Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tunawa da matan da mazajensu suka mutu

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Da dama daga cikin zaurawan na cikin mawuyacin hali

Ranar Alhamis 23 da watan Yuni ne rana ta farko da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe, domin tunawa da matan da mazajensu suka mutu.

Makasudin ware ranar shi ne: a fito da irin halin kaka-ni-kayin da irin wadannan mata ke shiga, da kuma irin wariyar da suke fuskanta, bayan rashin mazajen nasu.

A cikin watan Disamban bara ne, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da ranar, bayan wani kudiri da kasar Gabon ta gabatar.

Wani dan siyasar Burtaniya ne ya fara jagorantar wannan yunkuri, ganin cewa ya tashi maraya wajen mahaifiyarsa, bayan rasuwar mahaifinsa a Indiya.

An kiyasta cewa daga cikin irin wadannan mata miliyan 245 a duniya, miliyan 115 na fuskantar rashin adalci da talauci da kuma azabtarwa.

Domin tattaunawa kan wannan batu, muna tare da Hajia Aisha Muhtari, Shugabar wata kungiyar kula da matan da mazajensu suka mutu suka bar su da ya'ya a Ghana.

Da Madame Mariama Musa ta wata kungiyar dake kula da harkokin mata da yara a Jamhuriyar Nijar. Sai Hajiya Altine Abdullahi, Shugabar kungiyar Zawarawa a Kano.

A kwai kuma Mrs Christiana Yohanna, Daraktar harkokin mata a Ma'aikatar kula da mata ta jihar Pilato. Da Ustaz Hussaini Zakariya wani Malamin Musulunci a Abuja, da kuma Reverand Sabon -yaro Adams, Malamin addinin Kirista a Abuja.