Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Jinyar jami'an gwamnati a kasashen ketare

A shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon mun tattauna ne akan shawarar da gwamnatin Nigeria ta yanke cewa daga yanzu matukar ana iya yi wa jami'anta da iyalansu magani a cikin kasar, to ba za ta sake kashe kudade wajen kai su kasashen waje ba.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin ne, domin ta samu sukunin inganta asibitoci, ta yadda jama`ar kasar za su iya tsaya wa a gida domin a yi masu magani, ba wai sai sun fita waje ba.

Bincike ya nuna cewa akwai jihohin Najeriya da tuni suka dauki irin wannan mataki, kamar Jihar Rivers kenan a farkon wannan shekarar.

A kwanakin baya, an ambaci Gwamna Amaechi na jihar, yana bayyana cewar, a bara kadai gwamnatinsa ta kashe naira miliyan dubu daya, da miliyan dari biyar, kudaden da ya ce za a iya amfani da su wajen gina asibitoci akalla uku.

Babbar tambaya a nan ita ce: shin me ya sa gwamnatin ta dauki wannan matakin a yanzu? Kuma ko yin hakan zai sa a inganta asibitocin Najeriyar, kamar yadda gwamnatin ke ikirari? Shin wane hali ne asibitocin a Nijeriyar suke ciki?