Taimako da kuma Tambayoyin da aka saba yi

Taimako da kuma Tambayoyin da aka saba yi

Taimako da kuma Tambayoyin da aka saba yi

Hanyar da ta fi dacewa wajen ganin shafin

Wannan shafin an gina shi ne dai-dai da akwatin kwamfiyuta mai tsawo da fadin 1024 pixels. Idan kana amfani da akwatin kwamfiyutar da fadinta bai kai haka ba, to za ka bukaci ka daga shafin sama domin ganin dukkan abubuwan dake cikin shafin. Ko kuma ka shiga shafin mai rangwamen hotuna.

Wasu daga cikin abubuwan dake cikin shafin za su yi aiki ne kawai, idan an baiwa Javascript din dake cikin browser damar yin aiki. Shiga nan domin samun bayanai a cikin harshen turanci a kan yadda ake baiwa Javascript damar yin aiki a cikin browsa din da suka shahara.

Yadda ake kallon hoton bidiyo da sauraran sauti a shafin

Za a iya samun hotunan bidiyo da sauti a sassa daban daban na shafin BBCHausa.com. Wasu lokutan suna a ware, a wasu lokutan kuma hade da labarin da ya dace. Domin kunna hotunan bidiyon ko sautin, za a bukaci hada kwamfiyuta da intanet mai saurin akalla kbps 56, amma za a fi samun gamsuwa idan aka hada kwamfiyuta da hanayar intanet din broadband wanda ya fi hakan sauri.

Domin kallo\sauraron bidiyo ko muryar da aka hada cikin labari, za a bukaci Flash Player. Latsa nan don sauko da Flash Player

Domin kallo ko sauraron sauran sauti ko hoton bidiyo kuwa, za a bukaci ko dai Real Player ko kuma Windows Media Player.

  • Latsa nan don sauko da Real Player
  • Latsa nan don sauko da Windows Media Player

• Rashin alhaki: Duk wasu manhajoji da za ka bukata domin kallo ko sauraron wani abu a shafinmu na bbc.co.uk, kyauta ake sauko da su. Ba za a taba bukatar a bayar da wasu bayanan biyan kudi ba, misali bayanan katin banki.

A duk lokacin da aka sauko da wadannan manhajojin, za a bukaci da a amince da wasu ka’idoji na wancan kamfanin. Wannan bai shafi BBC ba. Ya kamata shi wancan kamfanin ya sanar da ku abin da zai yi da bayananku.

Cikakkun bayanai ta hanyar – RSS + ATOM

Bayanai ta hanayar RSS na bada damar a san lokacin da aka wallafa sabbin bayanai a shafin intanet. Za a iya ganin kanun labarai da dumi-duminsu da hotunan bidiyo a waje daya da zarar an wallafa su, ba tare da an ziyarci shafin intanet din da aka jono bayanan daga cikinsa ba.

Ana ci gaba da tattaunawa a kan ko menene RSS. A takaice dai RSS wasu shafukan intanet ne da aka gina su domin kwamfiyutoci su yi ta’ammuli da su ba mutane ba.

Ta yaya zan aiko muku da hotuna, sauti da kuma hoton bidiyo?

Latsa nan domin shiga shafin da za a yi amfani da shi wajen aiko mana da hotuna, sauti da kuma hoton bidiyo.

Mika koke / Maida martani

Latsa nan don aiko mana da ra’ayoyinku.

Yadda ake sauraron shirye-shiryen BBC Hausa na radiyo

Menene GMT

Greenwich Mean Time ko GMT a takaice, shi ne lokacin da ake aunawa daga layin longtitude ko meridian na ma’aunin sifir na duniya.

Ana nuna lokutan BBC mai watsa shirye shiryensa ga kasashen duniya ne a ma’aunin lokaci na GMT.