Masarautar Zazzau

Zazzau Emirate

Zazzau Emirate

Wannan wata makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko tambayoyinku a kan tarihin masarautar Zazzau. BBC ta kwashe lokaci mai tsawo wajen bin diddigin amsoshin tambayoyin naku daga masana tarihin wannan masarauta ta Zazzau.


Ita dai masarautar Zazzau tana daya daga cikin muhimman masarautun kasar Hausa da ma yankin Afirka ta yamma.

Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni cewa, Zazzau wata dadaddiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun daruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci.


Zazzau Emirate

Zazzau Emirate

Yadda kalmar  ‘Zazzau’ ta samo asali

Tushen wannan kalma ta ‘Zazzau’ yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin kasar ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo’, wato kasa mai laka, ba mai rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro.

A wani kaulin kuma ‘Zazzau’ na nufin wani takobi, wanda ja-goran jama’a yakan dauka ya jagoranci jama’a a wajen yaki. Mai daukar wannan takobi ba sarki ake kiransa ba, a wancan lokaci ana kiran sa ne ‘Madau-Zazzau’, wato ‘Mai Dauke da Zazzau’. 

Asalin Kalmar Zariya

Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa Turunku, wadda kanwa ce ga Sarauniya Amina


Bambancin Zazzau da Zariya

Zazzau masarauta ce, wadda ta kunshi dukkan kasashe da garuruwan da ke bin masarautar. Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da kasashe suna kawo wa sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni.

Kafuwar Masarautar Zazzau

Mahaya dawakin Zazzau

Mahaya dawakin Zazzau

A zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu wani addini da ya shigo, sai al’adu  ko rayuwa irin ta maguzanci. Kuma kaura daga wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a kokarin a kokarin neman wajen da zai zauna ya sami ingatacciyar rayuwa. Mafi yawan ayyukan da jama’a kan yi a lokacin su ne, noma da kiwo. 

Wannan lokaci ne kuma masana tarihi ke kira zamanin ‘Zo-zo’, wato zamanin maguzanci, wanda ya kasance tun kafin shigowar addinin musulunci.

Lokacin da al’umma suka rika taruwa, suna samun shugabanci, har sarakunan Habe suka fara mulki, aka samu kafuwar Hausa Bakwai, wato zuri’ar Bayajidda da Sarauniya Daurama.

Kuma Zazzau na daya daga cikin kasashen da aka ba ’ya’yan Bayajida mulki.

Bayanin da aka samo daga bakin Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Gunguma shi ne sarkin Zazzau na farko, kuma ya yi tafiyayya ne daga Daura, ya bi ta Kano da Rano, kuma ya fara yada zango a Kangi.

Wadanda suka biyo bayansa sun kafa biranen  mulkinsu ne a Kawari da Rikocci da Wuciciri da kuma Turunku, kafin su je Zariya.

Nohir ta auri wani bako, ta haifa masa da namiji, kuma aka sa wa dan suna dan Bakwa Turunku. Daga baya sunansa ya koma Bakwa Turunku, wanda ya gaji sarautar kawunsa Kawanissa a shekarar 1536.

Bakwa Turunku ya yi sarauta ne a garin Turunku, kuma har yanzu akwai sauran kufan masarautar ta Turunku a can kasan tsaunukan da suke shimfide  a yankin gabashin Zariya.

Kafuwar birnin Zariya

Kamar yadda aka sami labari daga wajen Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Zariya ‘yar Bakwa Turunku, kuma kanwar Sarauniya Amina ce ta kafa birnin Zariya, don haka ake kiran birnin da sunanta.

Hakan kuwa ya biyo bayan yadda hedikwatar mulki ta Zazzau ta yi ta sauya wuri saboda matsalar rashin ruwa, a zamanin mulkin Bakwa Turunku, wato mahaifin Sarauniya Amina da Zariya. Hedikwatar ta tashi daga Bomo zuwa Wucicciri zuwa Ancau zuwa Kargi, ta koma Turunku. A wancan lokaci an ce sai Bakwa ya ga Turunku ta yi wa mutanensa kadan a matsayin hedikwatar mulki, ga matsalar ruwa ana fama da ita. Saboda haka, sai ya koma Zariya a shekarar 1537.  Daga nan ne kuma masarautar Zazzau ta koma Zariya.

Amma ba a shiga Zariya kai tsaye ba, sai Bakwa Turunku ya gaya wa ‘yarsa Zariya, cewa ta je wajen kufannin iyayensu, wato Kufena kenan, ta je ta fara zama a wurin, kuma akwai rafi a wajen. Sai dai da Sarauniya Amina, wadda ita ce 'ya a wajen Zariya, ta dawo daga yake-yakenta, sai ta ce wurin ya yi fadi da yawa. Idan aka gina hedikwatar mulki a wurin a wancan zamani na yake-yake, to mahara za su iya kai masu hari. Saboda haka, ta ce a koma kusa da rafin da ake kira Fadamar Bono a cikin gari, wanda daga baya da Fulani suka karbi mulki suka mayar da sunan zuwa Fadamar Sarki.

Da aka gama sake shata gari, sai Sarauniya Amina ta sa wa wannan zagayen da’irar da aka yi sunan kanwarta, wato Zariya.  Don ta girmama suna ‘yar uwarta, kuma dalilin sunan garin Zariya kenan. Kuma ta gina gida a cikin gari, inda ya zama fadar Zazzau, inda mahaifinta ya zauna, kuma har yanzu nan ne fadar masarautar Zazzau.  Ana kiran gidan da sunan ‘Gidan Bakwa’.


Asalin Ganuwar Zazzau

A zamanin da,  mai karfi shi ke da iko a kasashen Hausa da sauran wurare, saboda haka kowacce kungiyar al’umma da suke so su yi karfi, sai sun kewaye kansu, yadda mahara ba za su shigo masu ba. Wannan shi ne dalilin ganuwa a kasar Hausa, kuma inda duk aka yi ta, an yi ne don wurin ya zama hedikwatar mulki na al’ummar wajen.

To, a Zazzau wadanda suka fara yin ganuwa a cikin gari, aka mayar da cikin gari hedikwata, wato babban birnin mulki na Zazzau, su Bako Turunku ne, mahaifin Sarauniya Amina ta Zariya.   

Ganuwar Zariya, ita ce ta dauka tun daga dutsen Kufena, ta kewaya zuwa Hanwa, ta shigo wajen barikin soja, inda ake kira Jushin Waje. Ta biyo ta Kofar Galadima, ta Kofar Kona, ta hada da rafin Saye, sannan ta koma ta Gwargwaje, ta hadu da Wusasa, kana ta koma Kufena. Saboda sanin dabarun yaki, sai Sarauniya ta sa bawanta, wato Bono, ya je ya sara da’ira da rafin Sarki a tsakiya ya kewaya aka yi kofofin garin guda takwas, wadanda suka hada da Kofar Kibo, da Kofar Kona da Kofar Galadima, da Kofar Bai, da Kofar Doka wadda a da ake kira Kofar Kano, da Kofar Jatau, da Kofar Kuyambana da kuma Kofar Gayan.


Sarauniya Amina

Sarauniya Amina Habe ce ta Zazzau, sai dai wasu masana tarihi na kallon ta a matsayin Sarauniya, amma ba Sarki ba ce, don haka babu sunanta a jerin sarakunan Habe. Ma’ana, akwai sarautu da ake ba ’ya’ya mata a da a karkashin sarautar Habe. Alal misali, akwai Sarauniya, akwai Gimbiya, akwai Iya, akwai Madanni, da dai sauran su. Duk wadannan sarautu ne na ’ya’yan sarakunan Habe.

Saboda haka, Sarauniya Amina ba wai ta zama ita ce Sarki ba, a lokacin mahaifinta (Bakwa Turunku) yana sarki, ita kuma tana matsayin sarauniya, wato babbar ’yar sarki. Bisa al’ada, babban dan sarki shi ne shugaban rundunar sojoji na wannan masarauta.

To, ita Amina ita ke rike da wannan kambi, kuma ita ta yi ta yake-yake. Ta buga daga Zazzau ta yi arewa har Kano, har Katsina, ta kare iyakokin masarautar Zazzau.

Ta yi kudu da yamma, don kara fadi kasa da karfin mulki, kuma da haka ne ta dangana da kasar Naija ta yanzu, ta dangana da kasar Idah, wato kasar Attah Gara a jihar Kogi.

Ta je har kasar Nasarawa ta yau, saboda karfin yaki da iya gudanar da yaki da jaruntaka. Tana da rundunoni da take jagoranta, kuma duk inda suka tunkara suna yin nasara, kamar yadda tarihi ya nuna.

QUEEN AMINA

Sarakunan Habe

Tarihi ya nuna cewa, an yi sarakuna sittin na Habe, wadanda suka mulki masarautar Zazzau tun daga kan Gunguma, wanda shi ne ya fara yin sarauta a matsayin ‘Madau-Zazzau’ na farko a wancan lokaci, kuma shi jika ne na Bayajidda.

Habe sun kwashe shekaru fiye da dari suna mulki, har ya zuwa lokacin mulkin Sarkin Zazzau Makau, wanda shi ne na karshe a jerin sarakunan na Habe, wanda shi ne ya fara zuwa Suleja (wadda aka fi sani da Abu-Ja tun asali).

Ga kuma jerin sunayen sarakunan na Habe:

Gunguma

Matazu

Tumsah

Tumusa

Suleman

Maswaza

Dinzaki

Nagogo

Katchina

Nawanci

Macikai

Kawo

Bashi Kar

Majidadi

Dihirahi

Jinjiku

Sakannu

Monan Abu  daga shekarar 1550 zuwa 1530

Gidan Dan Masukanan  daga shekarar 1530 zuwa 1532

Nohir  daga shekarar 1532 zuwa 1535

Kawanissa daga shekarar 1535 zuwa 1536

Bakwa Turunku daga shekarar 1536 zuwa 1539

Ibrahim daga shekarar 1539 zuwa 1566

Karama daga shekarar 1566 zuwa 1576

Kafo daga shekarar 1576 zuwa 1578

Bako daga shekarar 1578 zuwa 1581

Aleyu I daga shekarar 1581 zuwa 1587

Isma’ilu daga shekarar 1587 zuwa 1598

Musa shekarar 1598

Gadi daga 1958 zuwa 1601

Hamza shekarar 1601

Abdullah daga shekarar 1601 zuwa 1610

Burema daga shekarar 1610 zuwa 1613

Aleyu II daga shekarar 1613 zuwa 1640

Muhammad Rabo daga shekarar 1640 zuwa 1641

Ibrahim Basuki daga shekarar 1641 zuwa 1654

Bako II daga shekarar 1654 zuwa 1657

Sukana daga shekarar 1657 zuwa 1658

Aeyu III daga 1658 zuwa 1665

Ibrahim  daga shekarar 1665 zuwa 1668

Muhammad Abu daga shekarar 1668 zuwa 1686

Sayo Ali daga shekarar 1686 zuwa 1696

Bako Dan Musa daga 1696 zuwa 1701

Is’haq daga shekarar 1701 zuwa 1703

Burema Ashakuka 1703 zuwa 1704

Bako Dan Sunkuru daga shekarar 1704 zuwa 1715

Muhammad Dan Gunguma daga shekarar 1715 zuwa 1726

Uban Bawa daga 1726  zuwa 1733

Muhammad Gani daga shekarar 1733 zuwa 1734

Abu Muhammad Gani shekarar  1734

Dan Ashakuku daga shekarar 1734 zuwa 1737

Muhammad Abu daga shekarar 1737 zuwa 1757

Bawo daga shekarar 1757 zuwa 1759

Yunusa daga shekarar 1759 zuwa 1764

Yakubu daga shekarar 1764 zuwa 1767

Aleyu IV daga shekarar 1767 zuwa 1773

Cikoku daga shekarar 1773 zuwa 1779

Muhammad Maigamo daga shekarar 1779 zuwa 1782

Is’haq Jatau daga shekarar 1782 zuwa 1802

Muhammad Makau daga shekarar 1802 zuwa 1804

Yadda wasu wurare suka fita daga masarautar Zazzau

Lokacin da Shehu Usman Danfodiyo ya kawo jihadi a wuraren Hausa Bakwai da Banza Bakwai, Malam Musa yana jagorancin yaki. A tarihince, an ji cewa an kama Zazzau ba tare da an kashe ko da mutum daya ba. 

Malam Musa ya shiga Zazzau ta Kofar Bai, a lokacin sarkin Zazzau na karshe na Habe, Sarki Makau ya fita da dakarunsa, ya bi hanyar Hunkuyi, hanyar Kudan, hanyar Kano, tun da an ba shi labari cewa, Malam Musa zai biyo ta hanyar Kano, to sai ya bi wannan hanya.

Shi kuma Shehu Usman Danfodiyo, sai ya ba Malam Musa shawara to ya kauce wa wannan hanya. Ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin ilhamar manyan malamai na da, bayin Allah, suna addu’a, suna rokon Allah Ya ba su haske da ilhamar yadda abubuwa za su kasance.

Sai aka fada wa Malam Musa, cewa kar ya bi waccan hanya ta Kano, ya zagaya ya bi ta garin Likoro. Kuma haka ya bi, ya zagaya ya bi Farin Kasa da ke kasar Soba ta yanzu, sannan ya bullo wa Zariya ta Kofar Bai, ya kuma shiga garin.

Bayan shi kuwa Sarki Makau yana ta baryar arewa maso gabas, yayin da Malam Musa ya bullo ta arewa maso yamma, saboda haka ba a hadu an gwabza yaki ba.

Da haka Malam Musa suka shiga cikin birnin Zariya, suka rufe kofofin birnin, Sarki Makau na waje, yana jira, sai labari ya isa gare shi, cewa ai Fulani sun shiga Zariya sun kulle kofofi, wato an kori su Sarki Makau kenan.

Daga can Sarki Makau ya gudu, ya nufi kudanci, ya je nan, ya je can, don a lokacin akwai sarakuna irin su Sarkin Fatika da Sarkin Kajuru da Sarkin Kauru da sauran su, wadanda duka da suna bin Sarkin Zazzau na Habe.

Amma da Fulani suka zo, sai suka yi wa Sarki Zazzau Makau tawaye, suka bi Fulani. Suka ci gaba da biyayya, suka kuma zauna a karkashin Sarkin Zazzau musulmi, Bafulatani. Da haka fadin kasar Zazzau ya fara raguwa.

Bayan da Sarki Makau ya bar Zazzau, ya nufi kudanci yana neman goyon bayan kananan sarakunasa da ke can gefe,  wadanda tun zamanin Sarauniya Amina aka ci su da yaki, suna biyayya ga masarautar Zazau.

To, Shehu Usman Danfodiyo ya ce, idan mayakan Malam Musa sun sadu da wani wuri da wani babban dutse a kudu maso yamma da Zazzau, su tsaya a wurin. Iyakar daular da yake so ya tabbatar kenan. Inda Makau ya tafi, ya wuce wannan wuri, to, kar su bi shi. Hakan ne kuma aka yi.

Wannan shi ya sa aka kafa Zazzau Suleja a wurin, shi Sarkin Zazzau Makau shi ya tsaya a nan, kuma dakarun Malam Musa ba su ci gaba da bin su ba, suka koma Zariya. Saboda haka, ba a yi yaki da ya wuce wannan wuri ba.

Wato dai masarautar Suleja daga Zazzau ta fito, don haka har gobe masu sarautar Suleja suke kiran kansu da mukamin Sarkin Zazzau, amma Suleja. Shi ya sa za ka ji ana cewa, Sarkin Zazzau Suleja. Kuma duk sunayen unguwannin da ke cikin birnin Zariya, su ne za ka samu a Suleja, kamar su Kwarbai, Anguwan Fatika, su Kusfa, Anguwan Iya da dai sauransu. Saboda sun maimaita wadannan abubuwa da suka baro a Zariya.

Sai dai kuma a wani kaulin, an ce Malam Musa ya ziyarci Zariya ne tun kafin jihadin Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya zauna a birnin yana koyar da karatun Al-Kur’ani da sauran littattafan addinin musulunci.

To, da jihadin ya shigo, ya kasance yana cikin mukarraban Mujaddadi Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya sami matsayin ja-goran yaki. Da haka Malam Misa da mayakansa suka kai hari ga Muhammadu Makau, Sarki na  sittin a jerin sarakunan Habe, a ranar Asabar goma ga watan Zulhaji a shekarar 1804, lokacin yana filin sallar Idi da ke wajen garin Zariya.

Duk da yake dai Muhammadu Makau yana tare da dimbin mazaje tare da shi a lokacin harin, an ci shi da yaki. Saboda ba sa iya komawa cikin gari su dauko makamansu. Don haka aka tilasta masa tserewa tare da wasu magoya bayansa zuwa  Zuba da ke kudancin yankin masarautar Zazzau, inda a can ne ya yi tirjiya ga hare-haren Fulani. Daga cikin mutum dubu uku da ke tare da shi akwai ‘yan uwansa Abu-Ja da Abu-Kwaka.

A wannan wuri ne Sarki Makau ya zauna, kuma wadanda suka gaje shi suka  karfafa, suka kafa wata sabuwar masarautar Zazzau ta Habe mai cin gashin kanta a kasar da daga baya aka rika kira Abuja. Da ma kuma jama’ar yankin suna biyayya ga sarakunan Zazzau.

Wannan masarauta ta Habe ta rayu har ya zuwa lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, duk kuwa da matsanantan hare-hare da Fulani ke kai masu. Kuma sarakunann Zazzau na Abuja, sun rike mukaman da suke da su na asali tun daga Zariya.

Sarakunan Habe na Suleja (Abu-Ja)

Sarakunan Habe na Suleja (Abuja), sun samo asali ne daga tsatson Is’haq Jatau, Sarkin Zazzau na hamsin da tara a Zariya, wanda ya yi sarauta daga shekarar 1782 zuwa 1802. Ga kuma jerin sarakunan da suka yi mulki a wannan masarauta ta Suleja (Abu-Ja) daga farko zuwa yau:

Muahammadu Makau daga shekarar 1804 zuwa 1825

Abu-Ja daga shekarar 1825 zuwa 1851

Abu-Kwaka  daga shekarar 1851 zuwa 1877

Ibrahim Iyalai daga shekarar 1877 zuwa 1902

Muhammad Ganu daga shekarar 1902 zuwa 1917

Musa Angulu daga shekarar 1917 zuwa 1944

Suleman Barau daga shekarar 1944 zuwa 1979

Ibrahim Dodo Musa daga shekarar 1979 zuwa 1993

Muhammad Awwal Ibrahim daga shekarar 1993 zuwa yanzu

A yanzu dai akwai masarautu biyu na Zazzau, wato Zazzau ta Fulani da ke da hedikwata a Zariya, da kuma Zazzau ta Habe mai hedikwata  a Abuja wato wurin da a yanzu aka fi sani da Sule-Ja).


Sarakunan Fulani

A lokacin da Shehu Usmanu Dafodiyo ya yi jihadi daga shekarar 1804, kasar Zazzau ta dangana da inda Habe suka tsaya, wato kasar Idah a jihar Kogi ta yau.

A zamanin Sarkin Zazzau, Malam AbdulKarim, daga baryar kudu masarautar Zazzau ta dangana da har zuwa inda a yanzu ake kira Nasarawa, kuma har zuwa gabar kogin Benuwai.

A baryar arewa kuwa ta yi iyaka da sauran kasashen Hausa bakwai, kamar Katsina ta fuskar arewa, da Kano ta fuskar arewa maso gabas, sai Bauchi da Filato a arewa maso yamma. Kuma daga Zazzau ne ake nada sarakunan kasashen da ke karkashin masarautar ta Zazzau

Sarkin Zazzau na farko a karkashin daular Usumaniyya, shi ne Malam Musa, wanda Shehu Usumanu Danfodiyo ya ba tutar jaddada musulunci a kasar Zazzau, kuma na karshe kuma shi ne Sarkin Zazzau Makau wanda Turawan mulkin mallaka suka kawar.

Ga kuma jerin sunayen sarakunan Zazzau na Fulani:

Malam Musa daga shekarar 1804 zuwa 1821                                                     

Malam Yamusa deaga shekarar 1821 zuwa 1834                                                           

Malaam AbdulKarimu daga shekarar 1834 zuwa 1846

Malam Hammada daga shekarar 1846 zuwa 1853                                                  

Mamman Sani daga shekarar 1846 -1853

Sidi AbdulKadir daga shekarar 1853-1853

Malam AbdusSalami daga shekarar 1853 zuwa 1854

Malam AbdulLahi (nadi na farko) daga shekarar 1857 zuwa 1871 da (nadi na biyu)

daga shekarar 1874 zuwa 1879

Malam Abubakar daga shekarar 1879 zuwa 1888

Muhammadu Sambo daga shekarar 1888 zuwa 1890

Muhammadu Yero daga 1890 zuwa 1897

Sarki Malam Kwasau daga 1897 zuwa 1902 (shi ne sarki na karshe kafin zuwan Turawa)


Zuwan Turawan mulkin mallaka

Alu Dan Sidi (shi ne Sarkin Zazzau wanda Turawan mulkin mallaka suka fara nadawa) daga shekarar 1903 zuwa 1920

Sarki Dalhatu daga shekarar 1920 zuwa 1924

Sarki Ibrahim Dan Sarkin Zazzau Kwasau daga shekarar 1924 zuwa 19337

Sarki Jafaru daga shekarar 1937 zuwa 1959

Alhaji Muhammadu Aminu daga shekarar 1959 zuwa 1975

Alhaji Shehu Idris (wanda ke kan karagar mulki yanzu) daga shekarar 1975 zuwa yau

Gidajen Sarautar Zazzau

A karkashin Daular Fulani, masarautar Zazzau tana da gidaje hudu, wadanda  suka hada da:

·        Gidan Mallawa, wanda Malam Musa ya kafa,

1. Sarkin Zazzau Malam musa

2. Sarkin Zazzau Malam Abdulkadir dan Musa

3. Sarkin Zazzau Malam Abubakar dan Musa

4. Sarkin Zazzau Malam Alu Dan Sidi.

·     Gidan Barebari, wanda Yamusa ya kafa,

1.Sarkin Zazzau Malam Yamusa

2. Sarkin Zazzau Malam Hammada dan Yamusa

3. Sarkin Zazzau Malam Mamman Sani dan Yamusa

4. Sarkin Zazzau Malam Abdullahi dan Hammada                                                          

5. Sarkin Zazzau Malam Yero dan Abdullahi

6. Sarkin Zazzau Malam Kwasau dan Abdullahi

7. Sarkin Zazzau Malam Dalhatu dan Yaro

8. Sarkin Zazzau Malam Ibrahim dan Kwasau

9. Sarkin Zazzau Malam Ja'afaru dan Isiyaku

·        Gidan Katsinawa, wanda Malam AbdulKarim ya kafa,

1. Sarkin Zazzau Malam Abdulkarim

2. Sarkin Zazzau Malam Sambo dan Abdulkarimu

3. Sarkin Zazzau Malam Muhammadu Aminu

4. Sarkin Zazzau Malam Shehu dan Idrisu Auta

·        Gidan Sullubawa (Fulani), wanda Malam AbdusSalam ya kafa.

1. Sarkin Zazzau Malam Abdulsalam

Kowanne gida dai ya biyo asalin inda wanda ya kafa shi ne ya fito. Mallawa Fulanin Futo Toro  ne da suka fito daga kasar Mali,

Barebari kuma sun fito ne daga Kukawa a yankin da a yau aka fi sani da Jihohin Barno da Yobe, amma asali su Fulani ne, kuma ana kallon su ne a matsayin Fulani. Saboda haka ne ma ake kiransu da Fulata-Barno.

Haka Sullubawa Fulani ne da suka fito daga yankin jihohin Sakkwato da Kebbi, kuma yadda AbdusSalami Basullube ya sami sarautar Zazzau kenan.

Yadda aka sami gidaje hudu na sarautar Zazzau

Gidan sarautar Zazzau ya kasu hudu ne, saboda Zazzau kasa ce wadda ta tattara dimbin al’umma da suka fito daga wurare daban-daban, don neman ilimin addinin musulunci.

Saboda haka, a lokacin da jihadin Shehu Usman Danfodiyo ya zo, an sami malama ne masana  ilimin addinin musulunci, da shari’o’i, da kuma ka’idar mulki na musulunci.

A lokaci ba wai ana la’akari ne da cewa wane ya gada ko wane ne ya gada ba, ana neman wanda zai zama khalifa, don tabbatar da kafuwar addinin musulunci a Zazzau.

Zazzau wata cibiya ce, tun ma kafin jihadi Shehu Usman Danfodiyo, saboda kasancewarta ‘Zo-zo’, kasa mai albarka, mai daukar komai da komai na noma, tana da laima da ni’ima. Kowa yana son ya je ya zauna a Zazzau, ya amfana ta fuskar noma da kiwo.

Wannan ya sa Fulani da yawa suka zauna a Zazzau tun zamanin mulkin Habe, kuma da yawansu abin da suke yi baya ga kiwo, shi ne karatun addini. Kuma lokacin da dan uwansu Shehu Usman Danfodiyo ya bullo, sun kai masa gaisuwar caffa, suka yi masa mubayi’a, ya yarda da su. Suka zauna da shi, suka yi karatu tare da shi, suka yi yake-yaken da aka yi tsakanin Sarkin Gobir da Usman Danfodiyo.

Tun kafin a yi ganuwa, akwai mutane, wato Fulani, irin su Malam Musa da Yamusa da Malam AbdulKarim da su AbdulSalam da ke zaune a cikin garin Zariya, suna koyarwa ta addinin musulunci.

Da suka ji bullowar Shehu Usman Danfodiyo yana zuwa wurare daban-daban yana kira da a gyara addinin musulunci, suka yadda da abin da yake yi, suka yi masa mubaya’a

Tarihi ma ya nuna cewa, Malam AbdulKarim ya zauna da Shehu Usman Dan Fodiyo, ya yi karatu a wajensa. Shi kuwa Malam Musa kusan tsaran Shehu Mujaddadi ne, kuma tare suke tafiye-tafiye.

Gidan Malam Musa

Malam Musa shi aka ba tutar sarauta a lokacin da jihadi ya iso Zariya, Malam Musa shi aka ba wannan tuta, don ya yi jagoranci, kuma bayan mutuwar Malam Musa, ba a mayar da sarautar ta zama gado ba. 

To, bayan mutuwarsa ba a mayar da abin ya zama gado ba, sai aka ba wani daga cikin malaman da suke tare da Shehu Usman Danfodiyo, wato Malam Musa. Kuma Shehun ne da kansa ya ba shi tutar halifanci.

Gidan Malam Yamusa

Kana sai Shehu Usman Danfodiyo ya ba Malam Yamusa shugaban rundunar sojojin yaki na Malam Musa a matsayin Madakin  Zazzau.                                                  

Gidan Malam AbdulKarimu

Shi kuma Malam AbdulKarimu, Shehun ya ba shi sarautar Sa’in Zazzau, wato mai ilimin rabon arzikin kasa.Ya san masu dabbobi da suka cancanci bayar da zakka, ya san manoman da suka cancanci bayar da zakka, ya san nisabin dukiyar da za a fitar wa zakka. Ya kuma san su wa ya kamata a ba zakkar.

Gidan Malam AbdulSalam

Shi kuwa Malam AbdulSalami yana cikin dalibai Fulani wadanda suka yi amfani wajen taimakon Shehu Usman Danfodiyo a yake-yaken da ya yi tsakaninsa da Sarkin Gobir. Amma shi ba ya bullo ne kamar yadda su Malam Musa da Yamusa da AbdulKarimu suka bullo ba.

Hawan Malam AbdulSalam kan gadon sarauta ya kasance raba-gardama ne, saboda lokacin da sarautar Zazzau ta koma gado, ’ya’yan gidan sarakunan guda uku suka fara cewa sai daga cikinsu ne za a sami wanda zai zama sarki a Zazzau, sai ‘ya’yan Sarkin Zazzau Yamusa suka fara irin wannan  sarautar. Inda Hammada ya fara sarauta, daga nan sai kanensa Mamman Sani.

Bayan Mamman Sani ya kau, sai Sidi AbdulKadir, babban dan Malam Musa da Shehu Usman Danfodiyo ya ba tuta, ya zama sarki bisa gado. Shi ma yana da ilimin addini, kuma ya cancanci rike sarautar.

Sai dai bayan da Sidi AbdulKadir ya zama sarkin Zazzau, an yi ta samun kwamacala da rigingimu, tun da abin ya zama gado kowa ma dan gida yana ganin ya cancanci rike sarautar. Daga nan aka fara samun rashin yarda da juna, har aka kai kara Sakkwato, aka dakatar da Sarkin Zazzau Sidi AbdulKadir daga sarauta. Shi kuma ya ce, duk zargin da ake masa na sarautar ba shi kadai yake sarautar ba. Tare da shawarar dukkan ’yan majalisarsa ake yi, wato su masu son a ba su sarautar nan. Saboda haka, ba wanda ya cancanta a cikinsu, kamar yadda shi ma bai cancanta ba.

Saboda haka, sai sarkin musulmi na wancan lokaci ya ga ya fi dacewa a dauko wani malami cikin daliban Shehu Danfodiyo a ba shi jagoranci, duk da ya manyanta a wannan lokaci. Kuma lokacin ya yi tsawo, Malam Musa ya yi shekaru goma sha, Yamusa ya yi shekaru goma sha, AbdulKarim ya yi shekaru goma sha, Hammada ya yi ’yan kwanaki, Mamman Sani ya yi shekaru, Sidi AbdulKadir ya yi wata takwas zuwa goma a gadon sarauta. To, idan ka tara wadannan shekaru, ka ga an dumfari shekaru arba’in.

To, shi Malam AbdulSalam idan ka dora shekara arba’in a kan shekarunsa, ka ga ya manyanta. Amma sai sarkin musulmi na wancan lokaci ya ce a ba AbdulSalami sarautar Zazzau ya rike. Da haka ya zama raba-gardama. Ba a ba kowa ba daga cikin ‘ya’yan wadancan sarakuna. Wannan kuma shi ne dalilin zuwan gida na hudu a sarautar Zazzau kenan, wato don a sami natsuwa.                                                                                                                                                                                                             

Ta haka ne aka sami wadannan khalifofi guda hudu, kuma kowannensu an ba shi sarauta ne a matsayin kansa na masanin addinin musulunci, na mai biyayya da gaskata abin da jihadin Shehu Usman Danfodiyo ya kawo bisa koyarwa Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW).

Tarihin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris

Haihuwa da Tsatson Sarki

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo.

Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin ‘ya’yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo ya yi a kasar Zazzau, kuma shi ne ya assasa gidan Katsinawa a sarautar Zazzau.

Ina Sarki ya taso?

Shi Mai martaba Sarki lokacin mahaifinsu yana Mai Unguwa a unguwar Iya a nan aka haife shi. Unguwar Iya wata unguwa ce da ke tsakanin unguwar Durumi da Kuyanbana. A nan ya girma, ya shekara akalla bakwai, inda har ya shiga makarantar allo, ya fara karatun addini.

A nan dai unguwar Iya ya yi makarantar farko da Bature ya gina a cikin birnin Zariya, wadda ake kira ‘Town School one’, ita ce kuma makaranatar ‘Kofar Kuyanbana Local Government Education Primary School’. Yanzu ana ce mata ‘Waziri Lawal Local Government Education Primary School’, a nan ya fara karatu.

Bayan ya gama sai ya tafi Alhudahuda College, lokacin ana kiran makarantar da sunan ‘Middle School’.  Daga nan aka yi masa sauyi, ya koma makarantar koyar da malunta a Katsina lokacin ana kiran ta ‘Katsina Teachers’ College’.To, a nan ya koyi aikin koyarwa, wanda shi ne babbar sana’arsa ta farko da ya iya.

Daga baya mai martaba ya sauya daga malamin makaranta ya shiga aikin mulki, wanda har ya je kasar Ostireliya (Australia). Yana cikin daliban farko da ofishin jakadancin Ostireliya suka dauki dawainiyarsu suka je suka yi karatu na koyon ilimin mulki a kasar ta Osireliya

Wuraren da ya yi aiki

Daga shekarar 1956 ya koyar a wurare daban-daban a cikin garin Zariya da kauyuka. Ya koyar a Zangon Aya, ya koyar a Paki, har ya yi hedimasta a Pakin. Ya kuma yi hedimasta a Hancin Kare a makarantar ‘Town School No.3’’.

A shekarar 1962 ya koma aikin mulki, lokacin da ya koma karkashin hukumar ‘NA’ (Native Authority) ta Zariya a zamanin Sarkin Zazzau Aminu. Inda ya gwama aiki biyu, wato yana aiki a hukumar ‘NA’, kuma yana aiki a matsayin jami’in sadarwa na hukumar kula da kananan hukumomi da masarautu na jihar Arewa.

Daga baya Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki. Daga nan ne sai aka nada shi sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin masarauta a karkashin ‘Native Authority’ a wannan lokacin.                                                              

Ya rike wannan mukami na tsawon kamar shekara biyu zuwa uku, sai Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya nada shi hakimin birni da kewaye, mukamin da ya rike na tsawon shekara biyu zuwa uku, yana hakimi. Kuma Dan Madamin Zazzau.

A shekarar 1975 likafarsa ta yi gaba, aka ba shi a sarautar Sarkin Zazzau.

Sauyin da ya kawo a sarautar Zazzau cikin shekaru arba’in da biyar yana mulki

Makusantan Sarkin suna ganin ba wani al’amari da ya shafi rayuwar Zage-zagi a birnin Zariya ko a masarautar Zazzau ne da ba a sami ci gaba ba. Ta fuskar ilimi, tun daga kananan makarantun firamare zuwa sakandire, zuwa na gaba da sakandire, zuwa jami’o’i, makarantun sojoji da sauransu da aka yi a masarautarsa, akalla ba za a rasa makarantu ashirin ba.

Iyalin Sarki

Allah Ya albarkaci mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris da iyali masu yawa. Yana da mata hudu, da ‘ya’ya maza da mata da yawansu ba zai gaza arba’in da biyu ko da biyar ba.

Dabi’u da halayen Sarki

Daya daga cikin hakiman masarautar Zazzau, Salanken Zazzau, Dokta Muhammadu Bello AbdulKadir, ya ce, babbar baiwar da Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, shi ne hakuri, yana da hakuri matuka.

Ga shi kuma yana da kawaici, wanda a sakamakon haka ne ya kai kusan shekara ashirin yana sarauta, amma bai nada kowa daga cikin ‘ya’yansa sarauta ba, saboda kawaici. Sai da dattawa suka matsa masa, cewa idan bai nada ‘ya’yansa a sarauta ba, wa zai nada masa su.

Hakurinsa da dauriya suka sa Zazzau ta zama kowa ya zo karbabbe ne, zai zo ya sami karbuwa wajen al’umma ya yi kasuwanci, ko ya nemi ilimi, ko ya yi kasuwanci ko sana’a da sauransu.

Don haka, birnin Zariya ya zama wata matattarar kowacce kabila daga sassa daban-daban na Najeriya; ba kabilar da ba za ka samu ba a masarautar Zazzau.

Masallacin Juma’ar masarautar Zazzau

Zazzau wurin ne wanda tun kafin bullowar jihadin Shehu Usman Danfodiyo akwai rukuni-rukuni na Fulani a cikin gari da kauyuka wadanda aikinsu shi ne bayar da karatu na addinin musulunci. Kuma tun a wannan lokaci akwai masallacin juma’a a unguwar Juma cikin birnin Zariya, wanda aka gina a zamanin mulkin Isiyaku Jatau wanda Habe ne.

Malaman unguwar Juman nan ko da aka yi jihadi sun ci gaba da limanci, kuma har yau su ke limanci, tun da su ma Fulani, kuma an same su da iliminsu. Ko da Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim ya gina masallaci a kofar fada, wancan masallacin na unguwar Juma ya rushe, an ci gaba da yin sallar Juma’a tare da limanci wadannan Fulani na unguwar Juma.Har yau zuri’arsu ke limanci.  

Abin da kasar Zazzau ta ginu a kai

Ita Zazzau kasa ce da ma da ta ginu ne a kan abubuwa biyu, wato ilimin addinin musulunci, da harkar noma da kiwo. Kuma ko da Shehu Usman Danfodiyo ya yi jihadinsa abin da ya karfafa kenan.

Wasan Kanawa da Zage-zagi

Kamar yadda masana tarihi kan fada, mai karfi shi ke da iko. To, a wancan zamani, daular da ta yi karfi sai ta yunkura ta je ta mamaye wata. To, inda aka yi nasara, sai ka ji, amma inda aka gwabza, aka yi kare jini biri, ko kuma kowa ya tare kan iyakarsa, sai ka ji irin wadannan wasannin suna aukuwa.

Haka ma inda aka sami nasarar cin su da yaki, sai ka ji irin wannan wasa yana faruwa. Misali za ka ga Katsinawa da Gobirawa ana irin wannan wasa.

To, Kanawa da Zage-zagi ma akwai wannan wasa, cewa ita Sarauniya Amina ta kai hari Kano har Kofar Mata. Wannan kofar ai ana cewa nan ne aka dakatar da Sarauniya Amina, aka hana ta shiga cikin birnin Kano.

A wancan zamani na mulkin Habe dai, an ce an wani sarkin Kano ya kawo farmaki har Zariya, amma aka tare shi a tsakanin yankin da a yanzu aka sani da karamar hukumar Kubau, wajen garin Kargi. Aka yi ba-ta-kashi.

Saboda haka, ba mamaki ka ji ana wasa tsakanin Fulani da Barebari, tsakanin Katsinawa da Gobirawa, tsakanin har Yarabawa da Gobirawa. Kuma za ka ga irin wannan wasa yana dada dinke zumunci ne, ba yana batawa ba ne.

Wannan dai duk a zamanin mulkin Habe ne aka yi ire-iren wadannan hare-hare. Amma yayin da aka sami shigowar daular Usumaniyya, sai kasashen suka zama daya, addinin musulunci ya hade su. Saboda haka, wata kasa ba ta kai wa wata kasa farmaki ba a cikin titocin da Shehu Usumanu Danfodiyo ya kafa. Sun zama abokan aiki, abokan hulda, kuma abokan shawarar juna.

Girman kasar masarautar Zazzau a halin yanzu

Sauyin da aka samu bisa sabon tsari na gwamnati, a yanzu a kowacce karamar hukuma ana da gundumomi ashirin da uku wadanda hakimai suke mulki a karkashin Mai Martaba Sarkin Zazzau. Kamar dai yadda gwamnatin jiha mai ci yanzu ta mayar da su.

Amma gwamnatin baya ta nunnunka wadannan gundumomi, saboda ana shigo da harkar siyasa a cikin masarautun. Wata gwamnatin ta zo ta kara gundumomi, har sun kai tamanin da shida, ita kuma wannan gwamnati da ta zo sai ta rage su zuwa ashirin da uku.

A zamanin mulkin soja an yanke wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Kaduna, wadanda ke lardin Zazzau, wadanda suka hada da Kaciya da Zonkwa. Ta yankin kudu, sai aka bar lardin na Zazzau da kananan hukumomin Igabi da Kaduna ta kudu da Kaduna ta Arewa. Ta arewa akwai kananan hukumomin Giwa da Kudan, ta gabas kuwa akwai Makarfi da Ikara da Kubau. A yankin tsakiya kuwa akwai kananan hukumomin Soba da Sabon Gari da Zariya. A yanzu kananan hukumomi goma sha daya da gundumomi ashirin da uku kenan suke bin masarautar Zazzau a yau.

A da kuwa tun daga karamar hukumar Kaciya, zuwa Chikun, har zuwa Kagarko, duk suna bin Zazzau ne. Amma daga baya aka sami wata gwamnati ta soja ta yanke wadannan kananan hukumomi, ta yi wasu sababbin masarautu, abin da ya sa aka sami masarautu kusan talatin da biyu. Saboda ra’ayin siyasa na son a ba kowacce kabila ‘yancinta, kar a ce an danne wani yanki a jihar.

Wadanda suka yi aiki

Bincike da Rubutawa: Abdussalam Ibrahim Ahmed

Shiryawa da Tacewa: Halima Umar Saleh da Nasidi Yahaya

Tsarawa: Nkechi Ogbonna

Zane: Manuella Bonomi

Hotuna da Bidiyo: Getty, Kaduna State Government da Masarautar Zazzau.