Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi kiyaye da BBC Hausa: Wadatar kayan marmari a yankunan mu

A wani rahoto da hukumar abinci ta duniya, WFP ta wallafa a watan satumbar shekarar 2010 ya nuna cewa mutane miliyan 925 ne ke fama da rashin isashshen abinci mai gina jiki a duniya a shekarar data gabata.

Haka kuma kashi 98 cikin dari na wadannan al'umma na zaune a kasashe masu tasowa, inda kashi biyu bisa uku wato kashi 65 cikin dari ke zaune a kasashen Bangladash,China, jamhuriyyar democradiyyar Congo, kasar Habasha, India, indonesia da kuma Pakistan.

A cewar rahoton dai cikin mutane miliyan 925 da sukayi fama da karancin abincin mai gina jiki a bara, kasashen Afrika na kudu da sahara na dauke da mutane miliyan 239, yayinda yankin Asia da Pacific ke da mutane miliyan 578.

A wani rahoto na majalisar tattalin arziki da zamantakewa na majalisar dinkin duniya ko ECOSOC a takaice, na shekarar 2007 ya nuna cewa mata ne fiye da rabin al'umomin duniya, sai dai kuma su ne fiye da kashi sittin cikin dari na mutanen da ke fama da yunwa a duniya.

Matsalar da kusan ke tafe kafad da kafada da yunwa itace ta rashin isasshen abinci mai gina jiki. Kuma mata masu juna biyu ba su tsira daga wannan matsala ba, abinda ma yasa masana a fannin kiwon lafiya ke jaddada muhimmancin cin abinci mai gina jiki don samun lafiyarsu da kuma na jariran dake cikinsu.

Kayan marmari dai na daga cikin abincin da ke bayar da kariya ga jiki wato daya daga cikin kason abinci uku da suka taru suke samar da abinci mai gina jiki, To ko kayan marmarin na da saukin samu a yankunan mu ta yadda mata masu juna biyu za su iya saye? Abun kenan da zamu duba a shirin wananan mako. Sai ayi saurare lafiya.