-kahiru da Baghdad. Amma duk da haka, kamalan MBS sun yi daidai da abun da fadar White House ke son ji.

A wannan lokaci an riga an kulla kawance tsakanin Washington da Yarima MBS. Shugaban Amurka Donald Trump ya zabi Riyadh a matsayin wurin da zai fara ziyarta a kasashen waje. Shi ma surukin Trump, Jared Kushner ya kulla dangantakar aiki da MBS.

Maris 2018: MBS da Donald Trumpa a fadar White House

Maris 2018: MBS da Donald Trumpa a fadar White House

A kokarinsa na bin tsarin "Islama mai tafiya daidai da zamani," Yarima Muhammad Bin Salman ya ba da izinin bude wuraren kade-kade da raye-raye da ma taron kiristoci 'yan darikar Coptic.

A Saudiyya kuma farin jinin MBS na karuwa, musamman a tsakanin matasa da suka gaji da kasancewa karkashin mutane 'yan sama da shekara 50. Shi ko MBS mai shekara 34, shi ne babban mutum na farko a kasar da matasan ke neman irinsa.

"Wani dan kasuwa a yankin Gulf ya ce "MBS na sha'awar abincin makulashe, irinsu hot dog, da kayan sha irin na kwalba. Mutum ne mai son kere-kere wanda ya taso yana yin abubuwa tare da jin cewa nauyi ne da ya rataya a wuyansa."

A wani taron tattalin arziki da aka yi a Riyadh, mata matasa 'yan kasar sun yi ta neman daukar hotunan selfie da Yarima MBS. Hakan ya faranta masa rai kuma ya amince, inda har ya sakar masu fuska tamkar wani mashahurin jarumin fim a wurin taron."

Wani lauya masanin harkokin kasa da kasa Malek Dahlan, ya ce "Kasar na bukatar shugaba irinsa. An dade ba a yi shugaba mai kwarjini irinsa ba, tun zamanin kakansa, Sarki Abdulaziz."

Da yake magana game da yawan karfin ikon MBS, tsohon jakadan Burtaniya a Saudiyya daga 2006 zuwa 2010, William Patey, ya ce "A fahimtata yawancin 'yan Saudiyya musamman matasa na goyon bayan yariman dan alkiblarsa. A baya sun saba ganin an rarraba madafun iko, amma yanzu sun fahinci cewa kawo muhimman sauyi na bukatar karfin ikon a wurin yanke hukunci."

Wani tsohon jakadan Burtaniya da ya sha haduwa da MBS, amma ya bukaci a sakaya sunansa ya ce:

“MBS ya yarda a kansa fiye da misali. Yana da basira and karsashi wani lokaci har da zumudi da kan iya nuna yarinta."

Bayan haka akwai wani abu mara dadi:

Dakile tawaye

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam a ofishin jakadancin Saudiyya a Paris

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam a ofishin jakadancin Saudiyya a Paris

Idan neman sanin dabi'un MBS ake, idan so ake a siffanta halayyar MBS kokarinsa na kawo sauye-sauyen da yake yi, to shi mutum ne wanda ke don dole a yi yadda yake so. "A takaice MBS ba ya lamuntar masu bore.'

Mawallafa a intanet da malaman addini da masu zanga-zangar kare hakkin mata da mutane masu tsattauran ra'ayi da ma masu sassaucin ra'ayi da dama sun tsinci kansu a tsare, a karkashin wasu tsauraran dokoki a kokarinsa MBS na murkushe masu neman bijirewa ko neman tattaunawa kasar.

Rahoton kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch na 2018 ya ce "hukumomin Saudiyya sun yawaita tsare mutane ba gaira, ba dalili da kuma gurfanarwa da hukunta masu zanga-zangar lumana da masu fafutuka, ciki har da kai samame a kan kungiyoyin kare hakkokin mata."

Amma ba shi ne shugaban da daga karshe ya ba wa mata 'yancin tuka mota ba? Eh, haka ne. Amma masu sa ido sun ce MBS na so ne a samu sauyin daga sama zuwa kasa. Daga fadar gwamnati zuwa kasa.

Ana ganin babban hadari ne kowane irin neman sauyin dokoki sakamakon wani gangami a kan tituna komai kankantarsa a kasar da babu jam'iyyun siyasa ko na adawa.

Alal misali Dauki Loujain Al-hathloul, 'yar boko ce mai basira kuma fitacciya a shafukan sada zumunta. An tsare ta har ta yi bikin cikarta shekara 30 a gidan yari a Jeddah a wutan Yulin da ya gabata.

A cewar danginta, laifin da ta yi shi ne neman a ba wa matan kasar izinin tuki. Tana kuma neman a janye karfin ikon da maza ke da shi na lura da rayuwar matayensu da danginsu mata.

Yanzu an sauya dokokin biyu. Mata na iya yin tuki, kuma an sassauta dokar kulawar.

Amma da alamar gwamnatin Saudiyya ba ta ji dadin abin da Loujain Al-hathloul da sauran mata masu fafutukar suka yi ba, kasancewar MBS zai so a ce shi ne ya kawo sauyin. Kar mutum ya sake ya nemi kawo sauyi cikin gaggawa a kasar.

A 2014 aka fara tsare Loujain bayan ta tuka motarta daga Hadaddiyar Daular Laraba (UAE) ta shigo Saudiyya. Rahotanni sun ce a watan Maris na 2018 ayarin wasu motoci sun tsayar da ita a UAE, sannan suka kama ta suka mayar da ita Saudiyya inda aka tsare ta na lokaci. An sake tsare ta a watan Mayun 2018 a cikin wani babban samame.

Loujain da sauran mata 'yan fafutukar na zargin an azbatar da su kuma an tsare su a killace su kadai ne.

Lyn Maalouf na kungiyar Amnesty ya ce a watanni ukun farkon tsarewar an gana wa matan nau'ukan azaba da suka hada da yi musu bulala da sanya lantarki ta ja su da kuma keta mutuncinsu."

Hukumomin Saudiyya sun musanta zargin azabtarwa a gidajen yarin kasar ko ofisoshin 'yan sanda. Hukumomin sun kuma yi alkawarin bincikar gaskiyar zargin. Sai dai maimakon a hukunta jami'an gwamnatin da ake zargi, sai aka gurfanar da matan da suka yi zargin a gaban kotu.

Dan uwan Loujain mai suna Walid mazaunin wata kasa ya ce ba a binciki zargin azabtarwar da aka yi wa 'yar uwar tasa ba. Ya ce "Sau uku muna aikawa da takardar koke amma babu amsa. Alkalin ya dogara ne da rahoton hukumar kare hakkin dan Adam ta Saudiyya wurin yanke hukunci amma ba a gudanar da bincike mai zaman kansa ba." Walid na kuma neman a binciki Saud Al-qahtani wanda Loujain ke zargin yana cikin wadanda suka ci zarafinsu a sadda suke tsare.

Loujain al-Hathloul

Loujain al-Hathloul

Loujain al-Hathloul

Loujain al-Hathloul

Aziza al-Yousef

Aziza al-Yousef

A wata hirar minti 60 da aka yi da MBS, an kalubalance shi a kan zargin cin zarfn mata fursunoni. Yariman ya yi alkawarin bincikar zargin da kansa.

Kasashe fiye da 30 sun bukaci Saudiyya ta saki masu fafutukar wadanda galibinsu a baya kotu ta bayar da belinsu. Amurka da Burtaniya sun ce sun kai maganar sama. Amma a watan Agusta, dangin Loujain sun yi zargin cewa jami'an tsaro sun sha zuwa wurinta a gidan yari suna tilasta mata ta rattaba hannu a wata takardar da ke musanta zargin da dangin nata ke yi cewa ana azabtar da ita. Amma ta ki.

Sauran mata masu fafutuka da aka tsare sun hada da Samar Badawi, wadda aka tsare saboda kalubalantar dokar kula da mata. Da Iman al-Nafjan, mawallafiya a intanet wadda ta nemi a ba wa mata 'yancin tuki. Sai Aziza al-Yousef, tsohuwar malamar jami'a wadda taimaki wasu mata suka tserata daga cin zarafi.

Sai dai a cikin Saudiyya ba'a ba da wata kulawa ta a zo a gani ga bukatun matan ba. Kafafen yada labaran kasar basu fiye daukar labarin matan ba. Ana kuma kallon matan a matsayin maciya amanar kasa da ake zarginsu da ba wa makiya sirrin kasar.

Sau da dama ana tsarewa da hukunta mata masu fafutuka.

A watan Satumban 2018, alkalan kasar sun sanar da hukuncin daurin shekara biyar da tarar riyal miliyan uku (N267,000,000) a kan duk wanda aka kama da laifin yada wani abun da zai iya gurbata tarbiyya ko tayar da zaune tsaye a kasar.

Kuma MBS ba ya nadamar matakan da yake dauka a kan masu bore. A lokuta da dama da aka yi hira da shi, yariman ya amsa cewa an tsare mutane da yawa. Sai dai ya ce yin hakan na iya zama wajibi ta wata fuska, idan har ana so a kawo sabbin tsare-tsare masu muhimmanci.

Yaya aka yi mutumin da ya shekara shida ba ya ba a san shi ba, ya zamo mai karfi sosai a yankin gabas ta tsakiya?

Idan neman sanin dabi'un MBS ake, Idan so ake a siffanta halayyar MBS kokarinsa na kawo sauye-sauyen da yake yi, to shi mutum ne wanda ke sawa don dole a yi yadda yake so. "A takaice MBS ba ya lamuntar masu bore.'

Mawallafa a intanet da malaman addini da masu zanga-zangar kare hakkin mata da mutane masu tsattauran ra'ayi da ma masu sassaucin ra'ayi da dama sun tsinci kansu a tsare, a karkashin wasu tsauraran dokoki a kokarinsa MBS na murkushe masu neman bijirewa ko neman tattaunawa a kasar.

Rahoton kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch na 2018 ya ce "hukumomin Saudiyya sun yawaita tsare mutane ba gaira, ba dalili da kuma gurfanarwa da hukunta masu zanga-zangar lumana da masu fafutuka, ciki har da kai samame a kan kungiyoyin kare hakkokin mata."

Two women in full headdress, in Jeddah

Amma ba shi ne shugaban da daga baya ya zo ya ba wa mata 'yancin tuki ba? Haka ne. Amma masu sa ido sun ce MBS na so ne a samu sauyin daga sama zuwa kasa. Daga fadar gwamnati har kasa.

Suna ganin cewa babban hadari ne duk wani nau'in neman sauyin dokoki sakamakon wani gangami a kan tituna, komai kankantarsa a kasar da babu jam'iyyun siyasa ko na adawa.

Alal misali Dauki Loujain Al-hathloul, 'yar boko ce mai basira kuma fitacciya a shafukan sada zumunta. An tsare ta har ta yi bikin cikarta shekara 30 a gidan yari a Jeddah a wutan Yulin da ya gabata.

A cewar danginta, laifin da Loujain ta yi kawai shi ne neman a ba wa matan kasar izinin tuki da kuma sassauta karfin ikon maza na lura da harkokin matayensu da danginsu mata.

Loujain al-Hathloul

Loujain al-Hathloul

Yanzu an sauya dokokin biyu. Mata na iya yin tuki, sanan an sassauta dokar kulawar maza a kan mata.

Sai da alamar matakin da da Loujain da sauran matan masu fafutuka sauka dauka bai yi wa gwamnatin Saudiyya dadi ba saboda MBS ya so a ce shi ne ya kawo sauyin. Ba ya son gangancin nema kawo sauyi cikin gaggawa a kasar.

A 2014 aka fara tsare Loujain bayan ta tuka motarta daga Hadaddiyar Daular Laraba (UAE) ta shigo Saudiyya. Rahotanni sun ce a watan Maris na 2018 ayarin wasu motoci sun tsayar da ita a UAE, sannan suka kama ta suka mayar da ita Saudiyya inda aka tsare ta na lokaci. An sake tsare ta a watan Mayun 2018 a cikin wani babban samame.

Loujain da sauran mata 'yan fafutkar na zargin an azabtar da su kuma an tsare su a killace su kadai ne.

Lyn Maalouf na kungiyar Amnesty ya ce a watanni ukun farkon tsarewar da aka yi wa matan an gana masu nau'ukan azaba da suka hada da yi musu bulala da sanya lantarki ta ja su da kuma keta mutuncinsu."

Zanga-zangar da aka yi a Faransa na adawa da tsare mata masu fafutuka a Saudiyyya

Zanga-zangar da aka yi a Faransa na adawa da tsare mata masu fafutuka a Saudiyyya

Mahukuntan Saudiyya sun musanta zargin azabtarwa a gidajen yarin kasar ko ofisoshin 'yan sanda. Hukumomin sun kuma yi alkawarin bincikar gaskiyar zargin. Sai dai maimakon a hukunta jami'an gwamnatin da ake zargi, sai aka gurfanar da matan da suka yi zargin a gaban kotu.

Dan uwan Loujain mai suna Walid mazaunin wata kasa ya ce ba'a binciki zargin azabtarwan da aka yi wa 'yar uwar tasa ba. Ya ce "Sau uku muna aikawa da takardar koke amma babu amsa. Alkalin ya dogara ne da rahoton hukumar kare hakkin dan Adam ta Saudiyya wurin yanke hukunci amma ba agudanar da bincike mai zaman kansa ba." Walid na kuma neman a binciki Saud Al-qahtani wanda Loujain ke zargin yana cikin wadanda suka ci zarafinsu a sadda suke tsare.

A watar hirar minti 60 da aka yi da MBS, an kalubalance shi a kan zargin cin zarfn mata fursunoni. Yariman ya yi alkawarin bincikar zargin da kansa.

Kasashe fiye da 30 sun bukaci Saudiyya ta saki masu fafutukar wadanda galibinsu a baya kotu ta bayar da belinsu. Amurka da Burtaniya sun ce sai an kai maganar sama. Amma a watan Agusta, dangin Loujain sun yi zargin cewa jami'an tsaro sun sha zuwa wurinta a gidan yari suna tilasta mata ta rattaba hannu a wata takardar da ke musanta zargin da dangin nata ke yi cewa ana azabtar da ita. Amma ta ki.

Sauran mata masu fafutuka da aka tsare sun hada da Samar Badawi, wadda aka tsare saboda kalubalantar dokar kula da mata. Da Iman al-Nafjan, mawallafiya a intanet wadda ta nemi a ba wa mata 'yancin tuki. Sai Aziza al-Yousef, tsohuwar malamar jami'a wadda ta taimaki wasu mata suka tsere daga cin zarafi.

Aziza al-Yousef

Aziza al-Yousef

Sai dai a cikin Saudiyya ba a ba da wata kulawa ta a zo a gani ga bukatun matan ba. Kafafen yada labaran kasar basu fiye daukar labarin matan ba. Ana kuma kallon matan a matsayin maciya amanar kasa da ake zarginsu da ba wa makiya sirrin kasar.

A lokuta da dama an sha tsarewa da hukunta mata masu fafutuka.

A watan Satumban 2018, kotuna kasar sun sanar da hukuncin daurin shekara biyar da tarar riyal miliyan uku (N267,000,000) a kan duk wanda aka kama da laifin yada wani abun da zai iya gurbata tarbiyya ko tayar da zaune tsaye a kasar.

Kuma MBS ba ya nadamar matakan da yake dauka a kan masu bore. A lokuta da dama da aka yi hira da shi, yariman ya amsa cewa an tsare mutane da yawa. Sai dai ya ce yin hakan na iya zama wajibi ta wata fuska, idan har ana so a kawo gagaruman sauye-sauye.

Yaya aka yi mutumin da ba a san shi ba shekara shida da suka wuce ya zamo mai karfi sosai a yankin gabas ta tsakiya?

Dan kasa

An haifi Mohammed bin Salma a ranar 31 ga watan Agusta 1985. Ya taso cikin kulawa da rayuwa ta alfarma kamar sauran 'ya'yan gidan sarautar su kimanin 500.

A matsayin daya daga cikin 'ya'ya 13, MBS ya taso cikin tsaro da kulawa a cikin fadar da ke yankin Madher. Ga kuma hadimai da ma'aikata da suka hada da dogarai masu girki da direbobi har daga kasashen ketare domin biyan dukkan bukatunsa.

Cikin wadanda suka kula da shi yana yaro akwai Rachid Sekkai wanda yanzu ma'aikacin BBC ne. Ya taba siffanta yadda Rachid ke daukarsa a mota da Rachid din ke tukawa daga gida yana kai shi fada.

"Idan aka wuce kofar mai cike da masu gadi, sai motar ta biya ta wasu gine-gine na alfarma masu kayatattun lambuna da ma'aikata masu fararen kayan aiki ke kulawa da su," kamar yadda ya sheda BBC. Akwai wurin ajiye motoci cike motocin alfarma."

A wasu rahotannin an kwatanta MBS cewa hazikin dalibi ne da a koyaushe yake rubuta abubuwan da ake koyar da shi. Amma Rachid Sekai ya ce yana ganin MBS ya fi jin dadin zama da ma'aikatan fiye da lokacin da ya yake dauka yana bitar darussansa.

"Kamar akan bar shi ya yi yadda yake so." in ji shi.

Mahaifinsa ya ba shi dama zuwa ya yi karatu a kasashen wajen ko Amurka ko Burtaniya kamar sa'o'insa amma ya MBS ya ce a'a. Maimakon haka, sai ya yi karatun digirinsa na farko a fannin shari'a a jami'ar Sarki Saud. Masu sharhi na ganin wannan zabin da ya zi wanda ba'a saba gani ba ya taimaka masa ta wata fuska kuma ya takaita shi ta wata fuskar.

Yawancin 'yan Saudiyya na ganin tasowarsa a kasar ta sa ya zama cikakke ne "dan kasa," kamar yadda wasu ke kiran shi. Sai dai illar a ganin wasu ita ce hakan ya sa an dauki tsawon lokaci turancin MBS bai yi kwari ba kuma bai samu cikakkiyar fahimtar yanayin yammacin duniya kamar sauran 'ya'yan sarauta ba.

Duk da cewa a kasar an saba namiji ya auri mata hudu, amma MBS ya zabi zama da mata daya. MBS ya auri 'yar uwarsa ta dangi, Sara bint Mashur bin Abdulaziz Al-saud a 2009. 'Ya'yansu hudu, maza biyu mata biyu. Game da sha'anin iyalinsa kuma, MBS ba ya bayyanawa.

Yaya aka yi yau MBS ya yi saurin sama zama yarima mai jiran gado mai karfin iko haka, daga cikin dubban 'ya'yan gidan sarautar, alhali da can ba a fiye sanin shi ba.

Amsar ita ce kwarewa a siyasa da dabi'unsa da kuma karbuwarsa a wurin mahaifinsa.

Jirgin ruwan shakatawa na alfarma wanda MBS ya saya a kan Euro miliyan 500 (N193,000,000,000)

Jirgin ruwan shakatawa na alfarma wanda MBS ya saya a kan Euro miliyan 500 (N193,000,000,000)

Sadda MBS ke dan shekara 23, bayan kammala jami'a da kyakkyawan sakamako, sai mahaifinsa ya fara shirya shi domin rike mukami a gwamnati.

MBS ya yi aikin a fakaice a ofishin mahaifinsa wanda a lokacin shi ne gwamnan Riyadh. A lokacin, MBS ya mayar da hankali, inda ya lakanci yadda yarima Salman ya rika sulhuta rikici da daidaita tsakani cikin nasara.

A 2013 MBS na dan shekara 27 aka nada shi shugaban fadar yarima jiran gado. Daga nan aka yi masa karin girma zuwa matsayin minista.

A 2015 likafa ta ci gaba inda ya samu karin girman.

Jerin Sarakunan kasar Saudiyya daga Sarki Abdul Aziz zuwa Salman

Jerin Sarakunan kasar Saudiyya daga Sarki Abdul Aziz zuwa Salman

Bayan rasuwar Sarki Abdullah a watan Janairun shekarar, sai dan uwansa Salman daga gidan Sudairi ya gaji mulkinsa. A lokacin sabon sarkin na da shekara 80 a duniya. Bayan hawansa mulki, sarki Salman shi ke da ikon zabar wanda zai gaje shi. Nan take aka nada dansa na gaban goshi Mohammed bin Salman a matsayin ministan tsaro kuma sakataren gwamnati.

Yanzu Saudiyya na fama da rikici a iyakanta na kudanci. A makwabciyarta Yemen, 'yan kabilar Houthi daga tsaunukan arewacin kasar sun kwace babban birnin kasar Sana'a kuma sun hambarar da zababben shugaban kasar da gwamnatinsa, baya ga karbe kusan dukkan yankin yammacin kasar wanda shi ne bangare mafi yawan jama'a.

'Yan Houthi sun yi tarayya ta fuskar ra'ayi da akida da kasar Iran. Haka ya sanya Saudiyya cikin dar-dar. Ba tare da tuntubar sauran manyan 'ya'yan sarki ba kuma ba tare da sanar da kawayen Saudiyya ba, a watan Maris na 2015 MBS ya gayyato kawancen kasashe 10 inda ya jagoranci kasarsa fara yakin sama da 'yan Houthi.

Manufar gwamnatin Saudiyya ita ce dawo da gwamnatin zababben shugaban Yemen da MDD ta amince da shi da kuma aike wa kasar Iran sako cewa Saudiyyar ba za ta bari 'yan tawayen da Iran din ke goyon baya su kwace ikon Yemen ba. An yi hakan ne a matsayin wani matakin soji na gaggawa domin dakile 'yan tawayen masu dauke da makamai irin na zamanin tarayyar Soviet.

Amma sai kilu ta ja bau inda Saudiyyar ta yi asarar rayuka da dukiyoyi baya ga daidaita Yemen.

Jami'in tsaron iyakar Saudiya ya fuskaci Yemen

Jami'in tsaron iyakar Saudiya ya fuskaci Yemen

Babu wata nasarar a zo a gani da rundunar hadin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta ta yi a Yemen. Shekaru kusan biyar ke nan yaki ya daidaita Yemen kuma ya yi ajalin dubban mutate. Rashin abinci mai gina jiki da zazzabin cizon sauro da sauran cututtuka sun yadu a kasar. Mutane kimanin miliyan 20, kusan kashi biyu cikin ukun jama'ar kasar na cikin tsananin bukatar dauki.

A Saudiyya kuma, farkon kaddamar da yakin ya jawo wa MBS farin jiki nan take. MBS ba shi da wata masaniya a kan aikin soji, amma gidan talabijin na kasar ya rika nuna shi a matsayin wani jarumi da ya dauki matakin da ya dace domin kare muradun kasarsa.

Da farko kasashen yammacin duniya sun mara wa Saudiyya baya. Amurka ta ba da kayan yaki da mai da kuma tara bayanne sirri. Burtaniya ta taimaka da motoci da dabaru da kuma shawarwari kan amfani da kayan yaki. An kuma ajiye manyan hafsoshin sojin saman Burtaniya biyu a cibiyar tsaro da ke Riyadh domin kula da hare-haren saman da ake kaiwa. Sai dai ma'aikatar tsaron Burtaniya ta ce ba hafsoshin ke zabar wuraren da ake kai wa hari ba.

Sai dai yawancin hare-haren saman da mayakan saman Saudiyya ke kaiwa a Yemen kan yi rashin sa'a.

Irin barnar da yaki ya yi a Yemen

Irin barnar da yaki ya yi a Yemen

Hare-haren sun sha fadawa a kan asibitoci da taron jana'iza da gidaje da makarantu tare da kayayyakin aikin soji. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa yawancin mace-macen da suka auku a Yemen sun faru ne ta sanadiyyar hare-haren da Saudiyya ke jagoranta. Ana zargin dakarun Saudiyya da harba bama-bamai masu 'ya'ya a yankunan farar hula.

Su ma 'yan Houthi ana zarginsu da aikata laifukan yaki da dasa nakiyoyi barkatai da amfani da kananan yara a matsayin mayaka da kai wa harbin gidaje da katse hanyar isar kayan agaji. Gwamnatin Saudiyya ta yi zargin cewa zuwa watan Satumban 2019, 'yan Houthi sun harba makamai masu linzami fiye da 260 da kuma jiragen yaki marasa matuka guda 50 zuwa cikin Saudiyya. Sai dai wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta da irin matsanancin karfin sojin sama da rundunar hadin gwiwar da Saudiyyar ke jagoranta take amfani da shi.

Al'ummomin kasashen yammacin duniya bisa jagorancin kungiyoyin kare hakkin dan Adam ciki har da Amnesty International na ci gaba da nuna bacin ransu game da zubar da jinin da ake yi a Yemen.

A cikin shekara biyar Yemen ta zama kasar da ta fi bukatar agaji a fadin duniya.

Iko da fahimta

Ritz Carlton Hotel, Riyadh

Ritz Carlton Hotel, Riyadh

A ranar 20 ga watan Yunin 2017 wani abin ya faru a fadar dake Makka wanda kuma ya sauya tarihin kasar Saudiyya. A ranar Sarki ya kira yarima mai jiran gado fada, kuma bukace shi ya sauka daga mukamin ya bar wa MBS, mai karancin shekaru kuma dan dan uwansa.

Mohammed bin Nayef ya kwashe shekaru a matsayin babba jami'in tsaron kasar Saudiyya. A matsayinsa na shugaban yaki da ta'addanci yarima Mohammed bin Nayef ne ya jagoranci dakile tayar da kayar bayan kungiyar Al-qaeda a wuraren shekara ta 2000, kafin daga baya a nada shi ministan harkokin cikin gida. Amuka na sonsa kuma ta yarda da shi, duk da cewa ba shi da kwarewa a bangarori masu yawa. A lokacin ana ganin shi ne tsayayyen wanda zai gaji sarautar kasar.

Dalilin da aka bayar shi ne cewa har a lokacin bai gama farfadowa daga harin da kungiyar Al-qaeda ta kai masa a 2009 ba inda dan kunar bakin waken kungiyar ya yi irin shigar Mohammed bin Nayef din har ya shiga dakin da yake ciki.

Sarki Salman ya riga ya yanke shawarar wanda yake so ya zama magajinsa wanda kuma shi ne dan gaban goshinsa wato MBS.

A tsarin Saudiyya sarki na da cikakken iko, don haka babu mahawara kuma babu jayayya. Tuni dai aka daina ganin Mohammed bin Nayef a matsayin jami'i.

An daina ganin tsohon yarima mai jiran gado Mohammed Bin Nayef a bainar jama'a

An daina ganin tsohon yarima mai jiran gado Mohammed Bin Nayef a bainar jama'a

MBS da mahaifinsa sun yi abin da za a iya kwatantawa da juyin mulki ba tare da zabar da jini ba.

Burinsa na kokarin sauya fasalin kasar ta sa MBS bai yi kasa a gwiwa ba wajen jaddada karfin ikonsa.

Da magaribar Asabar 4 ga watan Nuwamban 2017, aka bayar da umurnin tsare wasu manyan 'ya'yan sarki da 'yan kasuwa kusan 200. Ba a tuhume su ba kuma ba'a kai su gidan yari ba, amma aka tsare su a wani katafaren otal na alfarma mai suna Ritz-Carlton Hotel da ke Riyadh. Daga cikinsu akwai wadanda suka yi watanni a tsare.

A matakin da ake gani a matsayin yunkurin yaki da zamba ne, an nemi sabbin bakin otal din da su sallama biliyoyin riyal da ake zargi sun samu ta haramtattun hanyoyi ne kafin a sake su.

Amma 'yan adawa MBS na ganin matakin ba komai rashawa ba ne illa kokarin nuna karfin iko da nufin karya lagon duk mai neman ya kalubalance shi.

Bugu da kari MBS ya tadiye 'ya'yan marigayi sarki Abdullah, daya daga cikin zuri'a masu karfi a cikin dangin. Tuni kuma ya mayar da rassan tsaron kasar karkashin ikonsa: kama daga ma'aikatar harkokin cikin gida da rundunar soji da kuma masu tsaron kasa(National Guard).

Tsare mutanen da aka yi a otal din Ritz-Carlton ya girgiza 'yan kasuwa da masu zuba jari daga kasashen ketatre. Ba su san wane ne babu hadari a cikin yin huldar kasuwanci da shi ba.

Har yanzu akwai 'yan Saudiyya matalauta a birnin Jidda da ke gabar Tekun Maliya

Har yanzu akwai 'yan Saudiyya matalauta a birnin Jidda da ke gabar Tekun Maliya

Duk da hakan 'yan kasan da dama sun yaba da matakin. Ana iya cewa Saudiyya ce aksar da ta fi hako danyen mai, amma 'yan kasar da dama na fama da talauci musamman a yankin kudanci. Ganin an kama wasu manyan 'yan kasuwan kasar da a baya ake ganin ba sa tabuwa ya kara wa MBS farin jini a tsakanin 'yan kasar.

Abin da ya kara masa farin jini a kasar kuma shi ne kokarinsa na bunkasa tattalin arzikin kasar ta wasu bangarorin da ba na man fetur ba. MBS na kokarin mayar da kasar cibiyar zuba jari da samar da ayyuka ga miliyoyin matasan kasar da ba su da aikin da zai iya rike su.

Shirinsa na Vision 2030 wani babban muradi ne na kawo kasar ci gaba nan da 2030. Shirin na da burin mayar da kasar Saudiyya wata cibiya ta duniya da ke hada nahiyoyin Turai da Asiya da kuma Afirka na ba da dadewa ba.

Shirin ya tanadi dala biliyan 64 domin bunkasa bangaren shakatawa da samar da miliyoyin sabbin ayyuka a bangaren yawon bude ido.

MBS ya kaddamar da shirin Vision 2030 a Riyadh a watan Afrilun 2016

MBS ya kaddamar da shirin Vision 2030 a Riyadh a watan Afrilun 2016

Sai dai kisan Jamal Khashoggi na neman dagula lissafi. Wasu masu zuba jari daga kasashen wajen sun rage wasu kuma sun janye goyon bayansu ga shirin na Mohammed bin Salman. 'Yan kasuwan na gudun a danganta su da mutumin da duniya ke zarginsa da hannu a kisan Khashoggi.

Hakan bai hana ci gaba da shirin Vision 2030 ba, wanda ya tanadi wani shiri na musamman domin rayuwar kasar a nan gaba mai suna NEOM - (Neo-Mustaqbal a Larabci), wato sabuwar rayuwa ta nan gaba.

Akwai kuma shirin kirkiro da wani katafaren birni na karnin na 21 a yankin arewa maso yammacin kasar inda Tekun Maliya ya hada kasar da kasashen Masar da Jordan da Isra'ila.

The front page of the official NEOM website

Ana tunanin akasarin abubuwan da za su mamaye birnin NEOM su ne jirage marasa matuka da giza-gizan dan adam masu amfani da hasken rana da na'urorin masu basira da motoci marasa matuka da na'urori masu amfani da mai da aka samar daga tsirrai da mutummutumi masu yin hidima.

A hukumance za a bude birnin ne a shekarar 2025. Amma wasu masana tattalin arziki na tababar haka.

"Kai, ba zai taba yiwuwa ba," in ji wani. "Maganar NEOM rudu ne kawai, kuma shi ne bambanci tsakanin irin buri da yakikin da MBS ke kallon duniya."

MBS na da kwarin gwiwa a game da shirin wanda aka sheda min cewa MBS ya yi imanin cewa NEOM zai zama kishiyar Palo Alto babbar cibiyar fasaha da ke California.

Saudiyya ba ta da wani tarihi na a zo, a gani game da batun gina biranen da aka tsara saboda wata manufa ta musamman.

"Alal misali ana son a samu mazauna miliyan biyu a babban birnin kasuwanci na Sarki Abdulaziz nan da 2020. Amma har yanzu mazauna kimanin 8,000 ne birnin. Don haka da wuya a cimma wannan buri," a cewar wasi masanin tattalin arzikin yankin Gulf.

Nasarar da aka samu a binin kasuwanci na Sarki Abdulaziz Economic City bata burge ba

Nasarar da aka samu a binin kasuwanci na Sarki Abdulaziz Economic City bata burge ba

Har yanzu akwai alamu za a gina NEOM amma ginin birnin na tafiyar hawainiya sabanin yadda aka shirya da farko. Akwai kalubale da dama a halin yanzu. Amma akwai kokwanton cewa birnin zai jawo 'yan kasuwa da masu zuba jari dage ketare da samar da ayyukan yi.

Daga baya

MBS's face on a billboard

A watan Satumban 2018, Boris Johnson ya yi tafiyar kwana uku zuwa Saudiyya, inda masu masaukin bakinsa suka kashe fam 14,000 wajen daukar nauyin tafiyar, kuma majalisar kasar ce ta amince da hakan. Boris bai san komai game da tafiyar na, amma hakan ya faru ne mako biyu kafin a kashe Jamal Khashoggi.

Maris 2018: MBS tare da sakataren harkokin wajen Burtaniya Boris Johnson a layin Downing Street

Maris 2018: MBS tare da sakataren harkokin wajen Burtaniya Boris Johnson a layin Downing Street

Kafin kashe Khashoggi, tsare masu fafutukar da ba a fiye ba da rahoto ba a wajen kasar, MBS na samun karin magoya a cikin shugabannin kasashen yammacin duniya.

Amma daga baya, da wuya a yi tunanin irin wannan ziyara za ta yiwu.

Yanzu ana nisantar MBS musamman a bainar jama'a a kasashen yammacin duniya inda a baya suke ganin sa a matsayin mai hangen nesa da neman kawo daidaito da sauye-sauye.

"Kashe Jamal Khashoggi ya sa ana kallon Saudiyya tamkar gungun 'yan ina da kisa,' a cewar wani mai sharhi a yankin Gulf. "Tamkar kisan ya sanya MBS a matsayi daya da irinsu Gaddafi da addam da Assad. A da can ba ruwan Saudiyya da irinsu."

A kebe kuma kasuwancin kasar na ta habaka. Tattalin arzikin Saudiyya na da girma sannan akwai riba mai tsoka wadda 'yan kasuwan yammacin duniya ba za su iya kyalewa ba. Har yanzu Shugaba Trump na Amurka babban abokin Saudiyya ne.

Majalisar dokokin Amurka sun sha yin kokarin hana kasar sayar wa Saudiyya makamai na biliyoyin daloli. Amma Trump ya kayar da su saboda dalilai na kasuwanci da dabaru.

Muhimmacin yin kasuwanci da Saudiyya da matsayin da take da ne na kalubalantar kokarin da Iran take yi na fadada karfin ikonta na iya sa kasashen yammacin duniya su sassauta adawarsu ga Saudiyya. Amma tun tuni kyamar da yammacin duniya ta nuna a kan tauye hakki a Saudiyya ya yi tasiri a Riyadh.

Larabawan na kokarin sauya salo. Sabuwar jakadiyar Saudiyya a Washington ita ce Gimbiya Reema bint Bandar Al-saud. Gimbiya Reema ita ce mace ta farko da ta zama jakadar kasa kuma gogaggiyar 'yar kasuwa ce da ta kwashe shekaru a Amurka.

Reema ce za ta zama fuskar gwamnatin Saudiyya a birnin Washington inda 'yan majalisar kasar ke sanya ayar tambaya a kan halascin kawancen Amurka da Saudiyya.

Gimbiya Reema bint Bandar Al-saud, jakadiyar Saudiyya a Washington

Gimbiya Reema bint Bandar Al-saud, jakadiyar Saudiyya a Washington

Amma Saudiyya ba ta duba yiwuwar kulla kawance da wasu muhimman kasashe irinsu Rasha da Canada da Pakistan. A cikinsu babu wanda ya kalubalanci zargin tauye hakkin jama'a a Saudiyya.

A watanni 12 da suka gabata wasu muhimman kalamai da zarge-zarge sun kunno kai daga jami'an hukumar tara bayanan sirri na Amurka da babbar jakadan Majalisar Dinkin Duniya, Agnes Callamard. Zarge-zargen sun sake tunatar da duniya cewa kasashen yammaci na zargin MBS ne da kanshi ya sa a kashe Khashoggi. Agnes Callamard ta dage cewa wajibi ne MBS ya fuskanci hukunci.

A gida kuma farin jin MBS na kara karuwa. "Duk dan shekara 16-25, za ka samu sun dauke shi a matsayin jarumi. Suna son sauye-sauyen harkoki da yake kawowa wanda ke rage ayyuakan masu tsattsauran ra'ayin addini," a cewar wani mai sharhi kar yankin Gulf.

Babu wata babbar alamar da ke nuna cewa Saudiyya za ta yi wani kwakkwaran kokarin komawa tsarin dimokuraddiya a karkashin MBS. Duk wanda ya kalubalanci gidan sarautar ko ko ya soke tsare-tsarenta a fili na iya cin dauri.

MBS ya samu cikakken goyon bayan mahaifinsa Sarki Salman na tsawon shekaru kuma babu wata barazana ga kujerarsa. Makusantan MBS a cikin fada kuma na ganin cewa guguwar da ta taso a yammacin duniya kan rawar da MBS din ya taka a kashe Khashoggi za ta zama tarihi. Watakila suna da gaskiya.

Ta fuskoki da dama ana iya cewa MBS shi ne Saudiyya. Baya goyon bayan dimokuraddiyya kuma ba ya neman kawo sauye-sauyen siyasa a kasar. Mutane da dama na daukar sa mai kama-karya. Amma babu shakka MBS mai zamantar da tattalin arziki da tsarin rayuwa ne. A shekara 34, ya san idan sarki ya rasu, shi ne zai zama shugaban kasa mafi girma a yankin gabas ta tsakiya na tsawon shekaru kusan 50 nan gaba.

MA'AIKATA

RUBUTAWA: Frank Gardner

DAUKAR HOTO: Alamy, Getty Images, Reuters, Shutterstock, Frank Gardner

SARRAFA HOTUNA: Debie Loizeau & Sana Jasmeni

HADAWA A INTANET: Ben Milne

EDITA: Finlo Rohrer