Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tankiya kan karba-karba a Majalisun Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan batu dai ya ja hankalin jama da dama a kasar

Wani batun da ya haifar da cece-kuce a fagen siyasar Najeriya bayan zabe shi ne na yadda shugabancin Majalisar Dattawa da ta Wakilai zai kasance a nan gaba.

Jam'iyyar PDP, wadda mabiyanta da dama ke ganin ta yi watsi da tsarin karba-karba a zaben dan takarar shugaban kasa.

A yanzu ta kekasa kasa ta ce wajibi ne a ci gaba da rike tsarin rarraba mukamai a tsakanin shiyoyin kasar 6, kamar dai yadda suke bayan zaben shekarata dubu 2 da 7. Sai dai wasu na ganin ya kamata a daina kwan-gaba-kwan-baya.

Wannan batu dai na ci gaba da haifar da cece-kuce a Majalisar dama kasar baki daya.

To shin Jam'iyyar PDPn ta yi amai ta lashe ne a kan wannan magana, ko kuwa yaya al'amarin ya ke?

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato baki da dama da suka hada da:

Ambasada Ibrahim Kazaure Mataimakin Shugaban Jama'iyar PDP na kasa shiyar Arewa maso Yamma da Hon. Musa Sarkin Adar, Shugaban kwamitin kula da harkar zabe na Majalisar wakilai ta Najeiya.

Da Bashir Jantile wani dan siyasa a Najeriya da Malam Kabiru Sufi, Malami a kwalejin Fasaha da Kimiya ta Kano, wanda mai sharhi ne kan harkokin siyasa da kuma wasu daga cikinku, dinbim masu sauraranmu dake kan waya.