Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Zanga-zangar neman sauyi a Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dandalin Tahrir ko kuma na 'yanci shi ne wurin da masu zanga-zangar ke taruwa

An shafe kwanaki da dama kenan, harkoki sun tsaya cik a Kasar Masar, a sakamakon zanga-zangar da jama'a ke yi a kasar ta neman Shugaba Mubarak yayi Murabus.

Wannan guguwar neman sauyi dai ta kada ne bayan irinta da aka samu a Tunisia, inda jama'ar kasar suka tilastawa shugaba Zine Al-Abidine Ben-Ali sauka daga kan karagar mulki.

Tare da tserewa gudun hijira zuwa kasar Saudiyya.

Baya ga kasashen na Tunisia da Masar, akwai alamun an fara irin wannan zanga-zanga a kasashe kamar Yemen da Jordan da Sudan, yayin da ake fargabar al'amarin na iya bazuwa zuwa wasu kasashe na daban.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da irin wannan zanga-zanga ke haifar da juyin juya hali ba.

A shekarar 1979, Jama'ar kasar Iran sun juyawa Shah Mohammad Reza Pahlavi baya, abun da ya kai ga juyin juya halin Islama a karkashin jagorancin Ayatullah Khomeini.

Yayin da a yankin Gabashin Turai kuma irin wannan bore ya kai ga kawo karshen mulkin kwaminisanci a shekarun 1989 zuwa 1990. Yayin da a shekarar 1991, Tarayyar Soviet ta wargaje a sakamakon irin wannan zanga-zanga.

A kasar Ukraine ma an sami irin wannan bore a shekara ta 2004 zuwa 2005, wanda shi ma ya tilasta aka samu sauyin gwamnati.

To amma shin me ke haddasa irin wannan bore ne da ke kaiwa ga juyin-juya hali, kuma wane darasi ne sauran kasashe za su koya daga wannan al'amari?

Domin tattaunawa akan wannan al'amari, mun gayyato Dr Ado Mahamane, Malamin tarihi a Jami'ar Abdulmummuni Diofo da ke birnin Niamey ta wayar tarho. Sai kuma Dr Kole Shettima a ofishinmu na Abuja, Masani akan kimiyyar siyasa kuma Direkta a ofishin Gidauniyar MacArthur da ke Abuja.

Kai tsaye ta wayar tarho daga kasar Masar akwai Malam Nasir S Rufa'i Sokoto, wani dan Jarida, inda kuma a kasar Tunisia muke tare da Malam Moussa Mahamadou Na Gadambo, wanda ke koyarwa a wata Jami'a a kasar ta Tunisia.