An sabunta: 16 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 16:40 GMT

Ra'ayi Riga: Tabarbarewar harkar tsaro a Najeriya

'Yan sandan Najeriya na bincike

A Najeriya, rashin tsaro na daga cikin abubuwan da suka addabi jama'a.

A farko wannan makon dai a Kano aka yanka wasu mutane guda 'yan gida daya. Sai kuma bindige wani jami'in hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

Baya ga haka akwai lamarin garkuwa da jama'a da fashi da makami da makamantansu.

To shin me ke janyi wadannan matsaloli.? Ta ya ya kuma za'a magance su.?

Abin kenan da zamu tattauna a filin mu na ra'ayi riga na wannan makon.

Domin shiga shirin sai ku aiko mana da ra'ayinku a takaice da kuma lambar wayarku a adireshinmu ta e-mail wato hausa@bbc.co.uk, ko kuma ta lambar wayar da aka saba wato 44 77 86 20 20 09 ko kuma ta dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawara wato BBC Hausa Facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na intanet, wato BBC Hausa.com.

Zaku iya tuntuban mu ta wannan shafin.

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.