Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Samun zuriya ta gari

Image caption Haihuwa ita ce tushen rayuwar al'umma

Tasirin haihuwa ga ci gaban al'umma abu ne wanda baya misaltuwa domin yankewa ko karancin yara masu tasowa kan haifar da illa na tsawon lokaci ga al'umma, kamar yadda lamarin yake a wasu kasashen duniya wadanda alkaluma ke nuna tsofaffi na fin matasa yawa.

Wani nazari da sashen dake gudanar da bincike kan tsofaffi a Afrika na hukumar lafiya ta duniya WHO yayi, ya nuna cewa yawan mutanen dake da shekaru sittin zuwa sama za su karu a Najeriya zuwa sama da miliyan talatin nan da shekarun 2050, wanda hakan ke nufin mutum daya cikin kowadanne mutane takwas a kasar. Kuma yawan shekarunsu zai kama daga 60 zuwa 69.

A takaice dai rashin haihuwa a tsakanin al'umma idan har ya kai wani mataki, ka iya shafar ci gaban wannan al'umma ta kowacce fuska.

Kuma daya daga cikin hanyoyin kaucewa yawan tsofaffi a al'umma ita ce samun al'umma masu tasowa ta hanyar rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da kuma jariransu.

Hakan zai samu ta hanyar samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya musamman ma a nahiyar Afrika da ta fi kowace nahiya yawan mace-macen mata masu juna biyu.

A cikin shirin mun tattauna da Dr Mairo Mandara, domin jin yadda yanayin mata ke sauyawa idan suka fara laulayi, kuma mun tsarma muku bayanai daga mata masu juna biyu don kun san an ce waka abakin mai ita tafi dadi.