Yadda karfin makaman Falasdinu da Isra'ila ya ke

Roka a sararin samaniyar Isra'ila
Bayanan hoto,

Koda yake ba wasu makaman zamani ne sosai ba, rokokin Falasdinawa na barazana ga Isra'ilawa da dama

Jiragen saman Isra'ila da bangaren jiragen ruwan ta na iya kai hare-hare kan ko ina a zirin Gaza a duk lokacin da suka so.

Idan da Isra'ila za ta kai kutse da sojinta ta kasa a zirin Gaza - abinda bangarorin biyu za su so su kaucewa- to a nan ma Isra'ila ce ta fi karfi.

Kazalika fadan da ke tsakanin bangarorin biyu ya da da jefa Isra'ilawan da ke zaune a kudancin kasar cikin wani mawuyacin yanayi saboda rokokin da Falasdinawa ke harbawa a kansu.

Sai dai ba lallai bane Rokokin da Falasdinawan ke harba wa suna da karfin gaske ko suna fada wa a wuraren da aka nufe su da su fada.

Amma duk da haka, suna da matukar hadari, kamar yadda harin da aka kai kan wani gini da ke Kiryat Malachi ke nunawa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3.

Garuruwa da Biranen Isra'Ila dake kudancin Tel Aviv na fuskantar barazanar isar Rokokin wurin da suke zaune. Daruruwan 'yan Isra'Ila ne ke cikin fargaba, abinda ya sanya gwamnatocin kasar kai kawo wajen magance wannan yanayi da al'ummar su ke ciki.

Rokokin Falasdinu dai na da dimbin yawa wanda a hankali suke kara karfin su. Da dama daga cikin makamai masu cin gajeren zango kamar makamin Qassam- wanda suna ne na wani dangin- ana kera su ne a yankin zirin Gazan. Kuma suna cin zangon da ya kai kimanin kilomita goma sha biyu.

Makamai masu linzami samfurin Grad wanda ake kyautata zaton kasar Iran ce ke samar da su, na iya cimma wuri mai nisa da ya kai kilomita 20, ta yiwu wasu da aka inganta su ci zango fiye da haka.

Bayanan hoto,

Dubun dubatar Isra'ilawa na zaune a wuraren da rokokin za su iya kaiwa

An kuma taba amfani da makamin roka na China wato WS-1E, wanda shi kuma ke cimma nisan kilomita 40.

Babban makamin da Falasdinawa ke amfani da shi wajen kaiwa Isra'Ila hari shi ne Fajr-5 wanda ke cimma nisan zangon kilomita 75. Wannan makamin zai iya kaiwa farfajiyar garin Tel Aviv, birni mafi girma a Isra'ila.

Isra'ila tana kai hare-hare a kan rumbun adana wadannan makaman.

Mai magana da yawun sojin Isra'ila ya tabbatar da cewa suna samun nasara wajen lalata makaman.

Sai dai akwai rahoton da ke nuna cewa, an harba akalla makamin Fajr daya a hare-haren bayan nan.

Isra'ila na mayar da martani ta hanyar kai hari da kuma kare kanta.

Sabon tsarinta na kariya daga makamai masu linzami mai suna Iron Dome na taimaka wa wajen kare hare-haren makamai masu linzami na Falasdinawa.

Tsarin na gano makaman da aka harbo, da inda za su iya fada wa sannan su harba kariya don kakkabo makaman da ka iya fadawa inda jama'a suke.

Da alama Iron Dome na aiki wajen samar wa Isra'ila kariya, sai dai babu wata kariya da ke iya nasara dari bisa dari.