Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Takaddama kan wakilci a jam'iyyun Najeriya

Image caption Wannan batu dai ya raba tsakanin 'yan siyasar Najeriya

Rahotannni daga Nijeriya na nuna cewa Majalisar wakilai ta kasa ta mika wuya game da sukar da ake ma ta, inda ta amince da dokar zabe ta shekara ta 2010 da aka yi wa kwaskwarima, ba tare da sashen nan dake janyo kace nace ba.

A makon jiya ne dai majalisar wakilan ta fara amincewa da gyaran da aka yi wa dokar zaben, kuma cikin batutuwan da suka janyo suka, akwai wanda ya tanaji mayar da 'yan Majalisar su kasance wakilai a kwamitin zartarwa na kasa a jam'iyyunsu.

Da kuma batun tsarin zaben fitar da-gwani na jam'iyyu da kuma na wakiland a za su halarci babban zabe na jam'iyyunsu domin fid-da-gwani.

Tun a shekaranjiya ne, majalisar dattawa ta amince da dokar, inda ta yi watsi da sashen da yayi wadannan tanade-tanade.

To shin tun farko wadannan dalilai suka sa 'yan Majalisar bullo da wadancan sauye- sauye, kuma me ya sa a yanzu 'yan Majalisar sauya matsayi?

Domin tattaunawa kan wannan batu, baya ga masu saurare dake kan layi, mun gayyato wasu baki da suka hada da Sanata Abubakar Sodangi, da Hon Musa Sarkin Adar, shugaban kwamitin harkokin zabe na majalisar wakilai ta tarayya.

Akwai kuma kakakin Majalisar dokokin jihar Sakkwato Hon Abdullahi Balarabe Salaame, da kuma Alhaji Salisu Dabo, mataimaki na musamman kan harkokin siyasa ga mataimakin shugaban Nijeriya.