Minene RSS?

A halin yanzu gidan Redioyon BBC yana Samar da Labarai ta Hanyar RSS a harsunan da yake watsa labarai cikinsu, ciki har da bbchausa.com.

Mecece Hanyar Samar da Larabai ta RSS?

Samar da Labarai ta RSS, hanya ce a saukake, wadda da kanta za ta tabbatar ka kasance a sane da irin labari da bayanin da ka fi so daga bbchausa.com.

Kowane lokaci na rana ana sabunta labarai da rahotannin na al’amurran sha’awa na musamman a bbchausa.com. Kàna, za a sabunta Hanyar Samar da Labaran ta RSS ta hanyar Makaranciyar Larabaranka ta RSS. A cikin Makaranciyar Labaranka, za ka ga kanun labarai na mafiya sabunta – kowane da labaran a takaice – da kuma mahadar da za ta kaika ga cikakken labarin.

Ko ta yaya zan iya yin rajistar neman Hanyar Samar da Labarai ta RSS daga bbchausa.com?

  • Lalle ne ka mallaki manhajar “RSS News Reader”, wato Makaranciyar Labarai ta RSS. Wannan manhaja tana nuna labarai da bayanan RSS daga adadin dandalin intanet da ka zaba a kwamfutarka.
  • Latsa aninin Hanyar Samun Labarai ta RSS daga bbchausa.com. Za ka ga shafin alamar xml a manhajarka ta shiga intanet.
  • Don kara wata hanyar ga Makaranciyar Labaranka ta RSS, juyi adireshin shafin da ke nuna alamar xml.
  • Sannan lalle ne ka bi bayanai a kan yadda za ka dora hanyar Samar da Labarai ta RSS zuwa Makaranciyar Labaran RSS dinka ta musamman domin ka iya karawa da wannan Hanyar Labaran ta RSS a cikin jerin wadanda ka yi rajistar samu, Da wasu manhajojin karatun labaran na RSS za ka iya dora adireshin a cikin “Add New Channel, za ta kuma nuna kanun labarai, da takaitattunsu da aka sabunta, da kuma mahada zuwa ga cikakkun labaran.

LURA: Mafiya Sabunta na Manhajojin karatun Labarai za su lurar da kai a kan cewa za ka iya rajistar neman samun Hanyar Samar da Labarai ta RSS a lokacin da kake kallon shafin.

Ko ta yaya zan iya samun Hanyar Samun Labarai ta RSS?

Akwai Manhajojin karatun Labarai na RSS iri daban-daban. Za ka iya ganin cikakken bayanin hakan ta hanyar bincikawa a intanet. Galibi za ka iya debo su kyauta.

Manhajojin karatun Labarai na RSS suna aiki ne ta hanya daban-daban, ya kamata ka san haka a lokacin da kake yin zabin naka.

Haka kuma, yana da muhimmanci ka san cewa wasu Manhajojin karatun Labaran na RSS ba sa iya nuna bayanai a cikin wasu harsunan.

Sharudda da ka’idoji

Duk wani iko, ciki har da na mallaka, na abin da ke cikin shafukan BBC na intanet, mallaka ne na BBC, ita ce kuma ke iko da su bisa wadannan dalilai.

Bisa shiga shafukan intanet na BBC da ka yi, ka amince ke nan cewa za ka iya sauko da abin da ke ciki ne kawai don amfanin kanka ba don wata harka ta kasuwanci ba.

Ba a ba ka iznin juya ba, ko watsawa ta kafar labarai, ko diba, ko adanawa (ta kowace hanya) ko nunawa ga jama’a, ko datarwa da wani abu, ko sauyawa ta kowace irin hanya, na shi abin da ke cikin wadannan shafuna na BBC, don kowace irin bukata, sai da izni a rubuce na BBC.