Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tabarbarewar ilmin sakandare a Najeriya

Image caption Batun ilmin yara na fuskantar matsaloli a kasashe masu tasowa

Filin Ra'ayi riga na wannan makon ya mayar da hankali ne kan sakamakon jarrabawar da hukumar shirya jarrabawa ta Afrika ta yamma wato WAEC ta fitar kan wadanda suka rubuta jarraabawar gama sakandire domin neman shiga jami'a.

Sakamakon ya nuna cewa kashi 75 cikin dari na wadanda suka rubuta wannan jarrabawa dai ba su samu sakamako mafi kankanta da ake bukata don shiga jami'a ba. Wato akalla samun nasara a kan maudu'i biyar, ciki kuwa har da lissafi da kuma turanci.

Babban abun damuwar shi ne cewar daliban ba su tabuka abun a zo a ganin koda a darussan da ba su shafi lissafi da turancin ba ma. Abin tambaya a nan shi ne me hakan ke nufi ga makomar ilmi, kuma ina mafita?

Domin gabatar da shirin, mun gayyato baki da suka hadar da, Farfesa Haruna Wakili, kwamishinan ilmi na Jihar Jigawa da kuma Dr Aliyu Tilde, mai yin sharhi kan al'amuran yau da kulum kuma tsohon Darakatan makarantu na musamman a Jihar Bauchi.

Mun tattauna da wasu daga cikin dimbin masu sararen mu ta wayar salula, wadanda su ma suka bayyana ra'ayoyinsu.