Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: A kasa a tsare

A kasa, a tsare, a raka, a jira', ya zamo wani take tun daga zabubukan da aka gudanar a baya, a Nijeriyar. Wadanda suka bullo da wannan dubarar, suna ganin wata hanya ce ta magance magudin zabe, kamar yadda ya faru a wasu jihohi a zaben shekara ta 2003 da ta 2007.

To sai gashi a wannan makon, hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriyar, watau INEC ta bi sahu, inda ta sanar cewa, jama'a suna da 'yancin su tsaya bayan sun kada kuri'a, har sai an gama kidaya, an kuma bayyana sakamako a kowacce mazaba.

To anya hakan zai sa a magance magudin zabe? Wanne kalubale ne kuma ke tattare da wannan mataki? ]

To domin amsa wadannan tambayoyi, baya ga dimbin masu sauraro da ke kan layi, mun kuma gayyato bakin da suka hada da, Mr Nick Dazang, na hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, da Farfesa Rufa'i Alkali, kakakin jama'iyyar PDP na kasa da MalamTambari Yabo Muhammad, kwamishinan 'yan sanda na Jihar Kano da kumaDr Mamman Lawan Yusufari, Malami a sashen shari'a a jami'ar Bayero dake Kano.

A yi sauraro lafiya.