Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalolin wasan kwallon kafa a Nigeria

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya, watau FIFA ta ce ta jingine dakatarwar da ta yiwa Nigeria har nan zuwa wani lokaci, saboda ta ga alamun an fara aiwatar da sauye-sauyen da ta ke bukata.

Wannan mataki zai baiwa Nigeriya damar karawa da kasar Guinea, a wasan kwallon kafa na share fagen gasar cin kofin nahiyar Afrika da zaa yi ranar lahadi.

Hukumar FIFA ta dakatar da Nigeria'r ne daga cikin kungiyar a wannan makon bayan da ta yi zargin gwamnatin Nigeria na yin katsalandam a harkokin wasannin kwallon kafa.

Zargin da hukumar FIFA ta yi ya hada da batun karar da aka shigar a gaban kotu akan zababbun shugabannin hukumar, abun da sam ya hana su gudanar da aikace aikacensu.

Tuni dai aka janye wannan kara aka kuma mayar da Sakatare Janar na riko kan mukaminsa.

Shin wadanne irin matsaloli ne suka dabaibaye fagen kwallon kafa a Najeriyar, har suke kai ga hukumar kwallon kafa ta duniyar na dauka ko kuma yin barazanar daukar matakan dakatarwar? Yaya kuma za a shawo kansu?

Wadannan su ne wasu daga cikin batutuwan da muka tattauna a kansu a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.