Farashi

Nawa zan kashe wajen kallo ko sauraren sauti a wayar salula?

BBC ba ta cajin kudi domin kallo ko sauraren bidiyo ko sauti a shafinta. Sai dai kamfanin da ya samar maka da layin wayar salula zai iya cajar ka kudin adadin bayanai da ka sauko da su daga intanet.

Idan baka da tabbas kan yawan kudaden da za a caje ka dan yin amfani da yanar sadarwa a wayar salularka, tuntubi wadanda suka samar maka da layin waya.

BBC ba ta da alhaki a kan duk wasu kudade da aka caje ka, sakamakon sauko da sauti ko bidiyo daga shafinta.

Ta yaya za a rage yawan kudin da ake caji

  • Sayi ‘dunkullallen tsari’ ko ‘pakitin shafukan yanar sadarwa’ wanda za a iya biya duk wata domin samun caji mai sauki wajen shiga yanar sadarwa.
  • Yi amfani da intanet da ake samu kyauta wato Wi-Fi