Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Zaben shugaban kasa a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan zaben ne ake saran zai maida kasar tafarkin dimokradiyya

Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Nijar wani bangare ne na shirin mayar da kasar bisa tafarkin Demokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi bara.

'Yan takara goma ne za su fafata domin dare kujerar shugabancin kasar ta Nijar.

Sannan kujeru 113 ne ake takarar su a Majalisar Dokoki.

Sai dai irin matsalolin da aka fuskanta a zaben kananan hukumomin da aka yi a farkon wannan watan, sun haifar da takaddama.

Inda har wasu daga cikin 'yan takarar suka bukaci da a dage zaben na tsawon makonni 3, to amma gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi watsi da wannan bukata.

Babban fatan masu zabe a wannan karon dai shi ne a kaucewa matsalolin da aka fuskanta, wadanda suka hada da rashin kai kayan aiki zuwa rumfunan zabe kan lokaci.

To baya ga dimbin masu sauraro da ke kan layi suna tofa albarkacin bakinsu, mun kuma gayyato bakin da suka hada da:

Alhaji Doudou Rahama, mamba a kwamitin kolin jam'iyyar CDS-Rahama, wadda a kwanan nan ta kulla kawance da wasu jam'iyyun biyar, wanda ake kira ARN a takaice.

Alhaji Zakari Umaru, mamba a kwamitin koli na jam'iyyar PNDS-Tarayya, kuma dan takarar majalisar dokoki daga jahar Tahoua

Sai kuma Parfesa Djibo Hamani na jami'ar Yamai, kuma mai sharhi kan al'amurran yau da kullum.