Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Cikar Najeriya shekaru 50 da samun 'yancin kai

Image caption An gudanar da kade-kade da raye-raye domin murnar wannar rana

A ranar 1 ga watan Oktoban 1960 ne Najeriya ta cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallakar Burtaniya.

A yayin da ake gudanar da bukukuwa a wannan rana, an sami hasarar rayuka a wasu hare-haren da aka kai a Abuja, babban birnin Tarayyar kasar.

Amma duk da haka an gudanar da shagulgulan a Abuja da kuma sauran sassa dabam-dabam na kasar, domin murnar wannan ranar.

Ra'ayoyin jama'a dai ya bambanta, akan irin nasarorin da Najeriyar ta samu a tsawon wadannan shekarun.

Kungiyar nan mai fafutukar kwato wa mutanen yankin Niger-Delta mai arzikin Man Petur hakkokinsu, ta MEND, ta yi gargadin kai wannan hari, tana mai cewar bata ga wani abun yin bukukuwa ba a wanann lokaci.

Domin tattaunawa kan wannan lamari, muna tare da Alhaji Yusuf Maitama Sule, Dan Masanin Kano, Kuma minista a Jamhuriyar ta farko karkashin jagorancin Priyi Minista, marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa.

Da kuma Alhaji Adamu Chiroma, tsohon gwamnan babban bankin Nigeria, tsohon ministan harkokin kudi, da kuma Minista mai ci yanzu a ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya, Dr Aliyu Idi Hong, Sai kuma Professor Sa'ad Abubakar, wani masanin tarihi da ke Jami'ar Abuja.

Akwai kuma ku masu sauraro, ta wayar tarho da kuma Facebook da kuma sakonni ta wayar salula.