Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Al'adun gargajiya ga mai ciki

Image caption Wata mata na tattaunawa da wakiliyar BBC Habiba Adamu

Daya daga cikin abubuwan da muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya na rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da kashi uku cikin hudu nan da shekarar 2015 ke naman cimma wa, shi ne samar da tsarin kiwon lafiya ingantacce ga mata masu juna biyu a fadin duniya.

A cewar wani mizanin dake nuna yawan haihuwa a duniya na hukumar leken asiri ta Amurka na shekarar 2010, jamhuriyyar Nijar ita ce kasar da ta fi kowacce a duniya samun haihuwa, inda a kasar cikin kowane mutane 1000 ake samun haihuwa sama da 50.

Sai dai kuma kasar na daga cikin kasashen da su ka fi talauci a duniya.

Hakan ya sa al'ummar kasar da mafi yawansu ke zaune a yankunan karkara dogara a wasu lokutan da al'adu da magungunan gargajiya wajen kula da lafiyarsu ciki har ma da mata masu juna biyu.

A makociyarta Najeriya kuwa, kamar yadda mizanin ya nuna, kasar na samun haihuwa kusan 37 cikin kowane mutum dubu daya.

Najeriyar ita ce kasa ta 28 a duniya wajen samun haihuwa.

Amma duk da dimbin arzikin da Allah ya yiwa kasar, miliyoyin jama'a ne ke cikin kangin talauci, musamman a Arewacin kasar, abinda ya taimaka gaya wajen dogara da wasu al'adu don warware matsalolin kiwon lafiyar mata masu juna biyu.

Mizanin ya kuma nuna cewa, kasashen da suka ci gaba kuma a daya bangaren sun fi karancin haihuwa kamar Burtaniya dake samun haihuwa sama da goma cikin kowane mutane 1000.

Abin lura a nan dai shi ne a kasashen da suka ci gaba hukumomi sun fi samar da tsarin kiwon lafiya ingantacce ga al'umominsu duk kuwa da cewa suna samun karancin haihuwar.

Sai dai rashin ingantacciyar harkar lafiya a kasashe masu tasowa, ya sa jama'a yin amfani da wasu al'adu na gargajiya wajen samawa kansu magani ciki kuwa har da mata masu juna biyu.

Shirin Haifi Kiyaye da BBC Hausa ya duba illoli ko akasin haka na wasu al'adun gargajiya da wasu camfe-camfe da ake yi game da renon ciki a Najeriya da Nijar.