Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sauya shugaban hukumar zaben Najeriya

Mun fara gabatar da shirin mu na musamman na Ra'ayi Riga, dan ku masu sauraro, inda zaku dinga bayyana ra'ayoyin ku kan abubuwan da suka shafi rayuwar ku. Batun zabe a Nigeria dai abu ne mai mahimmancin gaske, kuma jama'ar kasar na ci gaba da nemo duk wata hanya da za ta tabbatar da ingattacciyar demokaradiyya.

Kamar dai yadda watakila ku ka sani, Majalisun dokokin Nigeria na yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyara musamman bangaren harkokin zabe.

A shirinmu na farko mun tattauna ne kan daya daga cikin kudirorin da majalisar Dattawan Nijeriar ta amince da su a kwanakin baya, wanda ke cewa wajibi ne, sai mutum yana da ilimin gaba da sakandare, ko digri, zai iya tsayawa takarar kujerar Majalisar dokokin jihohi da tarayyar, da mukaman gwamna, shugaban kasa da mataimakinsa.

Ra'ayi Riga

Bakin da suka tofa albarkacin bakinsu a shirin sun hadar da Dr. Junaidu Muhammad da kuma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.

Dimbin Masu sauraro sun aiko da ra'ayoyinsu da kuma wasu da aka yi magana da su ta wayar tarho.

Masu sauraro kuma sun ci gaba da muhawara a dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawa, wato BBCHausa Facebook.