Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga : Makomar Kwalejojin horar da malamai a Najeriya

Image caption An dade ana cece-kuce kan kwalejojin horas da malamai a Najeriya

Ma'aikatar harkokin ilimi ta Najeriya ta ce a kokarin da ta ke yi na inganta harkokin ilimi a kasar, ta na yin nazari a kan wasu hanyoyi na yin garanbawul ga Makarantun horas da Malamai na Kasa.

A yanzu haka dai akwai irin wadannan makarantu akalla ashirin da daya wadanda ke karkashin ikon gwamnatin tarayyar.

Daga cikin shawarwarin da gwamnatin ke tattaunawa akai, akwai yiwuwar soke irin wadannan makarantu baki daya, ko kuma kara martabarsu yadda za su dunga bayar da digiri, a madadin takardar shaidar Malanta watau NCE, ko kuma a mayar da su kwalejojin Fasaha.

Wani al'amari da ke ciwa mutane da dama tuwo a kwarya a kasar dai, shi ne batun tabarbarewar harkokin ilimi, inda ala'amarin a yanzu yasa mutane da dama ke tura 'ya 'yansu zuwa kasashen waje domin samun ilimi mai inganci, duk kuwa da irin dumbin asarar da hakan ke haddasawa ga Najeriya.

Wata babbar matsala da mutane da dama ke ganin ta haifar da irin wannan al'amari shi ne irin rikon sakainar kashin da wasu gwamnatocin baya a Najeriya suka yiwa harkar ilimi, musamman ma a lokacin mulkin soji.

Abun da ya sa mutane da dama suka kauracewa aikin Malanta. Wannan al'amari ya haifar da karancin kwararrun malamai, musamman a makarantun Piramare inda nan ne tushe.

Daga cikin sauye-sauyen da aka yi a 'yan shekarun baya domin tabbatar da samun kwararrun Malamai a irin wadannan makarantu, shi ne na tabbattar da cewa duk wanda zai koyar, yana da akalla takardar shaidar cancanta zama Malamin Makaranta watau NCE.

To sai dai menene ra'ayinku ku masu saurare akan wannan al'amari. Wannan shi ne abin da shirin mu na yau ya mayar da hankali akai?