Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ko akwai yunwa a Najeriya?

Tuni dai wasu jihohin arewacin Najeriya suka soma taimaka wa yara da abinci mai gina jiki saboda karancin abincin da wasu jama'a ke fama da shi a jihohin.

To shin hakan na nufin akwai yunwa ke nan a wasu sassan Najeriya?

A karamar hukumar Gada da ke jihar Sokoto, kimanin yara goma sha biyu ne suka rasa rayukansu saboda matsalar tamowa ko yunwa.

Wannan matsala ce ta sanya Asusun Kula da Kananan Yara na Majlisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya kafa wata cibiyar sha-ka-tafi don kulawa da irin wadannan yara.

Haka kuma an fara baiwa yara tallafin abinci mai gina jiki a jahar Jigawa saboda karancin abincin.

Jihohin dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriyar da suka yi iyaka da jumhuriyyar Nijar, wadda kuma a halin yanzu take fama da matsalar karancin abinci da ma yunwa a wasu sassan kasar.

Yanzu haka dai mutane kusan miliyan takwas ne a Nijar din ke fuskantar barazanar yunwa.

To ganin cewa yanayin damuna da na noma a wannan yanki sun yi kamanni da juna, ko hakan na nufin akwai matslar karancin abinci a wasu johohin arewacin Najeriyar musamman masu makwabtaka da Jamhuriyar ta Nijar?

A kwanakin baya ne dai Hukumar Samar da Abinci ta, FAO, ta yi gargadin cewar kasashen yankin Sahel, wato na kudu kadan ga sahara, za su fuskanci matsalar karancin abinci.

To ko yunwa ta kai wadannan yankunan na Najeriya, ganin cewa tana cikin wannan yankin, sannan kuma ga karancin abincin a wasu jihohin kasar?

Wannan shi ne batun da muka tattauna a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.