Ra'ayi Riga: Rantsar da sabbin shugabanni a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Goodluck Jonathan ya na karbar shaidar lashe zabe daga shugaban INEC

A ranar Lahadi za a rantsar da shugaba Goodluck Jonathan da gwamnonin wasu jihohi da suka yi nasara a zaben da ya gabata. Ko wanne kalubale ne ke jiran sababbin hukumomin?

A ranar Lahadi ne za a rantsar da shugaban Najeria, Dr Goodluck Jonathan da gwamnonin wasu jihohi da suka yi nasara a zaben da ya gabata.

Tuni dai jama'ar Najeriyar suka fara bayyana fatansu game da sababbin hukumomin da za'a rantsar.

Yau shekaru goma sha biyu kenan da ake gudanar da mulkin Dimukuradiyya ba kakkautawa a Najeriya.

Bayan da ta shirya zabe a shekarar 1999, gwamnatin mulkin soja ta wancan lokaci, karkashin jagorancin Janar Abdusslami Abubakar ta mika mulki ga gwamnatin farar hula ta jam'iyyar PDP, karkashin jagorancin shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, wanda aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar ta 1999.

Tun daga wancan lokaci ne kuma aka mayar da wannan rana ta zama ranar Dimukuradiyya a Najeriya.

To yayin da a ranar Lahadi za'a rantsar da shugaba Goodluck Jonathan tare da gwamnonin wasu jihohin Najeriya, batun da yanzu haka ke jan hankalin 'yan Najeriyar da dama, shi ne na irin kalubalen dake jiran sababbin hukumomin.

To domin tattaunawa a kan wannan batu, mun gayyato baki da dama wadanda suka hada da:

Farfesa Ahmed Rufai Alkali, Sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar PDP mai mulki, da Dr Garba Abari, na Jam'iyyar adawa ta ACN.

Akwai kuma Cif Rochas Okorocha, gwamnan jihar Imo mai jiran gado da kuma Malam Abubakar Kari, na jami'ar Abuja, wanda kuma mai sharhi ne kan harkokin siyasa a Najeriya.