Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rikicin siyasar Cote d'Ivoire

Image caption Akwai sojojin Majalisar Dinkin Duniya a kasar, amma duk da haka Gbagbo ya ki ya mika wuya

Zaben shugaban kasar da aka yi a Cote d'Ivoire a watan Nuwamban 2010 ya bar baya da kura, bayan da sakamakon zaben ya nuna cewa dan takarar 'Yan adawa Alassane Ouatarra ne ya samu nasara.

Sai dai daga baya kotun tsarin mulki ta kasar ta yanke hukuncin cewa shugaba Laurent Ggabgo ne ya lashe zaben.

A karshe dukkan 'yan takarar biyu dai sun rantsar da kansu a matsayin shugaban kasa.

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afrika Ecowas, ta yi barazanar amfani da karfi idan har Laurent Ggabgo yaki amincewa ya sauka.

To abin tambaya a nan shi ne, me wannan dambarwar siyasa ke nufi ga tafarki mulkin Demokuradiya a nahiyar Afrika, kuma ta yaya za a kaucewa irin wannan sarkakiya?

Domin tattaunawa kan wannan lamari mun gayyato Farfesa Jibo Hamani, masanin tarihi kuma malamai a jami'ar Abbdulmumini Diof a jamhuriyar Nijar.

Akwai kuma Manjo Yahya shinko, masani kan harkokin tsaro kuma mai yin sharhi kan al'amuran yau da kullum a Kaduna Nijeriya

Akwai kuma Dr Aliyu Idi Hong, tsohon ministan kasar a ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya.