Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsin tattalin arziki ya shafi bikin kirsimeti

Ashirin da biyar ga wannan wata na Disamba - Krista a sassa dabam-dabam na duniya ke shagulgulan Krismati, domin tunawa da haihuwar Yesu Kristi, ko Annabi Isa Alaihi Salam, jagoran addinin Kristan.

A wannan lokacin mabiya addinin Kristan kan gudanar da addu'o'i, da ziyartar 'yan uwa da abokan arziki, da kuma rarraba kyauta ga jama'a.

Sai dai za a yi Krismatin ce ko Noel a wani mawuyacin hali na matsin tattalin arziki, wanda hakan ya sa da yawa ba za su iya yin irin abubuwan da suka saba ba.

Abun da aka tattauna kenan a shirin ra'ayi riga na wannan makon.