Mitocinmu da sauko da sautin labarai

Mitocin Da Muke Watsa Shirye-Shiryenmu

Sashen Hausa na BBC yana watsa shirye-shirye guda hudu a kowacce rana, na tsawon minti talatin-talatin a harshen Hausa. Akwai shirin Safe, akwai shirin Hantsi, akwai shirin Rana, sannan kuma akwai shirin Dare, dukkaninsu a lokutta kamar haka. A gajeren zango.

Lokaci a agogon GMT Mitocin da muke watsa shirye-shirye

Ga masu saurare a jumhuriyar Niger, ana iya kama shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC kai tsaye a gidan radiyon R-et-M, a kan zangon FM 104.5MHz a birnin Niamey.

Sannan akan kama wadannan shirye-shirye a gidan Radio Anfani a kan zango 100Mhz a Damagaram da Maradi.