Shirye-Shirye

Labarun Duniya

A kowace rana, Sashen Hausa na BBC yana watsa labarun duniya na akalla tsawon minti biyar a harshen Hausa a lokuta kamar haka: 0530 da 0630 da 1345 da 1930 agogon GMT.

Akan kama shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC a kan mitoci kamar haka:

  • 0530-0600: Mita 49 da 41 (Megahertz 5975, 6135, da 7205)
  • 0630-0700: Mita 31, da 21 da 25 ( Megahertz 9440, 7255 da 11750)
  • 1345-1415: Mita 16 da 13 ( Megahertz 15105, 17780 da 21630)
  • 1930-2000: Mita 41, da 19 da 16 ( Megahertz 11890, 15105, da 17885)

Labaru da Rahotannin yau da kullum

Galibin shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC suna kunshe da labarai da rahotanni na yau da kullum ne.

Wakilan BBC a sassa daban-daban na duniya sukan aiko da rahotanni a kan muhimman abubuwan da ke faruwa a duniya, tare da labarai na abubuwan da ke faruwa a Nigeria da jamhuriyar Niger.

Akwai labarun duniya na tsawon akalla minti biyar a cikin kowane shiri da Sashen Hausa na BBC ke watsawa.

Daga ranar Litinin har zuwa ranar Juma'a, dukkanin shirye-shiryen sashen Hausa na BBC, suna dauke da rahotanni daban-daban a kan labarun yau da kullum, na akalla tsawon minti ashirin. Labarin wasanni

A ranakun Litinin zuwa Juma'a, akwai labarin wasanni a shirin karfe 1930 agogon GMT da kuma shirinmu na 0630 agogon GMT.

Ra'ayi Riga

A shirinmu na 1930 GMT, a maimakon labarai da rahotanni, muna gabatar da shiri na musamman ne na Ra'ayi Riga inda masu sauraro ke bayyana ra'ayoyinsu kan wasu batutuwa da suke ci wa al'umma tuwa a kwarya.

Daga Jaridun Nigeria

Ranar Litinin a shirin karfe 0530 agogon GMT, akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da Jaridun karshen mako na Nigeria suka wallafa. Daga Jaridun Kasashen Duniya

Ranar Talata a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun wasu kasashen duniya suka wallafa.

Ranar Laraba a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun jamhuriyar Nijar suka wallafa.

Ranar Alhamis a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun kasar Kamaru suka wallafa.

Ranar Juma'a a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun kasar Ghana suka wallafa.

Shirye-Shiryen karshen mako

A cikin shirinmu na 0530 GMT na safiyar Asabar, muna gabatar da shirin Gane-Mini Hanya a kuma maimaita shi a shirin rana 1345 GMT. Muna gabatar da shirin Gata nan-Gatananku a cikin shirin Hantsin Asabar, a kuma maimaita a shirin hantsin ranar Lahadi. Shirin Amsoshin Takardunku na zo wa masu sauraronmu ne a ranar Asabar da maraice 1930 GMT, a kuma maimaita ranar Lahadi da rana 1345 GMT. Shirin Taba-Kidi-Taba-Karatu kuwa, ana gabatar da shi ne da safiyar Lahadi 0530 GMT a kuma maimaita a shirin dare na Lahadin 1930 GMT.

Za a iya tuntubar mu a wannan addreshin na email: hausa@bbc.co.uk

Karin bayani