Tambayoyi a kan yin talla a shafukan BBC

Abubuwan da suka sa BBC ta fara talla a shafin intanet dinta

BBC ta fara tallata hajar mutane a shafukanta na intanet domin tallafa wa 'yan jaridarta da kuma rage radadin rashin kudin da take ciki sakamakon janye hannun da gwamnati ta yi daga daukar nauyinta.Ta yi hakan ne bisa ka'idojin da gwamnati ta sanya, don haka wasu sassanta za su rika yin talla. A yanzu dai ana sanya talla a shafukan intanet na sassa da dama da kuma zangon FM da ke Berlin.

Ina Biritaniya amma ina ganin talla a shafukan BBC. Shin me ya sa?

Muna iyaka kokarinmu domin tabbatar da cewa mutanen da ke zaune a wajen Biritaniya ne ka dai za su ga talla, kuma muna amfani da fasahar zamani domin tabbatar da hakan. Amma idan kun ga talla a shafin BBC a cikin Biritaniya, ku sanarda mu cikin gaggawa ta hanyar e-mail.

Ta yaya zan tuntubi BBC da tambayoyin a kan tallace-tallace?

Aika sako zuwa wadanda adreshin: hausa@bbc.co.uk.

Domin karin bayani a kan tallace a BBC, sai ku duba adreshi kamar haka:

Shin kuna sha'awar saka tallaka a BBC? Latsa nan domin karin bayani (INGILISHI): http://advertising.bbcworldwide.com/

Yaya mu ke yanke shawara a kan tallar da za mu iya dauka a shafukanmu? Latsa nan domin karin bayani (INGILISHI)