An sabunta: 13 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 21:07 GMT

Kaidojin sabunta rajistar zabe a jamhuriyar Nijar, sun dace?

Allon da ke nuna hanyar zuwa Yamai

A jamhuriyar Nijar, ana aikin sabunta rajistar masu zabe, a shirye shiryen mayar da kasar turbar dimokradiyya.

Sai dai yayinda ake wannan aiki, wasu na korafi kan ka'idojin yin rajistar.

Sharuddan yin rajistar sun hada da mallakar paspo, da katin shaidar zama dan kasa, da lasisin tukin mota a matsayin shaidun da mutum zai nuna kafin a yi masa rajista.

Korafin da wasu ke yi shi ne cewar matakin zai hana wa galibin mazauna karkara dake amfani da takardar shaidar haihuwa, yin rajista.

Wadannan da ma wasu ka'idojin da suka shafi tsayawa takarar zabe a Nijar din, na daga cikin abubuwan da zamu tattauna a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako.

Sai ku aiko mana da lambar waya da takaitaccen ra'ayi ta e-mail a hausa@bbc.co.uk, ko ta lambar wayar nan da aka saba wato 447786202009, ko kuma ta dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawara, wato BBC Hausa Facebook.

Za kuma ku iya aiko mana da ra'ayinku ta gurbin da ke kasa:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.