Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Mahimmancin zuwa awo

Image caption Awo na kare lafiyar mata masu juna biyu

A wani sabon rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar a watan Satumbar, 2010 da hadin guiwar asusun tallafawa yara na majlisar dinkin duniya UNICEF da hukumar kula da al'umma ta majlisar UNFPA da kuma babban bankin duniya, rahoton ya kiyasta cewa a shekarar 2008 kadai an sami mutuwar mata masu juna biyu dubu dari 358 a fadin duniya, kuma abin yafi kamari a kasashen masu tasowa, inda kasashen Afrika na kudu da Sahara ke da kaso mafi tsoka.

Haka kuma rahoton ya bayyana wasu kasashe goma sha daya a matsayin kasashen da aka samu kashi 65 cikin dari na adadin yawan mata masu juna biyun da suka mutu a fadin duniya a shekarar ta 2008.

Na farko daga cikin kasashen dai itace kasar India, inda mata dubu 63 suka mutu, sai Najeriya dake biye da ita, wanda kuma mata masu juna biyu dubu hamsin ne suka riga mu gidan gaskiya a shekarar ta 2008.

Mai bi wa Najeriya a cewar rahoton itace jamhuriyyar Democradiyyar Congo, inda mata masu juna biyu dubu 19 suka mutu, Sai Afghanistan inda mata masu juna biyu dubu 18 suka rasu.

Sau ran kasashen dai sun hada da kasar Habasha, Pakistan, Tanzaniya, Bangladash, indonesia, Sudan da kuma Kenya.

Yayinda a daya bangaren kuma kasashe Ashirin da bakwai wadanda suka hada da kasashen da ma'aikata ke samun albashi matsakaici da kuma kasashen da ma'aikatansu ke daukar albashi mai tsoka, mata biyar ko kasa da hakan ne suka mutu a wannan shekarar.

Idan kuma aka dubi kasashen dake da matsanancin yawaitar mace macen mata masu juna biyu wato mutuwar mata masu juna biyu dubu daya cikin kowacce haihuwa dubu dari, a cewar rahoton kasashe hudu ne sukayi zarra, kuma su ne kasar Afghanistan, Sai Chadi, sai Guinue Bissau da kuma Somaliya.

Sannan cikin kasashen Afrika ta kudu da Sahara goma da ke da yawaitar mace-macen mata Najeriya itace kasa ta takwas kuma jamhuriyyar Nijar ta zama kasa mafi karancin mace-macen mata masu juna biyu, inda mata 820 ke mutuwa cikin kowace haihuwa dubu dari.

Rahoton dai ya kuma bayyana cewa mata masu juna biyu na cigaba da mutuwa ne saboda wasu manyan dalilai hudu da suka kunshi zubbar da jini bayan haihuwa, kamuwa da kwayoyin cuta, cututtuka da suka shafi hawan jini da kuma zub da ciki.

Sai dai wannan sabon kididdigan yace akwai yiwuwar kiyaye mutuwara mata yayinda suke da juna biyu.

Akai bukatar kasashe su sanya kudade a harkar tsarin kiwon lafiya tare da nuna daidaito wajen kula da lafiyar al'umma.

To idan muka dubi wadannan manyan dalilai dake ci gaba da janyo mutuwar mata masu juna biyu a kasashenmu, masana a fannin kiwon lafiya na ganin dalilai ne da za'a iya kauce musu, musamman idan akwai kyakkyawan tsarin kiwon lafi kuma mata na zuwa awo don gano matsaloli kiwon lafiya tun ba su riga sun faskara ba sun kaiga daukar ran mace ko na jaririn da take dauke da shi.

A yi sauraro lafiya.