Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Zagaye na biyu na zaben Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babu dai jam'iyyar da ta kai ga samun nasara kai tsaye a zagayen farko

'Yan takarar da za su fafata a zagaye an biyu na zaben kasar Nijar su ne Alhaji Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS-Tarayya, da Alhaji Seini Umarou na jam'iyyar MNSD-Nasara.

Alhaji Mahamadou Issoufou yana da goyon bayan kawancen CFDR da ya kunshi jam'iyyun siyasa fiye da talatin, yayin da shi kuma Alhaji Seini Oumarou, yake da goyon bayan kawancen ARN, wanda ya kunshi jam'iyyu fiye da ashirin.

A yakin neman zabensu dai, dukan 'yan takarar biyu sun yi alkawarin gudanar da ayyukan raya kasa a fannoni daban-dabam, domin inganta rayuwar al'ummar kasar, wadda tana daya daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya.

To su fa 'yan kasar ta Nijar, menene fatansu game da wannan zabe? Me kuma suke son ganin sabon shugaban da za a zaba ya yi, domin ciyar da kasar gaba?

To domin tattauna wannan batu mun gayyato wasu baki da suka hada da :

Mai sharia Abdourhamane Ghousmane, shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta, CENI. Da Malam Zakari Oumarou, mamba a kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PNDS-Tarayya.

Akwai kuma Malam Abdourraouf Sidi, mamba a kwamitin gudanarwa na jam'iyyar MNSD-Nasara.

Sannan kuma akwai Dr Soule Hassan, malami a jam'iyyar Poitiers dake Faransa.