Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tasirin dokar yaki da ta'addanci a Najeriya

Image caption Ana dai zargin kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram da kaddamar da hare-hare a arewacin Najeriya

Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya sa hannu kan dokar yaki da ta'adanci da kuma halatta kudaden haram. Sai dai ra'ayi ya bambanta a kasar game da yadda za a aiwatar da wannan doka.

To ko wane irin tasiri ne wannan doka za ta yi wajen yaki da ta'addanci da kuma halatta kudaden na haram?

Batun ta'addanci dai batu ne da ke da tsawon tarihi, kuma ya samo asali ne daga gwagwarmaya tsakanin kungiyoyi ko kuma gwamnatoci, wadanda suke kokarin yakar danniya, ko kuma cimma wata manufa ko akidar da suka yi imani da ita.

An sami kungiyoyi da dama a cikin karni na ashirin, wadanda aka yiwa lakabi da kungiyoyin ta'addanci, irinsu kungiyar ETA ta kasar Spain, da kuma kungiyar IRA ta arewacin Ireland, sannan a baya bayan nan kungiyar Alqa'ida, wadda ake ganin cibiyarta na Afghanistan, da kuma rassa a wasu kasashe.

To domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato baki da dama wadanda suka hada da:

Dr Rabe Nasir tsohon shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa, da laifuka da kuma hallata kudaden haram a majalisar wakilai ta Nijeriya da ta gabata da Manjo Yahaya Shunku mai ritaya, mai yin sharhi kan al'amuran tsaro a Kaduna da Dr Mamman Lawan Yusufari, malami a sashen Shari'a na jami'ar Bayero ta Kano da kuma Kwamred Shehu Sani, mai fafutukar kare hakkin bil'adama a Kaduna.

Sai kuma masu sauraro dake kan layi, wadanda suma zasu bayyana ra'ayoyinsu. Ayi sauraro lafiya.