Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yiwuwar kawar da zazzabin cizon sauro nan da shekaru 5?

Image caption Rashin samun kulawa na daga cikin abubuwan da ke haddasa cutar

Zazzabin cizon sauro, kamar yadda alkalumma suka nuna, yana hallaka akalla mutane miliyan guda - zuwa miliyan uku a kowace shekara, galibi a kasashen Afirka.

Rashin tsabtar muhalli, inda sauro ke samun wurin kyankyasa, shine ummul khaba'isun da ke rura wutar matsalar.

Shin yaya wannan matsala ta ke a yankunanku? Kuma a ganinku, ko za a iya takawa wannan cuta birki, nan da shekaru biyar masu zuwa, kamar yadda aka zayyana a muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya?

Wadannan na daga cikin matsalolin da muka tattaunawa tare da ku masu sauraro a filin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

To domin tattaunawa akan batun, mun gayyato Dr Muhammad Sadiq, babban jami'in hukumar Lafiya ta duniya, WHO wanda ke kula da yaki da cutar zazzabin cizon sauro a sashen arewa maso yammacin Najeriya.

A kwai kuma Dr Mansur Kabir, babban jami'i a ma'aikatar kula da lafiya ta tarayya a Najeriya, da kuma masu sauraro ta wayar salula.