Guguwar sauyi a gabas ta tsakiya: Kasa da kasa

Iran

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Iran

Gwamnatin Iran ta kira wani gangami a ranar Juma'a 18 ga watan Fabrairu domin nuna kyamar 'yan adawa a kasar.

Wannan ya biyo bayan zanga-zangar da 'yan adawar su ka gudanar a kasar domin nuna goyon bayan da sauyin gwamnati da aka samu a wasu kasashe da suke makwabtaka da Iran.

Daga baya sai zanga- zangar ta rikide ta koma ta kin jinin gwamnati wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu da kuma raunata wasu da dama.

Iran na da tsarin siyasa mai sarkakkiya da ba'a saba da shi ba inda ta hada gwamnatin shari'ar Musulunci da demokradiyyar zamani.

Akwai wasu hukumomin masu zaman kansu da kuma wadanda jama'a ke zabar su.

Hukumomi a kasar sun hadar da shugaban addinin kasar, da kuma shugaban kasa da 'yan majalisa da jama'a suka zaba.

An zabi shugaba Mahmoud Ahmadinejad ne a shekarar 2005, yana da ra'ayin rikau inda ya sha alwashin kawar da duk wata zanga-zangar kin jinin gwamnati da za'a gudanar a kasar.

Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Libya

An yi artabu tsakanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da kuma masu goyon bayan gwamnati a Libya a ranar 17 ga watan Fabrairu.

Wanda su ka shaida abin da ya faru sun ce dubban mutane ne su ka fito kan tituna a birnin Benghazi domin yi zanga-zanga.

An kashe akalla mutane 24 da ke zanga-zangar kin jinin gwamnati, in ji kungiyoyin kare hakkin bil'adama.

An dai haramta zanga-zanga a Libya, amma zanga-zangar ta kwanan nan ta taso ne bayan an tsare wani lauya wanda ke sukar gwamnati.

Kanel Gaddafi ne shugaban kasa a Afrika da Gabas ta Tsakiya da ya fi dadewa a kan karagar mulki.

Morroco

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Morocco

'Yan adawa a Morocco sun yi gargadin cewa za su kawar da gwamantin kasar matukar ba a kawo sauye-sauye ta fuskar tattalin arziki ba.

Morocco ta dade tana fama da matsalar tattalin arziki. Ta sanar da daukar matakai domin rage hauhawar farashi.

Martabar Morocco ba kara dusashewa bayan da shafin Wikileaks ya bayyana zargin cin hanci da rashawa a tsakanin sarakunan kasar da kuma na kusa da sarki Muhammad na shida.

Sarkin dai ya sha alwashin yaki da talauci, abin da yasa a kai masa lakabi da "garkuwar talakawa". Kuma matakin ya jo zuba jari daga kasashen waje.

Morocco kamar Masar da Algeria, tana bada takaitacciyar damar fadar albarkacin baki, kuma ta iya shawo kan matsalar kawo yanzu. Kamar Jordan, mulkin mulukiya ne amma mai samun goyon bayan wani bangare na jama'a.

Bharain

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Bahrain

Jami'an tsaro a Bahrain sun tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a dandalin Pearl dake tsakiyyar babban birnin kasar Manama.

Daruruwan 'yan sandan kwantar da tarzoma ne suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma kulake domin tarwatsa masu zanga-zangar a ranar Alhamis.

Akkalla mutane uku sun mutu, a yayinda wajen 303 suka samu raunuka.

Bahrain dai na fuskantar tashin hankali ne saboda gabar da ke tsakanin 'yan shi'ar kasar da kuma masu mulki wanda 'yan Al-halul Sunnah ne.

Masu zanga-zangar sun yi korafi kan matsin tattalin arziki da rashin samun cikakken 'yancin shiga harkar siyasa da kuma nuna banbanci da wariya wajen samar da aikin yi.

Tun da Sarki Hamad bin Issa Al Khalifa ya hau mulki a shekarar 1999, ya taimaka matukka wajen inganta harkar tattalin arziki da kuma siyasa domin bunkasa dagantaka da al'ummar shi'ar kasar.

Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Masar Shugaban Masar Hosni Mubarak ya ce zai sauka daga mulki a ranar 11 ga watan Fabreru bayan an shafe kwanaki 18 ana zanga-zanga.

Dan shekaru 82, ya kasance a kan karagar mulki tun 1981.

A baya Masar na daga cikin kasashen da ke zaune lafiya a yankin da ke fama da rikici, amma sai ga hargitsi ya barke domin nuna adawa da shugabancin shekaru 30 na shugaba Mubarak a ranar 25 ga watan Janairu.

Manyan abubuwan da suka haifar da rikicin sun hada da talauci, hauhawar farashi, cin hanci da rashawa da yawaitar matasa marasa aikin yi.

A yanzu majalisar sojojin kasar ce za ta ja ragamar al'amura nan da watanni shida har sai an gudanar da zabe.

Ana sa ran kungiyar 'yan uwa musulmi za ta taka rawar gani a duk wani zabe mai inganci da za a shirya, amma kasashen Yamma da Isra'ila na tsoron kungiyar ta kafa gwamnati a Masar.

Algeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Algeria

Zanga-zanga na ci gaba da gudana tun farkon watan Janairu, inda masu zanga-zangar ke bukatar shugaba Abdelaziz Bouteflika ya yi murabus.

Masu zanga-zangar sun hada da kungiyoyin 'yan kasuwa da jam'iyyun adawa.

Ana ganin batun tattalin arziki ne - musamman ma karuwar farashin kayan abinci kan gaba wajen haifar da boren na kasar Algeria.

A farkon watan nan shugaba Boutefika ya yi alkawarin kawar da dokar tabacin da aka sanya tun 1992, amma har yanzu bai yi ba.

Gwamnatin kasar na samu kudaden shiga daga man fetur da gas din da take sayarwa, kuma tana kokarin shawo kan matsalolin kasar ta hanyar kashe makudan kudade wajen ayyukan gina kasa.

Jordan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Jordan

Dubban mutanen Jordan ne su ka fito zanga zanga a makwanni biyar da suka wuce, domin neman sauyi ga yanayin rayuwa, da aikin yi, da kuma rage kudin abinci da kuma na man fetur.

A wani yunkuri da ya yi, Sarki Abdullah na biyu ya sallami Pira Ministan kasar Samir Rifai saboda tafiyar hawainiya da shirin cigaban kasar ke yi.

Sarki Abdullah ya nada Marouf al-Bakhit, wani tsohon Janar na sojin kasar a matsayin jakadan kasar a Isra'ila.

Ya nada sabbin ministoci 26 a watan Fabrairu.

Daular Jordan wata karamar kasa ce da ba ta da ma'adanai sosai kamar takwarorinta na yankin gabas ta tsakiya, amma kasar na taka gaggarumar rawa a gabas ta tsakiya.

Rasuwar Sarki Hussein, wanda ya yi mulki na tsawon shekaru 46, ya bar kasar cikin koma bayan tattalin arziki da kuma koma bayan siyasa.

Dan sa Abdullah, wanda ya gaji kujerar mulkin kasar ya fuskanci kalubale da dama wajen inganta rayuwar al'ummar kasar.

Saudi Arabia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Saudiyya

Saudiyya ita ce kasar da ta fi rike addini a kasashen gabas ta tsakiyya, kuma kasar ta fara ne daga kangin rashin ci gaba da koma baya, inda a yanzu haka ta zama daya daga cikin kasashen duniya dake da matukar arziki.

Amma masu mulkin kasar na fuskantar matsin lamba da kuma kalubale wajen aiwatar da sauyi a yayinda ta ke fuskantar matsalar ta'adanci a kasar.

Masu mulkin kasar dai na kokarin samar da zaman lafiya a yankin a yayinda suke duk mai yiwuwa domin kawar da ta'adanci.

An kuma hana 'yan adawa walwala a kasar.

Kasar na da martaba a yankin gabas ta tsakiyya a yayinda kasashen larabawa da dama ke nunuwa Sarki Abdullah Bin-Abd-al-Aziz Al Saud goyon baya.

Shugaban kasar Tunisia da aka tumbuke yana gudun hijira a kasar ta Saudiyya.

Syria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Syria

An yi yunkurin gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a Syria bayan da shugana Masar Hosni Mubarak ya sauka, amma hakan bai yi tasiri ba.

Shugaba Bashar al-Assad ya yi alkawarin kawo sauyi ga harkar siyasa, bayan da ya gaji mulki daga mahaifinsa Hafez, a shekarar 2000, bayan ya kwashe kusan shekaru 30 a kan mulki.

Har yanzu kasar tana karkashin dokar ta baci tun shekarar 1963 bayan mutuwar Hafez al-Assad.

An saki daruruwan 'yan adawa dake gidan kaso a wannan lokacin, amma har yanzu mutanen kasar ba su da cikakken 'yancin gudanar da harkokin siyasa, kuma tattalin azikin kasar na cikin wani yanayi na koma baya.

Tunisia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Tunisia

An ci gaba da zanga-zanga duk da cewa shugaba Zine al-Abidine Ben Ali ya yi murabus a watan Janairu.

Ya fice daga kasar bayan an shafe kwanaki ana zanga-zangar adawa da gwamnati da kuma tarzoma tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sanda.

Abinda ya haifar da boren shi ne cinnawa kansa wuta da wani matashi Mohamed Bouazizi mara aikin yi ya yi, bayan da jami'ai suka hana shi sayar da kaya a gefen hanya.

An rantsar da kakakin Majalisar dokokin kasar Foued Mebaza a matsayin shugaban riko, inda ya nemi Fira Minista Mohammed Ghannouchi, wanda ya ke kan mukamin tun 1999 da ya kafa gwamnatin rikon kwarya.

Shi ma Fira Ministan ya yi alkawarin murabus bayan an gudanar da zabe a watanni shida masu zuwa

Yemen

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Yemen

Bayan an shafe kwanaki ana zanga-zanga a kasar Yemen, Shugaban kasar Ali Abdullah Saleh ya bayyana cewa ba zai kara tsayawa takarar shugabancin kasar ba, bayan ya kwashe shekaru 30 a kan mulki.

Ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa ba zai mika mulki ga hannu dansa ba.

Amma dai an ci gaba da zanga-zanga a kasar, inda mutane suka fita a biranen Sanaa da Aden da kuma Taiz.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati dai sun yi artabu da wasu kungiyoyin da ke nuna goyon baya ga gwamnatin kasar kuma an turra 'yan sanda domin su tarwatsa zanga-zangar.

Yemen na daya daga cikin kasashen larabawa da ke fama da kuncin talauci a yayinda kusan rabin al'ummar kasar ke dogara da kasa da dalar Amurka biyu a rana.