Gagarumin aikin raba 'yan biyun da suka hade ta kwakwalwa

Daga Rachael Buchanan

An yi dandazo a dakin tiyatar likitanci. Amma tawaga daya ta mutum 20 ce za su yi aikin a tare.


Cikin natsuwa, komai ana bi daki-daki. Ba wata alamar tashin hankali ko damuwa, kawai ayyuka ne ake aiwatar da su bisa tsari.

Amma dai ba irin tiyatar da aka saba yi ba ce. Hasken dakin tiyatar ya haska lullubabbun yaran da ke cure. Safa da Marwa manne suke da juna ta kansu. An bude kwakwalwarsu lokacin da likitocin aikin fida suka dukufa wajen warware daure-dauren hadakar jijiyoyin da jini ke kewayawa..

Duk da haka lumanar dakin tiyatar ta gushe, daidai lokacin da jami’an lafiyar da ke da aikin kashe zafin ciwon wanda aka yi wa aiki suka yi nunin ankarar da matsala.

Jinin da ke fita daga kwakwalar Safa ba ya tsanewa da kyau, sannan yana bijire wa jinin da ke zuwa daga ’yar uwarta.

Wannan ya haifar da tarnaki ga zuciyar Marwa, sannan ta kasance tattare da hadarin kasancewa cikin mawuyacin hali.

Jami’an lafiya da ke tarairayar ciwon wanda aka yi wa tiyata, sun bayar da umarni kan rahoton bijirowar muhimman al’amura, sannan suka himmatu shawo kan mawuyacin halin da yaran ke ciki.

“Ina ganin akwai bukatar mu yi girgiza,” a cewar daya daga cikinsu.

Sai aka manna kunzugu a kirjin Marwa daidai lokacin da aka fara shirin aikin.

Jagoran tiyatar ya daga hannayensa ta yadda za a iya ganinsu, sannan ya koma da baya.

Daga sai kowa ya jira.

Idan har suka rasata, to ita ma Safa haka za a yi asarar rayuwarta. , sanna�b�63

Rayuwa a Pakistan

Zainab Bibi tana da ’ya’ya bakwai – kuma dukkansu a gida ta haife su. Don haka tun lokacin da ta dauki cikin tagwaye, niyyarta ta sake haihuwa a gida kamar yadda ta sha yi a baya.

Sai dai bayan da na’urar daukar hotun ciki ta yi nuni da akwai matsala, sai aka shawarceta kan lallai ta haihu a asibiti.

A lokacin iyalan na cikin mawuyacin hali. Watanni biyu da suka wuce mijin Zainab ya mutu sanadiyyar bugun ciwon zuciya.

Sannan jami’an kula da lafiyar masu juna biyu sun sanar da ita cewa akwai yiwuwar tagwayen da take dauke da su a manne suke da juna. Amma dai ba a ambaci sassan jiki da ke da likon alakar mannewar ba.

Kusan babu wanda ya fahimci hakikanin kimar dimbin matsalolin da ka iya bijirowa.

Zainab Bibi

A ranar 7 ga Janairun 2017, ta haifi ’yan biyunta bayan da aka yi mata tiyata a asibitin Hayatabad da ke Peshawar, kimanin mil 31 (kilomita 50) daga gidanta da ke Arewacin Pakistan.

An sanar da iyayen cewa jariran na cikin koshin lafiya.

Duk da haka dai Zainab ba ta ga jariran nata ba nan take, saboda akwai bukatar ta murmure daga aikin da aka yi mata.

Kakan wadannan tagwaye, Mohammad Sadat Hussain shi ne ya gano hakikanin gaskiyar lamarin – jariran sun kasance tagwayen da aka haifa a manne da juna da kimiyyance ake yi wa lakabi da “craniopagus twins,” al’amarin da ke nuni da cewa sun manne da juna ne ta likon alakar kansu. Al’amarin da ba a cika samun irinsa ba.

Kakan nasu ya je wajen kula da lafiyar masu haihuwa dauke da kyautar al’ada ta nau’ukan alawa don bai wa malaman jinya (nas-nas).

Yana dai cikin alhinin makokin rashin dansa, yayin da ya ga sabbin jikokin nasa a wani mummunan yanayin ban takaici. “Ina cike da farin cikin ganinsu, amma ina ta kai-kawo a tunani kan yadda zan yi da su, saboda kasancewar kawunansu a manne da juna?”

An shafe kwanaki biyar kafin Zainab ta murmure a nuna mata ’ya’yanta, inda daga bisani aka nuna mata hotunan tagwayen da za ta yi shirin kula da su

Ta ce nan take ta ji tana cike da kaunarsu.

“Suna da matukar kyau, sannan gashinsu na da ban sha’awa, kuma launin fatarsu fara. Ba na ma jin cewa a manne suke. Sun kasance wata baiwa daga Allah ce (kyauta ce daga Allah).

An rada musu suna Safa da Marwa, sunan da ya samo asali daga tsaunukan Makka da ke kasar Saudiyya, wadanda ke da matukar muhimmanci wajen gudanar da ibadar aikin hajji.

Safa and Marwa

Bayan wata guda, sai aka sallami ’yan tagwayen daga asibiti, kuma iyayen suka amince da cewa idan har zai yiwu, za a iya raba su.

Wani asibitin sojoji ya dauki nauyin yi musu tiyata, amma tare da gargadin cewa akwai yiwuwar daya daga cikin ’yan biyu ta mutu. Wannan hadari ne na asarar rayuwar da mahaifiyarsu ba ta shirya masa ba.

A lokacin da tagwayen suka kai watanni uku sai aka duba yiwuwarsu wasu zabukan daban-daban, inda wadannan iyalai suka tuntubi kwararren likitan tiyatar likon alakar sakonnin kwakwalwar yara (neurosurgeon), Owase Jeelani, da ke aiki a daya daga manyan asibitocin duniya da ke kula da lafiyar kananan yara, wanda yake a titin Great Ormond a Landan wato GOSH.

Wani dace da aka yi, shi ma haifaffen yankin Kashmir ne, kuma nan take ya kulla kyakkyawar dangantaka da su.

Bayan da ya yi nazarin hotunan ’yan matan da na’urar hotunan sassan jiki ta dauko, likitan tiyatar ya gamsu da cewar za a iya raba su ba tare da wata matsala ba, amma akwai bukatar a yi aikin tun kafin su kai watanni 12, ta yadda za a samu kyakkyawan sakamako.

Lokacin na ta tafiya.

A cikin Agustan 2018 aka samu bizar izinin shiga kasar Birtaniya, amma ba a samu tallafin kudin daukar nauyin tiyatar ba. Domin wannan ba aiki ne da tsarin kula da lafiya na Birtaniya NHS ke daukar nauyinsa ba, sannan Jelani ya tara kudi kadan daga cikin abin da ake bukata na kudin kula da lafiya a asibiti.

Yanzu ga shi jariran har sun kai watanni 19. Karin nisan watannin da ya wuce ka’idar da kwararrun likitocin asibitin GOSH suka so yin tiyatar. Kuma da zarar an ci gaba da samun jinkiri, to aikin rabawar zai kasance tattare da hadari, sannan murmurewar warakarsu takaiciyya ce.

Jeelani ya bukaci wannan iyayen da su hanzarta zuwa Ingila nan take.

Ya tuna lokacin da suka isa: Sun isa cikin farkon Agusta kuma a lokacin kudin da muke da su kadan ne, in an kwatanta da yawan abin da ake bukata. Yaran suna nan kuma dole dai na kasance cikin damuwa. A daidai matakin da ake sai na ji tamkar nauyi ne da ya rataya a kaina.”

An sauke kawun tagwayen Mohammad Idrees da kakansu a wani gida da ke kusa da asibitin. Amma ita Zainab ba za a iya rabata da ’ya’yanta ba, kuma ta fi son ta rika kwana a dakin da suke.

Duk da cewa a manne suke, wadannan tagwaye na da wata irin kimar mutumtaka ta daban, a cewar mahaifiyarsu.

Safa, mai wayo ce, cike da annashuwar farin ciki da yawan surutu”. Marwa, kuwa mai kunya ce. “A wasu lokutan takan yi magana da kanta, amma idan muka yi mata magana ba ko da yaushe take mayar da amsa ba,” in ji Zainab.

Mako guda daga bisani, Jeelani da wata Lauya abokiyar huldarsa suna cin abincin rana, kwatsam sai aka samu taimakon da ya sauya daukacin al’amura. Bayan da ya bayyana mata labarin tagwayen, sai lauyar ta dauki wayar salularta ta yi kira.

Sai aka bukaci likitan tiyatar ya sanar da mutumin da ke kan layin wayar labarin jariran. Lokacin yana magana ne da wani hamshakin attajiri dan Pakistan Murtaza Lakhani. Cikin mintuna kadan, ya bayar da isassun kudin da za su dauki nauyin aiki.

Mannewa ta kai

Tagwayen masu manne da juna da aka same su daga kwayayen haihuwa guda sukan kasance masu kama daya kwabo-da-kwabo.

Akwai mahangar fahimta biyu game da dalilin mannewarsu da juna – ko dai dan tayin da ke rabuwa ya faru ne daga bisani sabanin yadda aka saba, kuma ’yan tagwayen sun dan fara rabuwa ne kawai, ko daidai lokacin rbuwar wani yanki na dan tayin ya manne kuma wadannan sassan jikin suka hade har suka girma.

Yayin da al’amarin ya auku, tagwaye sun fi mannewa da juna a kirji da ciki ko ta kafar al’aura da ke tsakanin kafafu.

Mannewar Safa da Marwa ta bijiro da babban kalubale na daban ga kwararrun likitocin asibitin GOSH. Jariran sun manne ne a saman kansu – gam-gam – suna fuskantar alkibla daban-daban.

Ba su taba kallon fuskokin juna ba.

Safa and Marwa

Kokon kansu kamar bututun murhun rusho yake, wani zirin bututu mai tsawo.. Hotunan sassan jiki sun nuna ’yan matan na da kwakwalwa daban-daban, sai dai a tankware suke. Barin daman kowace kwakwalwa ya kai digiri 90, inda ya mika ya kutsa cikin kwakwalwar daya.

Wannan tankwarewar na bukatar gyara matukar ana son jariran su samu kwakwalwa mai fasalin kawunan mutane.

Babban abin damuwar rukunin kwararrun likitocin shi ne yadda za su raba wannan cukurkudadden al’amari mai wuyar sha’ani, inda jijiyoyi da kafofin gudanar jini a hade suke. Kowane daya daga cikin ’yan tagwayen na zuba wa dan uwansa jini. Raba likon alakar na tattare da hadarin dakatar da abin da ke kwarara a kwakwalwa har ta kai ga shanyewar gabban jiki.   


Babu jadawalin kididdigar alkaluma a hukumance kan yawan yaduwar tagwaye masu manne da juna, amma an kiyasta al’amarin kan cewa ana samun aukuwarsa sau daya a cikin haihuwa miliyan 2.5. Mafi yawansu ba su cika rayuwa tsawon wa’adin da ya wuce sa’ao’i 24 ba.

Kowane yanayin na aukuwa ne a wani salo na daban, sannan an taba ruwaito labarin raba manannun ’yan tagwaye ne sau 60 tun yunkurin farko da aka taba yi cikin shekarar 1952.

Jeelani  na da tabbacin jin cewa akwai kimanin manannun ’yan tagwaye shida da aka haifa a fadin duniya a kowace shekara, wadanda ta yiwu an samu nasarar raba su.

Asibitin titin Great Ormond shi ne ja-gaba a fadin duniya wajen aiwatar da irin wannan tiyatar (ta raba manannun ’yan tagwaye). Safa da Marwa sun kasance a jerin manannun ’yan tagwaye na uku, tun da sun fi shahara fiye da kowace cibiya. Rukunin kwararrun suna da masaniya daga irin gogewarsu cewa ana samun kyakkyawan sakamako yayin da aka yi aikin tiyatar wajen gudanar da dimbin ayyuka, don bayar da damar murmurewa a tsakani.

Likitocin tiyatar tare da malaman jinya, sun kai mutum 100 na kwararrun ma’aikatan asibitin GOSH da ke kula da tarairayar lafiya da raba manannun ’yan tagwaye, wadanda suka hada da injiniyoyin kula da lafiya da masu zayyanar faskain 3D da masu zayyanar shafukan intanet.

Mr Owase Jeelani da Farfesa David Dunaway

Mr Owase Jeelani da Farfesa David Dunaway

Jeelani  ne ya kasance jagoran aikin raba kwakwalwa da kafofin makwarar jinin jariran, amma dai kwararren likitan gyara fasalin mutum Farfesa David Dunaway ne ke da alhakin gyara kawunan jariran, inda zai samar wa kowace daga cikinsu rufin kai.


Tiyatar farko

Da karfe  08:00 na ranar Litinin 15 ga Oktobar 2018 rukunin ma’aikata 20 suka taru a dakin tiyata ta 10 a asibitin GOSH. Kowane daya daga cikin ma’aikatan ya gabatar da kansa tare da bayyana irin ayyukan da za su gudanar.

“Muna da aiki guda a jerin ayyukanmu na yau. Safa da Marwa: Kananan yara biyu, aiki guda da ke gabanmu,” in ji Jeelani.

An fara aikin sama wa tagwayen 'yancinsu.

Manufar wannan aikin tiyatar – na farko a jerin manyan ayyukan tiyata – shi ne raba manannun ’yan biyu’ wadanda jijiyoyinsu ke hade.

Owase Jeelani addresses the team

Jeelani ya yi aikin bibiyar tsarin aikin a karo na karshe, amma kowa na sane da abin da ya dace su yi. Rukunin kwararrun sun shafe watanni suna shirya wa wannan ranar.

“Mun yi nazarin komai da kyau – mun yi gwajin yadda za mu gudanar da aikin, inda muka yi ta maimaitawa. Wannan shi ne lokaci na gaskiya da ake son komai ya yiwu da kyau,” in ji Dunaway. 

Bayan haka a sashen kwantar da majinyata na Bumblebee, an shirya ’yan tagwayen don shiga tiyata. Safa da Marwa sanye da zulumbuwar rigar tiyata suna ta kwallara kuka, tare da juyi ba kakkautawa.

Zainab comforts the twins

Raba manannun ’yan tagwaye al’amari ne da ke tattare da hadari. Daya ko duka suna iya mutuwa yayin da ake tiyatar ko kuma a yi musu rauni a kwakwalwa. Iyayen sun fahimci hadarin da ke tattare da aikin, kuma sun yi matukar amanna da yarda da rukunin kwararrun ma’aikatan.

“A bayyane yake cewa ana cikin matsanancin halin rayuwa idan ka/ki ka kasance a manne da juna irin haka, shi ya sa ma akwai bukatar a shawo kan mutum ya amince a yi yunkurin rabawar, kuma wadannan iyaye sun nuna amincewarsu karara,” in ji Jeelani.

Dunaway ya ce rukunin kwararrun sun yi nazari a tsanake kan dabaru da ka’idojin aikin da suka yi.

“Ina da masaniya cewa karara lamarin yake a bayyane rayuwa a ware ta fi kyau fiye da a ce sun kasance manne da juna. Idan har ina jin cewa ba mu da tabbacin gudanar da aikin cikin nasara, to da sai mun yi tunani sosai kan ko za mu yi ma aikin gaba daya. Daukacin rukunin kwararrun suna da yakinin cewa akwai alamun smaun nasarar rabawar a nan.”

Zainab Bibi

Yayin da gadon da tagwayen ke ciki ya iso kofar shiga dakin tiyatar sai Zainab ta sumbaci ’ya’yan nata. Tana sane da cewa watanni masu zuwa za su kasance tattare da wahala a garesu kuma cike da sosuwar zukata na rabuwa da wurin da suka darsu da irin kyautatawar da aka yi musu. Cikin zubar hawaye, sai daya daga cikin malaman jinyar ta rika kwantar mata da hankali domin har sun zama tamkar ’yan uwa.

“Ina da tabbacin cewa komai zai yi kyau, sannan na yi amanna tare da natsuwa da likitocin. Ko da yaushe ina ta rokon Allah ya sa a yi komai lafiya cike da nasara,” in ji ta.

Surgery

A dakin tiyata, matakin farko shi ne cire manyan-manyan sassan kai uku. Jeelani sanye da tabaron aikin tiyatar likitanci (surgical loupes ). Ya rika bibiyar alamun da ya shata zanensu a kan jariran ’yan matan, wanda yanzu yake a aske, sai ya tsaga fatar da kashin.

Da zarar kwakwalwar ta bulluko sai ya sauya tabaronsa na aikin fida da wani abu mai karfin gaske.

An girke madubin da likitoci ke amfani da shi mai tsawon kafa bakwai (7ft), a dakin tiyatar. Yana bai wa likitan fidar damar ganin jijiyoyin sadarwar jikin yaran da yadda jini ke bi.

Owase Jeelani looks through the microscope

Yanzu da karfe 2:30 (14:30 lokacin GMT) sai Jeelani ya bayyana cewa: An daure zirin jijiyar jinin jikin Safa da za ta zubo wa kwakwalwar Marwa jini tamau. Yanzu muna jira.”

An shiga yanayin tashin hankali. Kowane lokaci ana datse likon alaka, al’amarin da ke tattare da hadarin raunata kwakwalwa. Bayan mintuna biyar sai likitan fidar tiyatar ya ce kwakwalwa “ba ta nuna akwai wata matsala tattare da ita ba,” don haka sai a ci gaba.

An ci gaba da wannan aiki mai matukar wahala har tsawon sa’o’i domin magudanan jinin da ke manne suna kai-kawo daga jikin dayar tagwaye zuwa wajen dayar an daure, an toshe gam.

Bayan haka sai rukunin kwararrun likitoci na biyu, karkashin jagorancin Dunday suka fara tsara nasu ayyukan daga dan taki kadan daga wajen da ake gudanar da ainihin aikin.

Aikinsu shi ne su kirkiri marufin tsandaurin da zai rufe sassan kan da aka rede, wadanda za a datsa su a bangaren aikin tiyata ta biyu.

David Dunaway screws together pieces of skull

An daure tankwararrun balli-ballin kashin a tare waje guda da mahadar kawanyar karfe da aka yi wa madauri.

Dunaway  ya ce wannan shi ne babban kalubale in an yi la’akari da shekarun ’yan tagwayen. “Da yake sun fara girma jikinsu ya yi kwari, saboda haka duk abinda muka yi sai ya kasance mai karfi sosai da zai bijirewa juyawa da lankwasawa da za su rika yi wa kawunansu.

Cikin natsuwa rukunin kwararrun suka rika raba kwakwalwar Safa da Marwa, sai suka cusa fallen robar magani da za ta hana sake hadewarsu a tsakanin ayyukan tiyatar da ake yi. An daura masargafin jawowa da zai hana dona fallen robar kawo tarnaki ga bangaren kwakwalwar kowacce daga mannewa a kan ta 'yar uwarta. Wannan shirin a hankali zai saukaka wa kwakwalwar komawa cikin mazauninta.

Da zarar an raba manannun magudanan jinin, sai a sake hade marfin kan. Aikin tiyatar ya kwashe sa’o’i 15 ana gudanar da shi.

An kai ’yan biyun wajen kula da lafiya na musamman don ba su cikakkiyar kulawa. Bayan kwanaki biyu, sai aka dawo da su wajen kwantar da marasa lafiya a dakinsu na Bumblebee – al’amura dai suna yin kyau.

Yadda kan 'yan biyun ya hade


Fasahar kere-keren zamani

Jeelani da Dunaway duk sun yi aiki ka’in da na’in wajen raba manannun ’yan tagwaye a asibitin GOSH a shekarun 2006 da 2011.

Na karshen da suka yi shi ne na raba Rital da Ritaj Gaboura, tgwayen ’yan mata da suka fito daga kasar Sudan, wadanda a lokacin suna da watanni 11.

Rital da Ritaj Gaboura

Rital da Ritaj Gaboura

Rital da Ritaj Gaboura

Dunaway  ya ce raba Safa da Marwa in an kwatanta shi ne aiki mafi wahala, in ma ba a ce ya kai makura ba saboda kwakwalwarsu da ke cukurkude.

"Aikin raba 'yan biyu na farko-farkon sun fi sauki kuma mun yi nasara. Daga baya mun gane cewa lallai mun raina aikin wadannan 'yan biyun sai bayan da muka fara aikin sannan muka gane kwakwalensu kusan a cukurkude suke. Sannan sun fara girma, kuma girman nasu ya jawo wahalar aikin.

Likitocin fidar tiyatar na da tabbacin cewa lokacin da ya fi dacewa da raba manannun tagwayen shi ne a lokacin da suke tsakanin watanni shida zuwa 12.

 “Mun yi aiki tukuru mai dimbin yawa a kan wadannan tagwayen,” a cewar Jeelani. “Kananan nau’ukan kwakwalwa da magudanan jini in an datse su sun fi saurin toho.”

Dunaway ya yarda cewa: “Komai ya kasance cikin sauki. An daye fatar har ta warke da kyau, kuma kashin ya toho da mafi kyawun yanayi.”

Safa da Marwa sun kusa kai wa shekaru biyu, duk da cewa shekarunsu sun kawo tarnaki, rukunin kwararrun sun samu madogarar kyautatuwar yi musu aiki. Ci gaban da aka samu na fasahar kimiyyar kere-keren bibiyar hotunan sassan jiki da sarrafa a shekaru takwas da suka gabata, ya taimaka musu wajen raba (mannanun tagwaye) da gaske fiye yadda lamarin yake a da.

A wani tsukukun ofis, inda allon na’urar kwamfuta ta babbake ko ina, nan ne kwararren likitan tiyatar gyaran sassan jiki Juling Ong yake. Shi ne ke jagorantar rukunin masu aikin gyara fasalin Safa da Marwa da aka raba, sannan ya yi gwaji da nunin fasahar zamani da suke da ita.

“Wadannan ayyuka ne na daban kuma a wasu lokuta mu kan samu horo a makarantar koyon aikin likitanci,” in ji shi. “Amfani da irin wannan massarafar kwamfuta, za mu iya fitar da fasali a kwamfuta da za mu yi bibiya ta daban ga sassan jikin wadannan kananan yara, sannan mu tsara yadda za a yi musu tiyata kaitsaye.”

A allon kwamfuta an fasalta yadda fatar ’yan matan za ta kasance a tsarin zayyanar 3D mai ban mamaki, kawuna da kwakwalwa wata a cikin wata wadda aka fitar daga fasahar daukar hotunan sassan jiki na al’ada da aka saba yi.

“Wannan fasalin na bayar da damar fito da dabaru daban-daban na aikin tiyata, kuma ta yiwu sassan da ake ganin suna tattare da hadari bisa la’akari da sassan jikinsu na daban.”

Amma wadannan kwamfutocin fitar da fasalin zayyana ba kawai a allon kallo suke ba, har ma sukan fito fili a yi aiki da su, tare da taimakon na’urar dab’i ta 3D.

Sa’o’i 48 daga bisani, ma’aikacin sarrafa fasahar zayyanar 3D na asibitin Kok Yean Chooi ya fito da wata roba mai taushi marar fasali. Yayin da ya kankare sannan ya wanke karin burbushin kayan aikin, sai siffar kawunan ’yan tagwaye ta bayyana na halokon kai da lullubin fata. Wannan siffa za ta taimaka wajen tsara yadda fasalin lullubin fatar kai za ta kasance a tsakanin jariran ’yan matan da kansu yake a hade, bayan an raba.

Dimbin zayyanar fasalin 3D an kirkirota, ta yadda za ta bai wa likitocin fidar tiyata damar nazarin sassan jikin mannannun ’yan tagwayen na daban, tun kafin a fara datsa fatar.

David Dunaway hold models of the twin's skulls

“Samun hasken fahimtar zayyanar fasali kafin a yi musu tiyatar ya yi matukar tasiri kan yadda muka tsara gudanar da aikin tiyatar,” a cewar Jeelani. “Abin da muke son cimmawa shi ne, a warware sasarin jirkicewar kwakwalen. Kuma wannan lamari ne mai wuyar sha’ani da za ka iya yi a kanka.” 

Dunaway ya yarda da cewa: Mun shafe tsawon lokaci a zaune kawai muna nazarin wadannan nau’ukan zayyanar fasali, tare da bijiro da dabarun yadda za a shawo kan matsaloli, wato “idan kaza ya faru.. ya za a yi ke nan..”

Amma rukunin kwararrun aikinsu ya fi gaban fasalin zayyana a fili: suna sanye da na’urorin nazarin bibiyar kadin ayyuka a shafukan kwamfuta tare da juya akalarsu, Jeelani na zaune ya tasa akwatin kwamfuta a gaba, yana ta kai-kawo daga wannan sashe zuwa wancan sashe.. Ya yi ta maimaita kalma iri guda: Lamarin ban mamaki.”

Likitan tiyatar ya nutsa cikin wata duniya ta daban, yanayin da ya ba shi damar bibiyar nazarin cukurkudaddun manannun jijiyoyin da magudanan jinin jikin tagwayen.

“Wannan dai ita ce mafita karara da za a rika amfani da ita nan gaba,” kamar yadda ya furta cikin zumudi. “Muna da yawan albarkar komai a nan (asibitin GOSH) kan abin da ya danganci injiniyoyi da kwararrun masana masarrafar kwamfuta – da dimbin dabarun da suka tattaro wadanda mu likitoci duk da irin horon da muke da shi na aikin likita ba mu san su ba.


Tiyata ta biyu

An yi tiyata ta biyu bayan wata guda da yin ta farkon. Yayin da tiyatar farko ta toshe likon alakar magudanan jini, aikin yau kuwa shi ne a raba jijiyoyi da tsane jini daga kwakwalwar ’yan matan. Kowane kullin mahada da aka datse na tattare da hadarin haifar da shanyewar gabobin jiki a daya daga cikin tagwayen.

A wannan karon kuwa al’amura ba sa tafiya cikin sauki.

Jeelani and Dunaway carry out surgery

Da zarar an datse murfin kokon kai, sai tagwayen suka fara zubar da jini. Tun bayan tiyatar farko jijiyoyn wuyan Safa suka rika zubar da jini. Sun takaita kwarara daga kwakwalwarta don haka akai-akai ta daina dura wa Marwa jini. Daya daga tagwayen jininta ya hau sosai, yayin da na dayar ya yi kasa matuka.

Jami’an kula da lafiyar da ke tarairayar zafin ciwo na ta kokarin daidaita halin da suke ciki.

A lokacin ne bugun zuciyar Marwa ya yi kasa sosai, sai suka ji tsoron kar ta mutu a wajen.

Sai kawai aka tsaya cik, aka yi shiru a zagayen teburin tiyatar inda daukacin idanu suka dubi allon kallo, sai dai kawai sautin da ake ji shi ne na karin bugun zuciyar a na’urar da ke bin kadin aikin.

Wannan matsalar ta kau, amma ba za a ce ba ta haifar da wata mummunar illa ba.

Rukunin masu aikin tiyatar sun fahimci cewa a cikin tagwayen Marwa ce kasance mai rauni. Don haka suka yanke cewa su ba ta jijiyar da ta fi kwari. Saboda a ba ta karin damar ta rayu.

Matsayar da aka yanke tana da matukar wuya. Jeelani na sane da cewa hakan zai yi babban tasiri a kan Safa, har zuwa yanzu da jikinta ya yi kwari.

Sai dai rukunin masu aikin tiyatar sun yarda cewa abin da aka yi shi ya fi dacewa. Tiyatar ta shafe sa’o’i 20 ana yinta. Jeelani ya yi matukar gajiya don haka ya mika ragamar aikin a hannun likitan gyaran fasalin surar mutum Juling Ong don ya kammala.

“Na samu sauki. Mun yi tsammanin za mu rasa Marwa a daya matakin aikin,” a cewarsa. “Amma idan suka farka kamar yadda muke fata, komai zai yi kyau.

Likitocin sun fice daga dakin tiyatar ne da karfe 06:30 na  safiyar washe gari.

Safa and Marwa

Da rana ta take, Jeelani ya buga wayar tarho zuwa asibitin daga gida don ya ji halin da yaran suke ciki. Sai aka sanar da shi cewa Safa na cikin mawuyacin hali, inda take shan wahalar yin numfashi, tare da shacin zanen launuka a fatarta.

“Na yi zaton Safa ta mutu,” a cewarsa, yana bayyana irin tashin hankalin da ya shiga a lokacin na sosuwar zuciya da rashin barcin da ya yi fama da shi, ''sai na zube na fadi kasa a daben dakin girki na fara kuka.''

“Matata ta rude don bata taba ganina a irin wannan yanayin ba. Sai ta ba ni wayata ta ce: “Ka kira David.''

“Ka yi matukar himmatuwa da sha’anin wadannan tagwayen kuma ga shi ka yi matukar gajiya a daidai wannan matakin, ba ka da sauran katabus,” kamar yadda ya bayyana. “Don haka yake da wuyar sha’ani, tattare da sosuwar zuciya kan irin fadi tashin da cukurkudadden lamarin ya haifar masa.”

Daukacin likitocin suka runtuma zuwa sashen masu tsananin bukatar kulawa don duba hotunan sassan kwakwalwar Safa.

Abin da suke gudu shi ne ya faru. Ta yi fama da shanyewar jiki a wani sashe na kwakwalwa, inda suka bai wa Marwa jijiyar da ta fi karfi.

Fiye da tsawon kwanaki biyu, Safa ta kasance a wani irin mawuyacin yanayi.

Zainab da dan uwanta da surukinta suka yi ta yi wa tagwayen addu’a a gefen gado.

Kwatsam sai aka ga Safa ta nuna alamun murmurewa. An cire wa tagwayen bututun shakar iska don suna iya shakar iska a kashin kansu. Daganan likitocin suka fara samun natsuwa.

Duk da haka dai, sanadiyyar shanyewar sashen jikin Safa sai ga shi kafadarta da kafar hagun sun yi rauni.

Lamarin ya yi ta kai-kawo a tunanin Jeelani. “Babban abin da zai sani nutsuwa shi ne idan na ga ta fara takawa tana tafiya sannan ta motsa kafadar hagun dinta da kyau, saboda ina sane da cewa ni na haifar mata da wannan raunin, kuma lamarin na da matukar wuya.”

The twins sleep


Toho da sabuwar fata

Samar da fatar da za ta lullube kawunan ’yan matan na zagayayyen curarren kwarkwaro mai fadi na tattare da kalubale. Babu isasshen wurin da zai rufe saman kawunan da zarar an raba su.

A watan Janairun 2019, makonni kawai suka rage kafin a kai ga yin aikin. Likitan gyaran fasalin jiki David Dunaway da Juling Ong na gefen tagwayen, suna kokarin shawo kan daya daga matsalar – wato rashin fatar da za ta rufe kawunan da zarar an raba su.

Makonni biyu kafin sannan, sun fara cusa kananan curin roba a karkashin fatar gaban goshinsu da bayan kokon kan, sai wadannan bangarori suka ciko kamar sun kumbura.

Safa and Marwa lie on a hospital bed

Curin bullukowar ne ke fadada talewar nama, wadanda aikinsu shi ne su bijiro da tohon fata, kamar yadda Dunaway ya bayyana:

“Suna da wata ’yar karamar mahada da ke like da su ta inda za a iya yin duren allurar sinadarin saline. Manufar ita ce a hankali, a hankali za mu ta yin allurar tale fadin bullukowar fata kamar balan-balan, kuma fatar da ke sama za ta yi ta budewa tana kara fadi.”

Suna sa ran cikin makonni shida fatar za ta kara fadi ta yadda za su samu isasshiyar da za ta rufe saman kawunan ’yan matan.

Twins' connected heads
Empty sacks inserted
Sacks filled with saline
Extra skin growth

Dunaway ya tabbatar da cewa tabbas watannin da suka gabata ba masu sauki ba ne.

“Lokacin ya kasance tattare da wahalhalu a wajen Safa da Marwa,” in ji shi. “Sun yi fama da cututtukan da ke yaduwa tare da zazzabi, har zuciyar Marwa ta rika aiki cikin wahalar da ta shafi daukacinsu, al’amarin da ya haifar mata wani kalubale. Amma suna nan suna jele a wurin kuma duk da haka suna da koshin lafiya.”


David Dunaway fills the skin expanders with saline

David Dunaway fills the skin expanders with saline

Abu na gaba da za a yi wa ’yan matan shi ne rabawa. A karo na farko cikin rayuwarsu za su samu damar ganin juna.


Aikin rabawa

An mayar da ranar aikin rabawar zuwa makonni hudu saboda zuciyar Marwa na fama da matsala. Cikin Fabrairun 2019 – wato watanni hudu bayan da aka yi musu aikin tiyatar farko.

Wannan shi ne dumbin abin da aka tattara a tsawon watannin da aka shafe ana ta tsare-tsare da shirye-shirye.

Tuni dai tagwayen sun jure wa aikin tiyatar da aka dauki tsawon sa’o’i 35 in an tara da tsawon lokacin da aka shafe a aikin tiyatar farko.

Tsawon wasu sa’o’i bakwai nan gaba, an raba sauran likon mahadar kashi da kwakwalwa da nama, illa dai kawai wani likon jijiyar saman kwakwalwa da ya hade yaran.

Surgery team operating to separate the twins

Daga nan, an datse duk wani likon kullin mahada. Da yawa daga cikin masu aikin tiyatar sai suka shigo don su daga jikkunan da aka raba su da juna. ’Yan tagwaye ne dai har yanzu, ba sauran kullin mahada (a tsakaninsu).

“Lamarin ya yi kyau” a cewar Dunaway.

Karo na farko cikin shekaru biyu, rayuwar kowace daya daga ’yan uwan ba ta dogara da dayar ba. Wannan ya bayar da saukin aiki ga tawagar masu kula da lafiya da ke aikin kashe zafin ciwo na fafutikar daidaita bugun zuciya, tare da hawan jini da sauran muhimman alamu.

 Amma dai aikin rabawar shi ne jigon share fagen tiyatar yau. Sai rukunin kwararrun sun gyara fasalin curarren kai ga kowace daya daga cikin yaran, daga burbushin sauran yankin kokon kai, inda suke hankoron ganin karin fatar da ta toho girmanta ya isa ya rufe su.

Kowace dayar ’yan tagwayen yanzu tana bukatar aikin tiyatar kashin kansu. Rabin rukunin kwararrun za su tsaya tare da Marwa a karkashin kulawar Jeelani da Ong, yayin da Dunaway zai jagoranci rukuni na biyu da za su yi aikin cura kokon kan Safa.

An yi amfani da fallen fim din roba wajen lulluben saman kanta da ya bude ta yadda za ta samu kariya yayin da aka dauke ta zuwa wani wuri.

A yayin da aka shirya dakunan tiyatar don gudanar da matakin karshe na aikin, manyan likitoci biyu da ke jagorantar aikin sun kasance cikin annashuwa cike da murmushi, suna musabiha da juna a farfajiyar wajen.

“Lamarin na da matukar sosa zukata,” in ji Dunaway. “Muna ta aiki tukuru tsawon lokaci don kawowa ga wannan lokaci - sun tsallake matakan aiki daban-daban kuma ga shi kwalliya ta biya kudin sabulu.

Jeelani ya ce:“Mun dauki tagwayen daban-daban, amma yanzu mun cura musu kawuna, sannan mun mayar da kowaccensu a tare.”

Rukunin “masu tarairayar Safa da masu tarairayar Marwa” suka fara muhimmin aikin da ke bukatar natsuwa na sake fasalta kawuna.

“Wani balli nawa ne, wani ballin naka ne,” a cewar Dunaway, kwararren da ya shafe shekara 23 yana aikin tiyatar gyaran fasalin sassan jiki, yayin da yake tarirayar curin balallun kawuna.

Don mu samu isasshen kokon kan da zai rufe daukacin kawunan, kowane balgace sai a raba shi biyu.

“Yana da matukar alfanu a kyautata zayyanar kokon kai a matakai uku: ciki da na waje biyu masu kauri da karfin kashi, amma a tsakanin zai kasance tamkar sakar zuma ta yadda za iya ballawa (gida biyu). Shi ne rabin fadin amma yana nufin za mu iya lullube kusan daukacin kan da kashi,” in ji Dunaway.

Ganin cewa kwakwalwar ’yan matan a cure take rufe-ruf, an yi wa mulmulallen saman kawunan yankan zarto. Balli guda an killace shi da zargagiyar zaren dinki, inda aka kirkiro da tsilli-tsillin balallen kashi.

An cike gibin da ke tsakani da kwayoyin halittar kashi, kuma watanni masu zuwa a hankali za su cike, yadda kowace daga cikin ‘’yar uwar za ta kasance da kanta daban.

Karshen aikin dai shi ne yadda za a talaye a fadada fatar ta rufe kawunan da aka sake wa fasali. Akwai isasshe da za a iya yi wa mahada. Dunaway ya girgiza kansa cikin mamaki. “Wannan rana ce mai cike da ban mamaki ko ba haka ba ne?” in ji shi.

Da karfe 01:30, bayan sa’o’i 17 a dakin tiyata, an yi wata ganawa mai sosa zukata a tsakanin manyan likitocin da iyayen yaran, wadanda ke ta jira a asibitin su ji labari.

Da yake bayani cikin harshen Urdu, Jeelani ya fada wa Zainab cewa an karkare aikin raba ’ya’yanta.

Saboda farin ciki, sai ta sumbaci hannayensa da na Dunaway.

Zainab kisses Owase Jeelani's hand


Rital da Ritaj

Yayin da Safa da Marwa suka daaki lokaci kafin su warke a asibitin Landan, Jeelani da Dunaway sun yi tafiya zuwa kasar Ireland don su ziyarci Rital da Ritaj Gaboura, wasu mannannun tagwaye da suka raba cikin shekarar 2011, lokacin suna da watanni 11.

Sun yi farin cikin ganin ’yan matan a karo na farko a gidan iyayensu da ke Cavan.

Mahaifinsu Abdel-Majeed Gaboura likitan mata ne a asibitin yankin. Matarsa kuwa kwararriyar likitar masu lalurarr tabin hankali ce a kasar Sudan.

Rital da Ritaj, masu sanye da fararren kaya da rigar sanyi ruwan hoda na cikin farin ciki. Za su cika shekara tara a watan Satumba.

Abdel-Majeed and Enas Gaboura with their daughters Rital and Ritaj

Wani dan shacin alamar yanka da ke kawunansu shi ne kadai shaidar da za ta tabbatar da cewa kawunansu da a manne suke. Ritaj ta yi musabiha da likitocin fidar tiyatar. Ta kasa cewa uffan – al’amarin da iyayenta suka ce sabon al’amari ne a wajensu, wato ba haka take ba.

Rital ta yi ta fakon kallon bakin ta bayan kafafuwan mahaifinta.

’Ya’yan Gaboura  sun samu mafi kyawun nasara wajen aikin fidar tiyatar raba manannun tagwaye. An haife su cikin shekarar 2010 a Sudan, ’yan matan kansu ya kasance a manne, amma sabanin na Safa da Marwa kwakwalwarsu ba ta tankware ko ta zoba ba.

Sun isa asibitin GOSH ne suna da watanni bakwai a duniya cikin wani mummunan yanayi. Zuciyar Rital ta kusa daina bugawa saboda dimbin aikinta da ta yi, wajen zuba wa kwakwalwar ’yar uwarta jini tare da tata. Da tuni tagwayen sun mutu da ba a yi musu tiyatar ba.

Aikin rabasu mai matakai hudu ya shafe tsawon sa’o’i uku, kuma cikin makonni kadan suka murmure, aka dawo da su wajen kula da majinyata.

Rital and Ritaj

Rital na fama da cutar dukum da ke mayar da mutum galhanga, saboda haka tana halartar makaranta ta musamman, yayin da Ritaj ke nuna alamun bunkasar ci gaban rayuwa a matakin shekarunta kuma tana halartar tsarin karatun da aka saba da shi.

’Yan biyun na da dangantaka mai karfi. Ritaj ita ce “ja-gaba” a cewar iyayensu, wadanda suka ce har taimakonta suke nema a duk sanda da Rital ta ki bayar da hadin kai.

Rital and Ritaj

Yayin da yake huta a kan kujera mai taushi ya’yan na tsalle a kansa, Abdel-Majeed cewa ya yi, cikin alfahari: “Ba zan iya nuna farin cikina ba, kan cewa muna zaune tare da lafiyayyun tagwaye, tamkar dai yadda na yi ta fatan gani a wancan lokacin. Wannan shi ne lokaci mafi cike da annashuwa a rayuwata.”

Enas na dauke da juna biyu .

“Da daya ne kawai, ba tagwaye ba,” a cewarta cike da murmushi.

“Lamarin ya sha bamban da yadda na dauki ciki a baya. Ban san cewa ko za a haife a raye ko za su mutu mutu ba. Na kasance cikin damuwa a waccan lokacin.”

A wajen likitocin tiyatar ganawar tasu cike take da sosa zukata. “Ziyarar da muka kai wa ’yan matan a gidansu, suna zuwa makaranta, da ganin farin cikin jin dadin rayuwarsu – wannan wani gwaggwaban sakamako ne na musamman. Lamarin na nuni da kimar alfanun irin wannan tiyatar ta daban,” in ji Dunaway.

Rital da Ritaj hujja ce da ke tabbatar da abin da ake iya cimmawa tattare da manannun tagwaye, matukar an yi musu tiyatar rabawar tun suna kanana, yayin da jikinsu ke da karfin yin toho. Sai dai irin wannan aikin tiyatar yana matukar cin kudi da yawa, wanda a mafi yawan lokuta a kan dade kafin a samu tallafin kudin aiki, tamkar dai abin da ya faru ga Safa da Marwa.

Jeelani ya fara tattaunawa da iyayen yaran ne tun yaran suna da watanni uku, amma sai da aka shafe wasu watanni 16 kafin a samu agaji. Kuma yana da tabbacin cewa rashin hanzarin da aka yi ya yi matukar tasirin haifar da irin sakamakon da aka samu. 

“Da mun samu yin aikin da wuri, ta yiwu sakamakon ya fi haka inganci,” in ji shi.

“Za su yi asarar tsawon lokaci, mun yi hasashen cewa za su samu matsaloli tattare da motsawa da yiwuwar tasgaron aikin kwakwalwa. Amma matsayinmu irin na mahaifiyarsu ce. Ta yi farin cikin cewa ga mu a wannan matakin da muke ciki. Ta ji tsoron ba za su rayu ba, da ba mu ba su wannan damar yin aikin ba.”

Yayin gudanar da irin wannan aikin na daban, likitocin fidar tiyar a ko da yaushe sukan yi kai-kawon cewa ko sun yi abin da ya dace. Amma Dunaway na sane da cewa rayuwa za ta yi matukar wahala ga tagwayen da ba a raba su ba.

“Zai yi matukar wahala kula da lafiyarsu. A bayyane yake karara za su fuskanci wani kalubale, amma daukacin al’amuran ina ganin sakamako ne mai kyau a gare su. Sun samu damar gudanar da rayuwa cike da farin ciki a yanzu.”

Likitocin  aikin  tiyar biyu, sun kafa gidauniyar neman tallafin daukar dawainiyar aikin tiyatar da suka sa wa suna Gemini Untwined, inda  za su tattara binciken da aka gudanar da bayanai game da manannun tagwaye don tara gudunmuwar kudin aikin raba duk wasu ’yan biyun da za a haifa a manne nan gaba.

Abin da muke son cimmawa shi ne ka da a sake samun irin wannan tsaikon rashin yin aiki a kan kari wajen tarairayar kula da lafiyar kananan yara, domin yana da matukar cutarwa. Kuma sashen bincike, za su samar mana da dimbin bayanai,” a cewar Dunaway. “Akwai dimbin al’amura da ba mu sani ba game da manannun tagwaye, har muke ganin cewa muna aiwatar da abin da ya dace, amma a hakikanin gaskiya muna bukatar fahimtar dabarun kimiyya.”


Samun sauki

Ranar sallamar Safa da Marwa ta zo. An shafe kimanin watanni biyar tun bayan da aka raba su, kuma lokaci ne mai tsawo, inda a hankali, a hankali jariran ’yan matan suka rika murmurewa. Kowaccensu na bukatar fatar rufe bayan kokon kawunansu ta keya. Kuma a kullum ana yi musu tarairayar motsa jiki don taimaka musu su kara kuzari – su koyi juyi da zama da dago kawunansu sama.

Mahaifiyarsu ta yi musu ado da tufafi masu daukar ido launin ja da ruwan zinare don murnar wannan rana. Yayin da Zainab ta kwashe kayansu, Marwa ta yi jijjiga da juyi a kan gado daidai lokacin da kakanta ke yi mata wasa.

Safa na kwaikwayon kawunta lokacin da yake buga ganga. Duk da cewa akwai sauran lokaci, amma dai sun samu matukar kyautatuwar ingancin lafiya, har sun fara dawowa da wasanninsu na da da suke yi.

Safa and Marwa

Da lokacin fita daga asibitin ya zo, sai sai uwar da malaman jinya da likitocin da suka duba lafiyarsu suka yi ta rungume juna suna hawaye.

Kwatsan Dunaway ya shigo tsakiyarsu don yi musu bankwana, sai Jeelani ma ya fitodaga dakin tiyata don yi musu rakiya. Kyakkayawar alakarsa da wadannan iyalai a bayyane take karara har ma nuna tunkaho yake yi ganin yaran sun murmure da kyau, har an sallame su daga asibiti.

Safa da Marwa da ahalinsu za su dan zauna a Landan nan da zuwa watanni shida a kalla, yayin da ’yan matan ke kara samun kulawar tarairayar gabobin jiki da bin kadin ingancin lafiyarsu, amma dai kamar yadda aka tsara za su koma gida kasar Pakistan a farkon shekarar 2020.

A yayin da suke barin asibitin da ya zame musu gida har na tsawon watannin 11, Zainab ta fahimta karara cewa raba yaran shi ne abu mafi alfanu.

 “Tabbas, ina cike da farin ciki, a matsayina na  mahaifiyarsu. Cikin yardar Allah a yanzu zan iya rike daya na tsawon sa’a guda, sannan in koma in dauki gudar, kuma ina tare da su a cikin dare. Allah Ya amsa addu’ata.”

Wadanda suka yi aikin

Masu rubuta labari: Rachael Buchanan daFergus Walsh

Tsara taswira: Joanne McDonald da Gerry Fletcher

Bidiyo da hotuna: Tony Fallshaw da Julius Peacock daRob Magee

Karin hotuna: Iyalan Bibi da iyalan Gaboura

Wanda ya shirya: James Percy

Edita: Kathryn Westcott