Game da aika wa

Me ake nufi da aika wannan bayani? Wannan zai baka damar aika bayanai daga shafin salula na BBC ga mutane ta hanyar email ko shafukan sada zumunta.

Me ake nufi da aika wannan ta email? Wannan zai baka damar aika bayanan daga shafin salula na BBC ga kowanne adreshin email da ka saka a wayarka.

Ta yaya ake amfani da shi? Idan kaga wani shafin salula na BBC da kake son yadawa, latsa alamar email da ke kasan shafin. Wannan zai bude maka wurin aika sakon email daga wayarka wanda zai baka damar samun adreshin mutanen da kake da su a wayarka, sannan ka rubuta musu sako tare da shafin da kake son yadawa.

Me ya sa baya yi a wayata?

Kana bukatar ka sanya email a wayarka kafin ka samu damar amfani da tsarin yada wannan ta email. Idan baka da tabbas kan yadda za ka sanya email a wayarka, tuntubi takardun da wayar ta zo da su da ke bayanin yadda ake amfani da wayar.

Nawa ake biya?

BBC bata cajar ko kwabo a kan wannan. Sai dai kamfanin wayarka na iya cajarka game da intanet din da aka yi amfani da shi . Idan baka da tabbas kan kudinda za a cajeka, tuntubi kamfanin wayar salularka.

Shin ko BBC tana ajiye bayanaina?

A'a. Tunda dai za ka yi amfani ne da adreshinka na email, ba za mu shiga adreshinka ko kuma ainahin sakon da za ka tura ba. Domin samun karin bayani kan matsayar BBC game da sirrin mutane, duba shafin da ke bayani kan manufofin sirri.

Me ake nufi da aika wannan ta Facebook ko Twitter? Wannan zai baka damar yada bayanai daga shafin salula na BBC zuwa shafin Facebook ko Twitter.

Ta yaya wannan ke aiki? Idan kaga shafin salula na BBC da kake son ka yada, latsa alamar Facebook ko Twitter a kasan shafin. Daga nan za a fito maka da shafin Facebook ko Twitter domin ka shiga shafinka da ka yi rijista. Za ka iya rubuta sako. Idan za ka yada ta Twitter ne, za a wallafa hoto daga shafin. Shafin da kake son yadawa zai fito a dandalinka na Facebook ko Twitter.

Shin sai na bawa BBC bayanan shafin sada zumunta na?

A'a. Da zarar ka shiga shafin Facebook ko Twitter, to za a fitar da kai daga shafin salula na BBC zuwa shafinka na sada zumunta, a don haka BBC ba za ta iya ganin bayanan sirrinka ba a kodayaushe.

Me yasa na tafi shafin yadawa kai tsaye ba tare da an nemi na sanya bayanai na ba?

Wasu wayoyin salular na ajiye bayanan mutum na Facebook da Twitter, wanda hakan ke nufin ba sai ka sake saka bayananka ba a duk lokacin da kake son wallafa bayanai a dandalinka.

Shin BBC na ajiye bayanai na?

A'a. A daidai lokacin da kake barin BBC zuwa shafin sada zumuntarka, ba za mu iya samun bayanan sirrinka ko kuma sakon da za ka tura ba. Domin samun karin bayani kan matsayar BBC game da sirrin mutane, duba shafin da ke bayani kan manufofin sirri.