Masallacin Annabi SAW na Madina

Ziyara zuwa waje na biyu mafi tsarki a Musulunci, wanda ya samu shekara 1440 da suka gabata.

A view of the mosque

A view of the mosque

A view of the mosque

Babban Masallacin Madina shi ne na biyu a cikin masallatai mafiya daraja, wanda kuma Annabi Muhammad (SAW) ya fara jagorantar Sallah a cikin sa.

Masallacin Manzon Allah shi ne wurin da aka fara sanya hasken lantarki a fadin yankin Larabawa a 1909, kamar yadda Sultan Ghalib Al Quaiti ya fada a littafinsa, The holy cities, the Pilgrimage and the World of Islam.

Yadda aka kawata cikin masallacin da fitilu

Yadda aka kawata cikin masallacin da fitilu

Yadda aka kawata cikin masallacin da fitilu

Ana fadada shi ta yadda zai dauki mutum miliyan daya da dubu 800. Inuwar rumfunan alfarma masu sarrafa kansu kuma masu daukar mutum dubu 800 guda 250 da ke masallacin sun kai murabba'in mita dubu 143, kamar yadda shafin hukumar gudanarwar masallacin ya bayyana.

Nan gaba za mu kawo muku bayanai gwargwadon hali a kan tambayoyin da kuka aiko mana na abubuwan da kuke son sani game da Masallacin Manzon Allah SAW da ke Madina.

Hadisai sun nuna cewa Masallacin Manzon Allah SAW shi ne masallaci mafi tsarki da falala da girma a ban kasa, bayan Masallacin Makkah.

Shi ya sa ake wa masallatan biyu lakabi da masallatai biyu tsarkaka masu daukaka, wato Al-haramainush sharifain, da harshen Larabci.

Masallacin Manzon Allah, wanda ke kwaryar birnin Madina a kasar Saudiyya shi ne wuri da aka fara sanya wa hasken lantarki a fadin yankin Labarawa tun a shekarar 1909 miladiyya.

Fitaccen marubucin tarihin Manzon Allah SAW, Safiur-Rahman Mubarakfuriya ya bayyana a littafin Al-rahikul Makhtum cewa masallacin shi ne biyu da aka gina a Madina bayan masallacin Kuba..

A wancan lokaci an gina masallacin ne a kusa da gidan Annabi Muhammad (SAW) shekara ta farko bayan hijira daga Makka zuwa Madina (632 miladiyya).

Kuma sallah daya a masallacin Manzon Allah SAW ta fi sallah 1,000 da aka yi a wasu masallatai daraja, ban da masallacin Ka'aba.

Kabarin Manzon Allah SAW da na manyan sahabbansa biyu, Abubakar da Umar na cikin masallacin a yanzu, sakamakon fadada masallacin da aka yi a tsawon shekaru sama da 1,400, kaburburan na cikin wani daki da aka yi na kusa da mumbarin da ke cikin rauda, wanda a zamanin Annabi dakin matarsa ne Nana Aisha.

Sakamakon fadada wannan masallaci a tsawon zamani, yanzu Rauda ta shige cikin wanan masallacin. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa tsakanin gidana da mimbarina akwai dausayi daga cikin dausayin Aljanna. Wannan wuri shi ne Rauda.

Hoton masallacin daga sama a lokacin da rana ke faduwa

Hoton masallacin daga sama a lokacin da rana ke faduwa

Hoton masallacin daga sama a lokacin da rana ke faduwa

Girman Masallacin Madina

Saboda girman Masallacin Madinah ya kan dauke duk miliyoyin mahajjata da masu umrah da ke ziyartarsa a kowace shekara. Kuma shi ne wurin da mahajjata da masu umrah suka fi ziyarta a fadin Madina.

A nan suke yin sallah, su shiga Rauda in hali ya samu, su ziyarci Annabi SAW da sahabbansa a makwancinsu da kuma makabartar Baki'a.

Har yanzu ana ci gaba da fadada shi ta yadda zai iya daukar masallata kusan miliyan biyu a lokaci guda, saboda yadda yawan masu ziyartarsa ke karuwa a lokacin Hajji.

Girman masallacin a yau ya kai ninki 100 na yadda aka fara gina shi. Kuma ya kusa mamaye fadin asalin garin Madina a zamanin Manzon Allah SAW.

Sannan masallacin a bude yake a koyaushe domin masu ibada.

Baya ga manyan hasumiyoyi 10 masu tsawon mita 103 kowannensu, masallacin na da kubbobi (tulluwa) 170 da suka hada da masu ruwan azurfa da farare da wasu 27 na zamani masu sarrafa kansu.

Akwai kuma wata koriyar kubba babba a daidai saman inda kabarin Manzon Allah yake, ita ake wa kirari da Koriyar Kubba ta Dan Abdullahi. A gefen koriyar kubbar akwai wata kubba mai ruwan azurfa.

Girman Masallachin Madina

Ainihin girman masallachin Madina kusan kafa 98 ne da tsawon kafa 115, kamar yadda Zafar Bangash ya sanar a cikin tarihin Masallachin Annabi (SAW) da kuma Raudah da ake wallafawa a duk wata a mujallar Institute of Contemporary Islamic Thought. (ICIT)

To sai dai an yi ta fadada shi lokaci zuwa lokaci domin ganin an kara samun damar daukar masallata da dama daga gadin duniya musamman mahajjata, kasancewar sa daya daga cikin masallatai uku da musulunci ya yi umurni da a ziyarta.

Farfesa Dr Spahic Omer a wata kasida da ya rubuta mai taken ''The Prophet Muhammad (SAW) and the Urbanisation of Madinah'' ya ce masallacin a yanzu ya ninka ainihin girmansa sau 100 ya kuma mamaye kusan dukkanin fadin tsohon birnin Madinah.

Farfesan ya bayyana cewa katangar da ke kan iyakar masallacin a yanzu na makwabtaka da makbartar Al-Baqi wadda a zamanin Annabi SAW a wajen gari take kamar yadda Dr Muhammad Wajid Akhter ya rubuta a littafin '9 Things You Didn't Know About The Prophet's Mosque'.

Fadada masallacin da ake kan yi a halin yanzu wanda King Abdullah ya kaddamar a shekarar 2012 zai bai wa masallacin damar daukar masallata miliyan biyu.

Ministan kudin Saudiyya Ibrahim Assaf ya ce, ''Yayin da ginin zai mamaye ''murabbu'in mita 614,800, fadin ga baki dayan masallacin idan aka hada sauran gine-ginen da ke makale da shi zai kai murabbu'in mita 1,020,500. Hakan zai sa ya iya daukar masu ibada miliyan daya, da kuma wasu karin dubu 800 a harabar gine-gine.''

Kafar yada labaran Larabawa ta Arab News ta ruwaito mai magana da yawun masallacin Sheikh Abdulwahed Al-hattab na cewa Sarki Abdallah ya bayar da damar kafa lemomi 250 a farfajiyar masallacin da za su mamaye murabbu'in mita 143,000.

Lemomin na zamani da ke sarrafa kansu na katange masallata daga rana da kuma ruwan sama. Sheikh Hattab ya kara da cewa masallacin na da masu kula da shi sama da 3,200.

Ana sa ran kashi na biyu da na uku na ginin masallachin zai dauki sama da mutum miliyan daya,yayin da kashi na farko zai dauki masallata 800,000. Duk ana sa ran zai dauki masu mutane miliyan 1.2 daga nan zuwa shekarar 2040.

Some Minarets and Domes

Kula da masallacin

Kamar haramin Makka, shi ma Masallacin Manzon Allah SAW na karkashin kulawar ofishin Sarkin Saudiyya.

Shi ya sa ake kiran Sarkin Saudiyya mai kula da manyan haramai guda biyu (Khadimul haramainish sharifain) a Larabci.

Kula da masallacin ya kebanta ne da gwamnatin Saudiyya kuma ba tare da gudumowar wasu gwamnatoci ko attajirai ko kungiyoyi ba.

Dubban ma'aikata ne ke aiki dare da rana a masallacin, da suka hada da jami'an tsaro, da ma'aikatan lafiya da masu shara da goge-goge da sauran ma'aikata masu kula da kai-komon jama'a da kuma gudanarwa.

Shugaban sashen hulda da jama'a na fadar Sarkin Saudiyya kan harkokin Masallacin Manzon Allah SAW, Abdulwahed Hatab ya ce a kalla mutum 3,000 ne ke aikin tsaftace masallacin.

Wasu daga cikin manyan gine-ginen da ke zagaye da masallacin sun hada da makabartar Baq'i da ke bayan bangon yamma na masallacin.

A nan ne kaburburan daruruwan Sahabban Annabi (SAW) suke.

Sauran gine-ginen da ke zagaye sun hada da ma'aikatun gwamnati da asibitoci da otal-otal na alfarma da manyan shaguna da kuma manyan hanyoyi.

The Baq' graveyard

The Baq' graveyard

Some buildings surrounding the mosque

Some buildings surrounding the mosque

some neighbouring buildings

some neighbouring buildings

The Baq' graveyard

The Baq' graveyard

Some buildings surrounding the mosque

Some buildings surrounding the mosque

some neighbouring buildings

some neighbouring buildings

Limamin Masallacin Madina

Annabi Muhammad SAW shi ne ya fara jagorantar sallah a masallacin a tsawon rayuwarsa.

Bayan rayuwarsa sai aka yi ta samun wasu limamai karni bayan karni har zuwa yanzu.

A hirar tarho da muka yi da Dakta Jamilu Yusuf Zarewa, wanda tsohon dalibin Jami'ar Madina ne, ya bayyana wa BBC cewa a zahiri Manzon Allah bai nada na'ibi a lokacin rayuwarsa ba.

Sai dai a wasu lokuta ya kan umarci sahabinsa Abubakar ya yi wa mutane limanci.

Duk da haka hadisi ya tabbata cewa Manzon Allah ya taba shigowa masallaci a sadda Abubakar ke jagorantar sallah.

Daga nan sai sahabbai suka yi wa Abubakar ishara da cewa Manzon Allah ne ya shigo masallacin, sai Abubakar ya koma baya.

Daga nan sai Annabi (SAW) ya ci gaba da jan sallar.

Bayan rayuwar Manzon Allah kuma an yi ta samun limamai a masallacin har zuwa wannan lokaci.

Kuma limaman ba 'yan garin Madina ko kasar Saudiyya ba ne kadai.

Babban limaman masallacin na yanzu shi ne Sheik Abdul Rahman Al-huthaifiy.

Akwai kuma wasu limamai biyar masu jagorantar sallolin yau da kullum tare da shi a masallacin.

Sannan akan samu karin limamai masu mara masu baya musamman a lokacin Sallar Tahajjud.

Limaman a yanzu sun hada da:
• Sheikh Abdulrahman Ali Hudhayfee
• Sheikh Abdul Bari Ath Thubaiti
• Sheikh Salaah Budair
• Sheikh Abdullah Buayjaan
• Sheikh Ahmad Al Hudhayfee
• Sheikh Ahmad Taleb Hameed
• Sheikh Hussain Aal Sheikh
• Sheikh Imaad Zuhair Hafiz
• Sheikh Khalid Al Muhanna.

Wurin tsayawar limamin Madina (Mihrab)

Mihrab (wurin da liman ke jan sallah) da aka yi a masallacin a tsawon tarihi guda biyu ne kamar yadda Dakta Jamilu Yusuf Zarewa ya yi mana bayani.

Na farko shi ne Mihrab din da Manzon Allah ya jagoranci sallah a ciki a asalin masallacin da aka gina zamanin Manzon Allah SAW.

Wannan Mihrab din na dab da mimbarin Manzon Allah a wancan lokaci.

Wannan mihrabin shi ne ke hade Rauda kusa da Mukabbariyya (wurin da ake kiran sallah) a wannan zamani.

Za a iya fahimtar cewa yanzu an sauya wa wannan mihrab din fasali sakamakon gyare-gyare da fadadawar da aka yi wa masallacin tsawon zamani.

Na biyu shi ne Mihrab inda limamai ke jan sallah a yanzu, wanda ke bangon da ke barin alkibla na masallacin.

Mihrab din da limamai ke jan sallah a ciki na da tsawon tarihi tun zamanin khalifancin Usman.

Khalifa Usman Bn Affan shi ne na biyu kuma karshen wanda ya fadada masallacin ta bangaren kudu, wanda shi ne alkiblar masallacin.

Haka wani jami'i ya bayyana a wani rahoto na Musamman da Al-arabiyya ta yi kan Mihrab din Masallacin.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne na farko wanda ya jagoranci sallah a masallacin. Bayan wafatinsa, sahabbansa ne da tabi'an da suka biyo bayansu suka ci gaba da jagorantar sallar.

Manzon Allah (SAW) ba shi da na'ibi, duk da cewa yana sanya Abubakar (Babban amininsa) da ya jagoranci sallah, amma Manzon Allah (SAW) ya taba shiga masallaci a lokacin da Abubakar ke jagorantar sallah, amma sai Abubakar ya dawo baya inda Manzon Allah ya ci gaba da jagorantar sallar.

Amma bayan wafatin manzon Allah, Abubakar ya zama Khalifa na farko kuma limamin Madinah. Daga baya masallacin ya samu wasu limamai daga lokacin har zuwa yanzu.

Sheikh Abdul Rahman Al-Hudaify shi ne babban limamin amma a Juma'ar 11 ga watan Aktobar 2019, gwamnatin Saudiyya ta bayyana kari sabbin limamai guda biyu; su ne; Sheikh Ahmed Hudaify wanda 'dan babban limamin ne, da kuma Sheikh Khalid Al Muhanna.

Wasu wadanda suka sanya domin su rika jan sallar Tahajjud (sallar dare) .

Sheik Abdul Rahman Al-huthaifiy lead Imam, Madina mosque

Ladanan masallacin

Ladanin Masallacin Wanda Manzon Allah ya fara nadawa ya kira sallah a Masallacin Madina shi ne Bilal Bn Rabah.

Dokta Jamilu Zarewa ya yi mana karin bayani cewa bayan Abdullahi Bn Zaid ya yi mafarkin yadda ake kiran Sallah kuma Annabi Muhammad ya tabbatar da cewa mafarkin gaskiya ne, sai Annabi ya umarci Abdullahi ya koya wa Bilal yadda ake kiran sallah domin bilal ya rika kiran sallah a duk lokacin sallah.

Masu kiran sallah a masallacin na yanzu guda 17 ne karkashin jagorancin Sheik Abdulrahman bn Abdul'ilah bn Ibrahim, kamar yadda Sheikh Abdul Rahman ya shaida wa jaridar Saudi Gazette a shekarun baya.

Ladanan da ke kiran Sallah a masallacin yanzu, kamar yadda muka samu sunayensu daga ofishin da ke kula da shafin intanet na masallatan Makka da Madina su ne haka:

•Sheikh Adul Majeed Surayhi

• Sheikh Abdul Rahman Kashukji

• Sheikh Abdullah Hattab Al Hunaini

•Sheikh Adil Katib

•Sheikh Ahmed Afifi

•Sheikh Ahmed Ansari

•Sheikh Anas Sharif

•Sheikh Ashraf Afifi

•Sheikh Esam Bukhari

•Sheikh Faisal Noman

•Sheikh Hassan Kashukji

•Sheikh Iyad Shukri

•Sheikh Mahdi Bari

•Shiekh Muhammad Majid Hakeem

•Shiekh Muhammmad Qassas

•Sheikh Sami Dewali

•Sheikh Saud Bukhari

•Shiekh Umar Kamaal

•Sheikh Umar Sunbul

• Sheikh Usaama Akhdar.

Asalin masallacin Madina

A cewar Mubarakfuri lokacin da ya zo Madinah, shi ne ya sayi gonar da ake sanya dabino a kandinari 10 daga wasu marayu guda biyu, Sahl da kuma Suhail. A wannan filin ne taguwar Manzon Allah ta tsaya a Madina.

Manzon Allah (SAW) ya sanya hannu wajen ginin masallacin wanda aka yi da bangon laka a kan tubalin duwatsu. An yi amfani da jijiyoyin iccen dabino da ganyensa domin yin rufin.

Yana kallon masallacin Kudus (kudu) wanda a lokacin shi ne Al Kibla kuma yana da kofofi guda uku. Akwai inuwa sosai a bayan wurin inda ake aje marassa karfi da kuma baki, ''Al-Saffa.''

An mayar da shi Arewa lokacin da Al Kibla ta sauya zuwa Ka'aba. An rufe kofar ta kudu inda aka sauya ta da wata sabuwa da ke a Arewa.

Lokacin da sahabbai suka nemi da Manzon Allah ya taya su sanya wa shigifar tabo sai ya ki, ya ce ''A'a, wuri (arish) irin na Annabi Musa, rufi irin na Annabi Musa. Kasan wurin ba a rufe shi da komai ba sai bayan shekara uku.

"Ainihin girman masallacin kafa 1,050 ne kafin Annabi (SAW) ya yi umurnin a mayar da shi kafa 1425, shekaru bakwai bayan hijira.

Yadda lemomi suka kawata harabar masallacin

Yadda lemomi suka kawata harabar masallacin

Masu ziyara a gaban kabarin Manzon Allah SAW

Masu ziyara a gaban kabarin Manzon Allah SAW

Gidajen matayen Manzon Allah

A gefen masallacin ne Manzon Allah ya fara gina gidajen matansa, kuma anan ne aka binne shi bayan ya yi wafati - a dakin Nana Aisha.

Dr. Zarewa ya ce a yayin da Manzon Allah SAW ya yi wafati sai sahabbansa suka fara shawarar inda ya fi dacewa a binne shi, sai Sayyadina Abubakar ya shaida musu cewa Annabi SAW ya ce ana binne Annnabawa ne a wajen da Allah ya karbi rayuwarsu.

A sakamakon haka sai suka binne shi a inda ya rasu wato dakin Nana Aisha.

A lokacin da Sayyadina Abubakar, Khalifan farko ke jinya, sai ya nemi izinin Nana Aisha wadda take 'yarsa don a binne shi a dakinta kusa da Manzon Allah SAW, sai ta amince.

Sayyadina Umar ma hakan ya yi, ya roki Uwar Muminai Aisha 'yar Sayyadina Abubakar kuma ta amince aka binne Umar kusa da mijinta da mahaifinta a gidanta.

Sai dai aikin fadada masallacin da aka yi ta yi tsawon daruruwan shekaru sun sa kaburburan nasu sun shiga cikin masallacin sosai. Koriyar Khubba da ake cewa ta Dan Abdullahi a yanzu haka tana daidai saitin inda kaburburan suke ne.

Yana da kyau a fahimci cewa asali ba a cikin masallacin aka gina dakin A'isha ba. Akin fadada masallacin Manzon Allah a tsawon zamani ne ya sa a hankali har masallacin ya mamaye dakin, inda a nan aka binne Manzon Allah da manyan sahabbansa, da sauran gidaje masu makwabtaka da masallacin.Kwalliyar Masallacin Madina

The mosque's premises

The mosque's premises

An kawata Masallacin Manzon Allah da kayan ado iri-iri sai wanda ya gani. An yi wa ginin kwalliya da kayan alutun zayyana da tsari na alfarma da ban sha'awa.

Baya ga manyan hasumiyoyi 10 masu tsawon mita 103 kowannensu, masallacin na da kubbobi (tulluwa) 170 da suka hada da masu ruwan azurfa da wasu 27 na zamani masu sarrafa kansu.

Akwai kuma wata koriyar kubba babba a daidai saman inda kabarin Manzon Allah yake ita ake kira Koriyar Kubba Ta Dan Abdullahi. A gefen koriyar kubbar akwai wata kubba mai ruwan azurfa.

Kowace rumfar alfarma mai sarrafa kanta da ke masallacin na daukar mutum dubu 800. Irin wadannan rumfunan guda 250 a ne masallacin.

Yawan fitilu iri-iri da ke Masallacin Manzon Allah sun kai 10,300 masu ruwan zinare da siffofi iri-iri, kamar yadda wani jami'in ya shaida wa Khamis al-Zharani na gidan talabijin na Al-arabiya.

Jami'in ya ce karfin wutar da fitilun masallacin ke amfani da ita ya kai megawatt 32.

Akwai kuma injinunan samar da wutar lantarki guda takwas domin shirin ko-ta-kwana.

Ya ce kowanne daga cikin janaretocin na samar da megawatt biyu da rabi na lantarki.

Wani jami'i mai suna Saleh Lamei Mustafa a cikin wata makala da taibanet.net ta wallafa ya ce tun zamanin Khalifa Al-walid bn Abdulmalik aka fara kawata masallacin Manzon Allah ta hanyar kwalliya da ruwan zinare baya ga zanen rubutu na musamman da aka yi masa da kuma ado da duwatsu na alfarma masu launi iri-iri.

Shi ma Sarki Salim na daular Ottoman ya sa an yi wa gimshikan masallacin kwalliya da fararen duwatsu da masu launin shanshambale, wanda daga baya aka mai da kore.

A zamanin Sarki Sulaiman kuma aka yi Mihrab Al-hanafi kuma aka kawata shi.

Shi kuma Sultan Murad ya sa aka kawo wa masallacin wani mimbari na farin dutse da aka shafe jikinsa da ruwan zinare.

A shekarar 1849 miladiyya, Sarki Abdulmajid ya sa an kawata rufin masallacin da tulluwarsa da bangonsa da wasu kofofin masallacin.

A wannan lokacin sai da aka kwashe shekara 13 ana aikin kawata masallacin ta hanyoyi daban-daban.

An yi amfani da karau da kayan alatu masu launi iri-iri wurin yi wa masallacin ado da kwalliya da zayyana na rubutun Larabci da suka hada da ayoyin Al-kur'ani, da sunayen Allah da wasu alamomi.

Wasu kananan kubbobin da ke masallacin

Wasu kananan kubbobin da ke masallacin

Mai magana da yawun hukumar kula da masallacin Sheikh Abdulwahed Al-hattab, ya ce akwai lemomi 250 masu juyawa da kansu a harabar masallacin wadanda suke samar da inuwa ga masu ibada daga zafin rana ko ruwan sama. Lemomin wadanda suke hade da magudanun ruwa na iya bai wa masu ibada 800,000 inuwa kuma sun mamaye fadin murabbu'in mita 143,000.

Kofofi

A yau masallacin na da kofofin a kalla guda 41 cikinsu har da kofofi guda uku na masu keken guragu.
A saman kowace kofa an rubuta (Udkhulu ha bi salamin aminin) "Ku shiga cikinta da sallama kuna amintattu" da zayyana ta Larabci.

Akwai karin wasu kofofi da hanyoyi masu matakala a cikin masallacin da ke kai mutane hawa na daya na masallacin, inda a nan ma haraba ce, da rumfuna da kuma sarari.

Daga cikin kofofin akwai masu mashiga daya, wasu biyu, wasu uku, wasu biyar hadi da lifta mai matattakala da ke kai wa hawa na farko da kuma sauran wurare.

Idan aka hada duka kofofin da ke masallachin adadin su zai kai guda 85, kamar yadda aka samo daga Al-hattabi.

Ga jerin sunayen kofofin kamar yadda muka samo daga ma'aikatar da ke kula tafiyar da Masallachin Annabi da kuma shafin internet na madainproject.com

·        Bab Al-salam

·        Bab Abubakar Siddiq

·        Bab Al-rahmah

·        Bab Al-hijrah

·        Bab Quba

·        Bab Al-malik Sa'ud

·        Babu Imam Al-bukhari

·        Bab Al-aqiq

·        Bab Al-sultan Abdulmajid

·        Bab Umar bn Al-Khattab

·        Bab Badr

·        Bab Al-malik Fahd

·        Bab Uhud

·        Bab Usman bn Affan

·        Bab Ali bn Abi-talib

·        Bab Abu-zar

·        Bab Al-imam Muslim

·        Bab Al-malik Abdulaziz

·        Bab Makka

·        Bab Bilal

·        Bab Nisa'

·        Bab Jibril

·        Bab Al-baqi'

·        Bab Al-ana'iz

·        Bab Al-a'imma

One of the gates with three doors

Fadada masallacin Madina

An yi ta fadadawa da sabuntawa da kuma zamanantar da ginin wannan masallaci mai daraja a lokuta daban-daban.

An yi aikin fadada masallacin ne bayan yakin Khaibar, a shekara ta bakwai bayan hijira, sa'adda Manzon Allah SAW ya sa aka fadada masallacin saboda ya yi wa jama'a kadan.

Sayyidina Usman Bn Affan ne ya sayi filin da aka fadada masallacin a lokacin.

A zamanin khalifofin Manzon Allah an kara fadada masallacin saboda karuwar yawan al'ummar Musulmi a Madina.

Haka zalika an ci gaba a zamanin Daular Usmaniyya da Bani Umayya da Abbasiyya da Ottoman har zuwa wannan karni.

A zamanin khalifancin Umar bn Al-khattab ne a shekara ta 17 bayan hijira (638 miladiyya) aka fara fadada masallacin da sauya fasalinsa bayan Manzon Allah ya yi wafati.

A lokacin an fadada masallacin ta bangaren alkibla (Kudu) inda aka kara masa kofa shida, bayan an saye an kuma rusa gidajen da ke makwabtaka da masallacin ta barin kudu, aka fadada masallacin.

Khalifa Usman Bn Affan ma ya kara fadada masallacin a shekara ta 29-30 bayan hijira (650 miladiyya).

Usman ya sa an yi wa bangon masallacin yabe kuma aka wa masallacin ado da duwatsu masu zayyana.

Sannan kuma aka sanya wa masallacin turaku na duwatsu masu ado da karafa da aka shafe da ruwan dalma.

Baya ga haka an yi wa rufin masallacin dabe.

A shekara ta 88-91 bayan hijira (707) Khalifa Al-walid bn Abdulmalik ya umurci sarkin garin Madina, Umar Abdulaziz ya saye gidaje masu makwabtaka da masallacin a sake fadada shi.

A wannan aikin ne aka fara yi wa masallacin hasumiya.

An yi wa masallacin hasumiya hudu (daya a kowace kusurwa), sannan aka yi baranda a saman rufinsa.

A shekarar 161-165 bayan hijira, Sultan Mahdi na Daular Abbasiyya ya kara fadada masallacin.

Sai kuma Sultan Ashraf Qaitbay ya kara fadadawa a 888 bayan hijira da 1202.
A 1256 (654 bayan hijira) an yi wata gobara a masallacin.

Hakan ya sa khalifofi da shugabannin Musulmi bayar da gudumowa domin sake gyara shi.

Khalifa na karshe a Daular Abbasiyya, Al-Mu'tasim Billah, shi ne wanda ya fara aiko da gudumowar kayan aiki da magina da suka gyara masallacin daga Iraki a shekara ta 655 bayan hijira (1257 miladiyya).

An sake yin wata gobara da ta lalata mafi yawancin rufin masallacin a shekarar 886 hijiriyya (1482 miladiyya).

Sakamakon haka, sai Gwamna Qaytbay na Masar ya aika da ma'aikata da kayan aikin da masu zanen taswirar gini su fadada tare da sabunta masallacin, wanda aka yi a 890 hijiriyya (1486).

Daga nan sai da aka kwashe shekara 387 ba a kara fadada masallacin ba, sai dai 'yan gyare-gyare da kwaskwarima a kan hasumiyoyi da kubbobi da bangon masallacin.

A wannan aikin ne aka sabunta watan da ke kan hasumiyoyi da kubbobin masallacin.

A zamanin Daular Ottoman an dauki shekaru 13 ana sabuntawa tare da kara fadada Masallacin Manzon Allah SAW.

Sarki Abdulmajid na biyu ya aiko da magina da ma'aikata da kayan aiki a shekarar 1265 bayan hijira (1849 miladiyya).

Aikin fadada Masallacin Madina da ya fi daukar hankali a wannan zamani shi ne na 1994, zamanin Sarki Abdallah bn Abdulaziz na Saudiyya.

Sarki Abdallah ya sa an sanya kayatattun rumfuna na alfarma guda 250 a kan gimshikan da ke harabar masallacin.

An kera rumfunan ne musamman domin masallacin na Manzon Allah.

Fadin inuwar da rumfunan ke samarwa a harabar masallacin ya kai murabba'in mita 143,000.

A karkashin kowace rumfa mutum 800 na iya yin sallah.

A shekarar 2012 (1433 bayan hijira), Sarki Abdallah ya kaddamar da harsashin fadada ginin masallacin ta yadda zai iya daukar mutum 1,600,000 zuwa mutum 2,000,000.

Da Sarki Salman Bn Abdul'aziz ya hau mulkin Saudiyya bayan rasuwar Sarki Abdullah, sai ya jaddada ci gaba da aikin fadada Masallacin Manzon Allah (SAW).

Aikin fadada masallachin zango na biyu da na uku zai bawa sama da masallata miliyan daya damar gudanar da ibada, ya yin da aikin farko zai dauki masu ibada 800,000.

Karin na nufin samun dama ga masu ibada miliyan 1.2 daga yanzu zuwa shekarar 2040.

Taswirar Masallacin Annabi SAW da gine-ginen da ke makwabtaka da shi

Taswirar Masallacin Annabi SAW da gine-ginen da ke makwabtaka da shi

Mimbarin Manzon Allah SAW

Mimbarin Manzon Allah (SAW) na daga cikin wurare masu muhimmanci da daraja a masallacin mai alfarma.

Daga cikin muhimman wurare a masallacin akwai mimbarin Manzon Allah, inda a nan yake yin huduba.

Mimbarin farko a masallacin an yi shi ne da kututturen dabino kuma yana da matakala uku.

A mimbarin su ma manyan Khalifofin mazon Allah suka yi huduba. Abubakar da Umar sun rika yin huduba a mataki na biyu.

Usman ya rika tsayawa mataki na farko, kafin daga baya ya koma yana yin huduba a kan mataki na uku kamar yadda manzon Allah ya ke yi.

A shekarar 886 bayan hijira, an yi wata gobara a masallacin na manzon Allah wadda ta yi sanadiyyar konewar mimbarin Manzon Allah.

Sakamakon haka sai mutanen Madina suka maye gurbin mimbarin da wani da suka gina da jar kasa.

Daga bisani sai wani daga cikin sarakunan Musulunci ya aiko da wani sabon mimbari fari na alfarma da zai maye gurbin mimbarin na jar kasa.


Wannan mihrabin shi ne ke hada Rauda da Mukabbariyya (wurin da ake kiran sallah) a wannan zamani.

Za a iya fahimtar cewa yanzu an sauya wa wannan Mihrab din fasali sakamakon gyare-gyare da fadadawar da aka yi wa masallacin tsawon zamani.
Na biyu shi ne Mihrab inda limamai ke jan sallah a yanzu, wanda ke bangon da ke barin alkibla na masallacin.

Mihrab din da limamai ke jan sallah a ciki na da tsawon tarihi tun zamanin khalifancin Usman.

Khalifa Usman Bn Affan shi ne na biyu kuma karshen wanda ya fadada masallacin ta bangaren kudu, wanda shi ne alkiblar masallacin.

Mimbari na uku kamar yadda Dr Akhter ya yi bayani ana kiran shi Suleymaniye ko kuma Ahnaf Mihrab wanda aka yi bisa umurnin Sarki Suleyman. Anan ne Imam Hanafi ke jan Sallah, yain da Imamu Maliki ke jan sallah a mimbarin Annabi (SAW).


Rauda

Rauda wani wuri ne da ke dab da gidan Annabi (SAW).

Annabi Muhammad (SAW) ya ce ''a tsakanin gidana da munbarina dausayi ne daga dausayin aljanna kamar yadda Bukhari ya ruwaito daga Abu-Hurairah''.

A ko da yaushe Rauda a bude take domin masu ziyara. Ana raba lokutan ziyarar ga masu ziyara maza da mata wanda hakan yana rage cinkoso.

Masu ziyarar kan yi nafila kafin su ziyarci kabarin Annabi (SAW).

Fadada masallacin da kuma kawata shi da ake yi a ko da yaushe yasa itama Rauda ta samu kula ta musamman.

Ma'aikatar da ke kula da masallacin ta bayyana cewa Rauda na da fadin murabbu'in mita 330.

A ko da yaushe wannan wuri na da jami'an tsaro da masu kula da shi da ke lura da yadda zirga-zirgar jama'a take gudana.


Koriyar Kubba

Wannan Koriyar Kubba na daga cikin wuraren da ake iya gani karara a duk lokacin da aka ziyarci wannan masallaci. An gina ta ne a kusa da ginin da ke dauke da kaburburan Annabin Muhammad (SAW) da Abubakar da Umar.

Al Samhudi in 'Wafa Al-Wafa' ya ce an gina tulluwar farko ta Rauda a kan kabarin Annabi sama da shekaru 650 da itace. Sultan Qalawun ne ya gina ta a 1279 (678 bayan hijira).

Koriyar Kubbar da muke gani a yanzu ta saman rufin dakin Annabi ne. Akwai kuma karama a ciki wadda ke dauke da sunan Annabi (SAW) da kuma Abu Bakr da Umar (AS) a cewar Dr. Akhter.

Dr Akhter ya kara da cewa kafin yi wa tulluwar fenti a shekarar 1837, kafin lokacin ta dade dauke da farin fenti daga baya kuma aka maida ita ruwan shinshinbale da kuma shudi.Dakin karatun Masallacin Madina

Akwai dakunan karatu biyu a Masallacin Manzon Allah SAW. Dakin karatu na farko an gina shi ne tun a shekarar 886 bayan hijira.

A wannan dakin karatu ake samun takardu masu dauke da ainihin rubuce-rubucen magabata.

Litattafan da ke dakunan karatun sun kunshi dukkan fannonin ilimin musulunci.

Daga baya an rasa wasu daga cikin litattafan sakamakon gobara da aka yi ta samu a lokuta daban-daban.

A halin yanzu wannan dakin karatu na a bangaren yamma a saman masallacin.

Bangaren adana takardun da aka rubuta su da hannu

Bangaren adana takardun da aka rubuta su da hannu

Littafan da ba kasafai ake samu ba suna wani bangaren na musamman tare da rubuta lokacin da aka buga su.

Bangaren littatafan da suke da wahalar samu

Bangaren littatafan da suke da wahalar samu

Akwai kuma bangaren littafai bugun hannu da kuma dakin karatu na intanet. Haka ma akwai wanda ke kula da sauran ababe kamar bincike da fassara da kuma kiyaye masallacin daga gobara da makamantan su.

Dakin karatun na da wasu dakunan karatu na maza da mata da kuma kananan yara.

The Prophet's pulpit
The Mihrab where call to prayers are made
The Green Dome
A library manuscript

The old library

The new library

The old library

The new library

Masallachin Annabi (SAW) na daga cikin masallatai mafiya kyau da kawa irin ta zamani a duniya.

An zuba mukadan biliyoyin riyals na Saudiyya wurin sake gina wa da fadada shi da kuma kawata shi.

Ganin yadda miliyoyin musulmai ke tururuwa don kai ziyara musamman a lokutan Hajji da Umra, masu kula da masallacin na nan ko yaushe wanda hakan ya nuna jajircewa wurin ganin masu ibada sun samu abunda su ke so.

Ziyarar masallacin baya cikin aikin hajji ko kuma umra, to amma mahajjata ba za su taba samun gamsuwa ba tare da sun kai ziyara kabarin Annabi (SAW) tare da ibada a wannan masallaci mai matukar muhimmanci da kuma ban sha'awa.

KARSHE

Visitors trooping to see various monuments

Visitors trooping to see various monuments

Wadanda suka yi aiki

Bincike da Rubutawa: Sagir Saleh

Shiryawa da Tacewa: Halima Umar Saleh

Tsarawa: Nkechi Ogbonna

Dukkan hotuna da bidiyo hakkin mallakar Getty da BBC da kuma hukumar kula da Masallacin Madina ne.