Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalar 'yan gudun hijira a Nijar

Image caption Wannan rikici dai ya ritsa da 'yan cirani da dama daga kasashen Afrika

'Yan gudun hijira kusan dubu dari ne suka kwarara Jumhuriyar Nijar, tun bayan barkewar rikici a Libya da kuma Cote D'Ivoire.

Sai dai yayinda suka isa Nijar din, galibinsu sun shiga wani mawuyacin hali.

Gabannin yaki ya barke a Libya dai, dubun dubatar 'yan Afrika ne ke zaune a kasar inda suke gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban da suka hada da fannin gine-gine da harkar noma da kuma fannin hakar man fetur.

Kasancewarsu a kasar ta Libya dai na taimaka musu wajen samun kudaden shiga, inda suke taimakawa danginsu da kudade da sauran taimako.

Sai dai tun da yaki ya barke a kasar, dubban 'yan Afrikar ne ke kwarara cikin Jamhuriyar Nijar inda alkaluman baya-bayan nan suka nuna cewa yawansu ya kusa kai dubu dari, ciki har da wasu 'yan kasashen Afrika, kamar Najeria da Ghana.

To ko ta yaya za'a taimaka wa wadannan 'yan gudun hijira?

Kuma ko suna samun kulawar da ta dace daga gwamnatin Nijar?

Kadan kenan daga cikin irin abubuwan da muka tattauna a kai a cikin Filinmu na Ra'ayi Riga.