Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rawar da mata ke takawa a fagen siyasa

Image caption Ana lakanta koma bayan da mata ke fuskanta da rashin cikakken ilimi kan wasunsu

Shekaru goma sha biyar da suka wuce ne, babban taron Mata da aka gudanar a kasar China, ya amince da yarjejeniyar ware akalla kashi talatin cikin dari na mukamai ga mata, musamman ma dai mukaman da akan zaba kamar kujerun majalisun dokoki.

Sai dai kawo ya zuwa yanzu, kididdigar da Kungiyar Majalisun dokoki ta kasashen duniya ta fitar a cikin watan Yuni, na nuni da cewar a fadin duniya baki daya, mata na da kashi goma sha tara ne kacal cikin dari na jumlar kujerun majalisun dokoki, watau kasa kenan da yarjejeniyar da aka kulla ta birnin Beijing.

Kuma koda a nahiyoyin da ake ganin harkokin siyasarsu sun samu ci gaba matuka, kasashe kalilan ne za su bugi kirji, su ce sun cika wannan alkawari.

A Kasashen Afrika akwai kasashe kamarsu Rwanda da Burundi da Tanzania da Swaziland da Africa ta kudu da Angola da suka cika wannan alkawari, to amma ga saura kuwa, kamar su Najeriya, da Kamaru da Chadi, akwai sauran jan aiki, ballatana kuma Niger, inda a yanzu mulki ne irin na soji.

To shin ko me ke kawo cikas ga Mata wajen shiga harkokin siyasa, musamman a kasashenmu na Africa? Kuma wace hanya za a bi domin kara yawan matan, yadda zas u iya bayar da tasu gudunmawar wajen ci gaban kasa?

Wannan shi ne abun da zamu tattauna a yau tare da ku masu saurarenmu a cikin shirin namu na wannan makon.