An sabunta: 7 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 13:08 GMT

Asusun hadin gwiwa: Dacewa ko rashin ta?

Taswirar Najeriya

An dade ana cece kuce kan yadda ake tafiyar da asusun kananan hukumomi a Najeriya

A Nijeriya, daya daga cikin batutuwan dake janyo kace nace shi ne tanajin tsarin mulkin kasar na baiwa kananan hukumomi kudadensu ta hanyar asusun hadin gwiwa tare da gwamnatocin jihohi.

Yayinda wasu ke cewa hakan na takura kananan hukumomi wajen gudanar da ayyukansu, wasu na cewar matakin ne ke tabbatar da ana sa ido kan yadda suke kashe kudade.

Shin ko ya dace kananan hukumomin su rika karbar kudadensu kai tsaye daga kwamitin rabon arzikin kasa na tarayya, ko kuwa a ci gaba da wannan tsari?

Za ku iya bayyana ra'ayinku a kan wannan batu a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

To Domin shiga cikin shirin, Sai ku tuntube mu ko dai ta email a hausa@bbc.co.uk, ko kuma ta wayar salula a kan wannan lamba: 44 77 86 20 20 09.

Ko kuma ta dandalin mu na muhawara BBCHAUSA Facebook, a shafinmu na Internet, a BBCHausa.com.

Har ila yau za ku iya bayyana ra'ayinku ta hanyar cike wannan sashi.

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.