Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yakin neman zabe a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An sha samun tashe-tashen hankula a lokutan yakin neman zaben

Yakin neman zabe dai wata hanya ce da dan takara zai bi domin tallata manufofinsa na cigaban kasa da yake fatan aiwatarwa idan jamaa sun zabe shi.

Don haka ne ake sa ran ire- iren kalamai da ayyukan jam'iyyu ko yan takara su kasance wadanda suka dace da tafarkin lumana ta yadda masu zaben za su iya banbancewa tsakanin manufofinsu domin zabar wadanda suka fi.

A Najeriya, yayinda yan takara ke gudanar da gangami a shirye-shiryen su na tinkarar zaben watan Afrilu, wani batu da ya fito fili a yakin neman zaben, shi ne na yadda ake samun tashin hankali tsakanin magoya bayan 'yan adawa da na gwamnati inda a wasu lokutan ma ake samun asarar rayika.

Yayinda Yan-adawa ke zargin gwamnatoci a matakai daban-daban da kawo masu cikas wajen gudanar da tarukan yakin neman zabe, su kuma gwamnatocin na zargin 'yan adawan ne da janyo hatsaniya.

To domin tattaunawa kan yadda yakin neman zaben na Nijeriya ke gudana, mun gayyato baki da suka hada da Alhaji Abba Daboh, Kakakin Kwamitin yakin neman zaben Shugaba Goodluck Jonathan na Jama'iyar PDP.

Da Alhaji Buba Galadima, Sakataren Jama'iyar CPC na kasa , da Nick Dazang, Kakakin Hukumar zabe ta Najeriya,INEC da Barrister Yahya Mahmoud, Lauya mai zaman kansa a Kaduna.

Haka kuma akwai Auwalu Salihu, Kakakin Hukumar Kula da gidajen Rediyo da Talabijin na Kasa a Najeriya, -NBC da kuma Comrade Shehu Sani, na kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Civil Rights Congress.

Haka nan kuma akwai wasu daga cikinku, ku masu saurarenmu da muka gayyato.