Hanyoyin saukaka amfani da shafi

Hanyoyin saukaka amfani da shafi

Shafin intanet na BBC Hausa ya kunshi amfani da wasu hanyoyi na kwarewa, irin wadanda W3C ( www.w3.org) ke kokarin yadawa domin bayar da damar amfani da bayanan da muke wallafawa a shafinmu, ga wadanda suke amfani da bayanai ta wasu fasahohi kamar fasahar da ke karanto rubutu a shafin intanet da sauransu.

Daya daga cikin wadannan hanyoyi ita ce amfani da abin da ake kira semantic markup wato wani yanayin rubutu da naurori ke karantawa a intanet, wadda kuma ke saukaka wa shafukan matambayi- ba- ya-bata wajen tattara bayanai.

Muna kuma samar da bayani ta hanyar RSS (RSS real simple syndication) muna amfani da ATOM ( http://en.wikipedia.org/wiki/Atom_(standard)) wanda za a iya gane shi da alama mai ruwan goro da za a samu a dukkan sassan shafin.

Mai rubutu zalla: muna baiwa masu ziyarar shafinmu damar ganin shafin cikin sauki wanda ya kunshi muhimman labarai na kowanne sashe. Za ka iya samun gurbin shiga shafi mai rubutu zalla a saman shafi.

Muna kuma shaida muku cewa, idan kuna bukata, za ku iya sauya girman rubutu da launin shafin ta hanyoyin sauye sauyen yanayin shafi na brawsar ku.

Za ku iya samun karin bayani a kan hanyoyin saukaka amfani da shafin a sashen turanci na BBC. Sai ku ziyarci http://www.bbc.co.uk/accessibility/