Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tasirin zaben Burtaniya kan kasashen Afrika

Yanzu haka dai Shugabanni biyu daga cikin manya-manyan Jam''iyyun Burtaniya uku, wato Jam'iyar Conservatives da kuma Liberal Democrat na tattaunawa domin duba yuwuwar ko za su iya kafa wata Gwamnatin kawance.

Hakan dai na zuwa ne ganin yadda jam'iyyar Conservative da ke kan gaba ta kasa samun yawan kuri'un da ake bukata ba, domin samun cikakken rinjaye. Shugaban Conservatives, David Cameron, yayi wata ganawa da shugaban jam'iyar Liberal Democrat, Nick Clegg.

To wai wane irin tasiri wannan zabe na Birtaniya wadda a baya ta mulki kasashen Afrika da dama zai yi ga kasashen na Afrika? Wane irin darasi ne kuma kasashen na Afrika irinsu Najeriya za su iya koya daga wannan zabe?

A zaben da Najeriya ta gudanar a baya dai, ta sha suka daga bangarori da dama abisa yadda aka gudanar da zaben, abinda yasa mahukunta suka sha alwashin kawo sauyi a fannin zaben.