Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Shin kwalliya ta biya kudin sabulu a zabukan Najeriya?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An samu korafe-korafe da dama a lokacin zabukan

A Najeriya bayan babban zaben da aka gudanar, wasu na zargin cewa ba ta sauya zane ba, dangane da matsalolin da aka fuskanta a zabubbukan baya ba.

Matsalolin dai sun hada da magudin zabe, da tashe-tashen hankula, da makamantan su.

Hakane kuma yasa kafin zaben na bana aka yi gagarumin garambawul a dokar zaben kasar tare kuma da nada sabbin shugabannin hukumar zabe, dan tabbatar da an kawadda wannan zargi a zukatan 'yan Nigeria.

Hukumar zaben dai ta lashi takobin kawo sauyi a harkar zaben na Najeriya, inda ta bayyana cewa dokar zabe ta ba 'yan kasar damar su kasa su tsare kuri'unsu, domin tabbatar da sun yi tasiri.

To ko shin daukar wadannan matakan sun sa ta sauya zani a harkar zaben na Najeriya.

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato :

Dr. Jibrin Ibrahim, masanin siyasa a Najeriya, da kuma Nick Dazang, mukaddashni daraktan yada labarai na INEC.

Sai Farfesa Rufa'i Alkali, daraktan yada labarai na jam'iyyar PDP.

Da kuma Alhaji Buba Galadima, Sakataren jam'iyyar adawa ta CPC.